06/04/2026
MATAKAN GINA YARO A MARHALAR YARINTA
Kamar yanda muka fada a baya kula da marhalar yarinta yana da matukar muhimmanci wurin gina yaro. Yayin da yaro yake cikin yarinta akwai abubuwa da ya kamata a kula da su don samar da ginannen yaro Wanda zai yi kwakwaro har karshen rayuwarsa .
1. Yarinta tana shudewa da matakai Wanda akwai bukatar duk wani uba ko wata uwa ta san wadannan matakan saboda ta gane ya dabiar yaro ta ke a wannan matakan kuma ya yakamata a muamalance shi. Don rashin sani yana iya ruguza kurciyar yaro da halaka masa rayuwa ba tare da fahimtar haka ba.
2. Yiwa yaro kyakkyawar muamala yana gyara kurciyar yaro ya sauya rayuwarsa gaba daya idan ya girma.
3.Barin yaro ya dandani kurciyarsa ba tare da yi masa shisshiga ga abunda wannan lokacin ne yake da muhimmanci.
4. Kula da feelings na yaro da kokarin gujewa duk wani abu da zai jawo masa matsala psychologically domin mafi yawan matsaloli suna farawa ne daga kurciya daga nan kuma abun ya yi tasiri ga rayuwar mutum bayan ya girma.
Gina mutum yana farawa ne daga kurciyarsa ba sai ya girma ba shi ya sa ya zama dole kula da yarinta da ginata ta hanyar da ta dace don samun lafiyayyen mutum da alumma za ta yi alfakhari da shi bayan ya girma.
Dr Fatima Muhd Bello