Hassan Haruna Zuru

Hassan Haruna Zuru Zuru

MUHIMMANCIN KWANAKI GOMA (10) NA ƘARSHEN WATAN RAMADANKwanaki Goma na Ƙarshen Watan Ramadan, Kwanaki ne masu Muhimmanci ...
20/03/2025

MUHIMMANCIN KWANAKI GOMA (10) NA ƘARSHEN WATAN RAMADAN

Kwanaki Goma na Ƙarshen Watan Ramadan, Kwanaki ne masu Muhimmanci sosai a cikin Addinin Musulunci, waɗanda ake Buƙatar Musulmi su ba da Himma domin Aikata Ayyuka na Alkhairi a cikin su. Waɗannan Kwanaki su ne Kwanakin da ake Samun Dare Lailatul Ƙadari.

Ga wasu daga cikin Muhimman Ayyukan da ake Buƙatar Musulmi ya Aikata a cikin waɗannan Kwanaki a Taƙaice:-

~I'tikafi: I'tikafi shi ne Zama a cikin Masallaci da Niyyar yin Ibada ga Allah Maɗaukaki. Ƙarancin sa shi ne Kwana Ɗaya, Yawanci sa kuma Kwanaki Goma. Yayin da Mutum yake a cikin I'tikafi, ana Buƙatar ya Yawaita Karatun Alkur'ani, Sallolin Nafila, Tasbihi, Istghfari da Sauran su. Idan za ka yi I'tikafi a Kwanakin da Juma'a za ta faɗo a cikin su, to Dole ne ka yi shi a cikin Masallaci Juma'a. Idan ko ba haka ba, to koda Masallacin Ungawarku kana iya yin I'tikafi.
~ Wanda Bai samu damar yin I'tikafi ba, ana bukatar ya Raya Darairan (Dare) waɗannan Kwanaki Goma ta hanyar tashi Cikin Dare domin yin Ayyuka na Ibada, domin Dacewa da Daren Lailatul Ƙadari, Musamman ma Daren 21, 23, 25, 27 & 29.
Daren Lailatul Ƙadari Dare ne wanda, yin Aikin Alkhairi a cikin Shi, ya fi yin Aikin Alkhairi a cikin Watanni Dubu (Shekara Tamanin da Uku) wadanda babu Lailatul Ƙadari a cikin su. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallama ya ce, "Ku Nemi Lailatul Ƙadari a cikin Kwanaki Goma na Ƙarshen Watan Ramadan". A wata Ruwaya kuma ya ce, "A cikin Kwanaki Bakwai na Ƙarshen Watan Ramadan".

~ Ana son a Yawaita Addu'o'i, Sadaka, Sada Zumunta, da dai sauran Ayyuka na Alkhairi.

Game da Irin Addu'ar da mutum zai yi Idan ya dace da Daren Lailatul Ƙadari, A'isha R.A. ta Tambayi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallama. Sai ya ce mata, ki ce, اللهم إنك عفو تحب" "العفو فاعف عنا

ƘARIN BAYANI: Ana Fara Neman Daren Lailatul Ƙadari ne da Ranar Ashirin ga Watan Ramadan, wato ita ce Ranar Dare na Ashirin da Ɗaya, wato daga Ranar Gobe Alhamis ke nan da Dare.

Allah Ya sa mu Dace, Amin.

Address

Jarƙasa
Zuru

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hassan Haruna Zuru posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Hassan Haruna Zuru:

Shortcuts

Share

Category