05/03/2026
Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuh.
Da farko muna miƙa gaisuwar Ramadan ga daukacin ‘yan’uwa Musulmi.
Muna roƙon Allah Maɗaukaki Ya karɓi ibadunmu, Ya gafarta mana kurakuranmu, Ya sa mu cikin bayinsa da aka ‘yanta daga wuta a wannan wata mai albarka. 🤲
Muna sanar da al’umma cewa wannan shi ne sabon shafinmu na Daliban Arewa UT Saudiya, bayan tsohon shafinmu ya samu matsalar tsaro (hacking). Saboda haka mun buɗe wannan shafi domin ci gaba da hulɗa da al’umma da kuma isar da saƙonni masu amfani.
Manufofin wannan shafi sun haɗa da:
• Ƙarfafa ilimi da wayar da kai kan damar karatu da guraben karatu (scholarships).
• Ƙarfafa haɗin kai da zumunci tsakanin ɗalibai da al’umma.
• Koyar da tarbiyya, ladabi da kyawawan halaye ga matasa.
• Yin ƙoƙarin kawo tasiri mai kyau ga al’ummar Najeriya da al’ummar Musulmi gaba ɗaya.
Muna roƙon ‘yan’uwa da abokai su bi wannan shafin namu, a turawa 'yan uwa domin su bibiya, domin mu ci gaba da yada alheri tare.
Allah Ya sanya wannan aiki ya zama mai amfani ga al’umma, Ya kuma sanya shi a ma’aunin ayyukan alheri.
Nagode sosai.
________________________________________________
Ramadan Mubarak to everyone.
We are pleased to inform you that this is the new official page of Daliban Arewa UT Saudiya after our previous page was unfortunately hacked.
Through this new platform, we aim to continue our mission of:
Promoting education and scholarship opportunities
Strengthening unity and cooperation
Encouraging discipline and good character among youth
Making a positive impact on Nigerian society and the wider Muslim Ummah
We kindly invite everyone to follow, support, and share this page so that we can continue spreading beneficial knowledge and positive initiatives.
________________________________________________
رمضان مبارك للجميع.
نود أن نُعلمكم أن هذه هي الصفحة الجديدة الرسمية لطلاب Daliban Arewa UT Saudiya بعد أن تعرضت صفحتنا السابقة للاختراق.
تهدف هذه الصفحة إلى:
دعم التعليم وفرص المنح الدراسية
تعزيز الوحدة والتعاون بين الطلاب
نشر الانضباط والأخلاق الحسنة بين الشباب
إحداث أثر إيجابي في المجتمع النيجيري والأمة الإسلامية عامة
نرجو من الجميع متابعة الصفحة ومشاركتها حتى نواصل نشر العلم والخير بإذن الله.