05/06/2022
Wata rana Ash-Sheikh Ahmad Al-Garkawiy "yana zaune a ofishinsa, sai wata daliba ta shigo"sai tayi sallama tace masa: "Malam na zo duba sakamakon jarabawana ne amma dalibai sun yage takardan, don haka nake so don Allah ka taimaka mun ka roki Exam officer a
nuna mun nawa.
Sai Malam ya tashi ya shiga ofishin Exam officer (mai kula da harkan jarabawan makaranta) yace masa idan babu damuwa kuma ba a
sab'a doka ba, a taimaka a nunawa wannan dalibar sakamakon jarabawanta.
Sai s**a ce ai Malam tunda ta biyo ta wurinka duk da baka san ta ba, amma bari a bata ta duba da kanta.
Bayan an baiwa wannan daliba tana dubawa,tana zuwa kan sunanta keda wuya sai kawai s**a ga ta rufe takardan da sauri ta fashe da kuka ta juya ta fita daga ohishin.
Fitar wannan 'daliba keda wuya, sai Malaman nan s**a ga Malam Ahmad Algarqawiy yana zubda kwalla, har ta kai ga ya kasa mallakan idanuwansa.
Bayan an 'dan natsa ka'dan, Sai Malaman s**a ce ma Sheikh Ahmad" Akramakallahu mu ma kasa zukatanmu sun tsinke saboda ita wannan yarinya ko bamu tambaye ta ba mun san sakamakon jarabawa ce bata yi mata kyau ba,
amma kai kuma sai muka rasa dalili, amma mun san dukkan abin da
zai sanya ka zubda kwalla lallai wannan abun ba karami ba ne.
Sai Sheikh Ahmad, Hafizahullahu, ya ce musu: "Wallahi lokacin dana ga wannan yarinyar ta fashe da kuka sai zuciyata take ce mun "Yanzu inda sakamakon lahiranta ne beyi kyau haka ba yaya kenan ?" Yace wannan shine abin da ya tsorata ni saboda a nan ana iya gyara"
"amma banda Lahira "Saboda haka, mu ma 'yan uwa sai mu "hankalta,mu tuna cewa akwai babban sakamako a qiyama"
Muna rokon Allah yasa muga sakamako mai
kyau a ranar lahira dan tsarkin Sunayensa
Usman Albani Abu Abdilrahman