Markaz Abiyhurayratul Islamiy, Kamfa Jushin Gari Zaria

Markaz Abiyhurayratul Islamiy, Kamfa Jushin Gari Zaria Educate people islamic shari'a which is Alqur'an & Hadith according to teaching of Prophet Muhammad (s.a.w) and his companion.

03/06/2020

SHEIKH ALBANIY ZARIA PROJECT
Z A R I A - N I G E R I A
http://facebook.com/dsnzn

don samun karatuttukan Sheikh Albaniy Zaria (Rahimahullaah) ka tuntubi wadanan hanyoyi don samu

Whatsapp request: Send your name, State/country via whatsapp only to 👇🏻
+2347036108733

Histogram: 👇🏻
daarussahaabah_network_zaria

Twitter: 👇🏻
https://twitter.com/DaarusN

Telegram Channel:👇🏻
http://t.me/albaniyzariaproject

“Doing religion best on teaching of Alqur'an and Sunna according to understanding of Prophet and his companion.”

02/06/2020

SIRRIN GASKIYAN DAKE FUTOWA DAGA BAKIN ALBANIY ZARIA (RAHIMAHULLAAH).

✍🏻 El-Maude Ahmad Zaria (Abu Rumaysat)

Na saurari zantuttuka da jama'a keyi akan Marigayi shehin Malami Albaniy Zaria (Rahimahullaa), wasu su kace Malam Albaniy (Rahimahullaah) waliyyi ne !!!

wasu kuma s**a ce Malam Albaniy (Rahimahullaah) ba waliyyi bane amma ya shiga gonan waliyyai !!!😀
Na karshe kuma sun kace sheikh Albaniy Zaria (Rahimahullaah) Bawan Allaah ne !!!

Amsa shine: Malam tun farko Gaskiya ce yake karantarwa kawai amma mutane s**a ki karba saboda sabanin aqeeda ko kiyayya ko kuma hassada, Allaah swt yace:
(( بل نقذف بل لحق على البطل فيد مغه فائذاهوزاهق ولكم الويل مما تصفون. سورة الائنبياء ١٦ )).

Danfodio a wasiqatul ikhwan yace:
(ان طرق الحق واحد غير مختلف).
Wannan ke nuna gaskiya ko anki ko anso dole komai daran dadewa sai ta bayyana.
Malam lokacin da yake raye akwai abubuwa da yake fadi wanda gaskiya ne amma saboda ya sabama tinanin ko fahimtar wasu mutane ko kiyayya, ko kuma girman kai, sai suyi futo na futo da dashi ko kai tsaye ko a kaikaice misali na farko shine:
1. Shigan Aljani cikin jikin mutum, yanzu kuwa kowa babu wanda yake shakka akan shigan aljanni jikin mutum, wasu ma da suke in kari yanzu wasu nasu da harkan suke cin abinci.

2. Zaman hutu (Jilsa) yanzu ko 'yan bidi'a sun amince sunna ne a sallah b***e mai da'awan Sunna, in ma bakayi danka ko jikanka yanayi yanzu saboda yaga gaskiya ne.

3. Boko haram: Farkon rigimar boko haram Malamai da yawa basu san sharrin boko haram ba, sun dauka musulunci suke karewa, sai gwamnati take yaki dasu, shine kadai ya mike ya nuna ma jama'a cewa ba musulunci bane, a lokacin mafiya yawan mutane zaginshi sukeyi, ban mantawa acikin kaset din karshen alewa kasa yace duk lokacin da yayi magana akan boko haram sai wani daga cikin Zaria yayi mishi text din zagi, amma yau kowa tsoro yake a danganta shi dasu.

Gaskiya itace ke da wuyan karba wajen jama'a, ita kuwa gaskiya daya ce karbanta dole ne kuma shine shiriyan addini.
yana yawan fadin gaskiya daci gare ta, sh

Malamai Magadan AnnabawaAllah ya jikan Malaminmu Abbad ba don ya mutu ba✍️ Mansur SokotoAssabar 7 ga Shawwal 1441H (30/0...
30/05/2020

Malamai Magadan Annabawa

Allah ya jikan Malaminmu Abbad ba don ya mutu ba

✍️ Mansur Sokoto
Assabar 7 ga Shawwal 1441H (30/05/2020).

Wannan takardar da kuke gani a sama fitaccen Malamin Hadisin Birnin Madina ne ya rubuta ta a jiya Jum'ah.

Sunansa Sheikh Abdulmuhsin bn Hamad Abbad Al-Badr.
Ya fara koyarwa a Jami'ar Madina tun 1381H (Shekaru 60 da s**a wuce) har ya zama Vice Chancellor ya gama kafin mu zama dalibai a Jami'ar.

Ya fara koyarwa a Haramin Annabi (S) a shekarar 1406H (Shekaru 35 kenan yanzu) inda ya sauke duk كتب الستة a Masallaci mai Alfarma na Madina.

Ya karantar da mu Tauhid a Kolejin Hadisi a shekarar 1410 (1990) a lokacin ya tsufa har idanunsa sun ragganta.
Na kuma samu karatun wani sashe na Sunan Abi Dawud da wani sashe na Sunan An-Nasa'i a wurinsa a Harami.

A yau babu wani Malamin Hadisi dattijo da ake ji da shi a Madina ko ma a kasar Saudia baki daya irin sa. Kuma yana nan da jinsa garau da cikakken hankali da ilimi da basira; yana koyarwa. Yana tuna dalibansa na sama da shekaru 50 da zarar sun fadi sunansu. (Ni shaida ne).

A cikin wannan takarda Shaihun Malamin ya bayyana cewa, fatawar da ya yi a farkon bayyanar cutar Corona cewa, ba ya halalta ayi sallah da tazara a tsakanin jama'a (Social Distance), ya ce, kada jama'a su yi aiki da ita tunda yanzu hukuma ta fitar da doka a kan haka. Yana kiran jama'a su ajiye fatawarsa su yi aiki da doka.

Tsakani da Allah idan a Najeriya ne wace fassara zamu yi masa? Na yi amanna ko wanda bai san shi ba daga dan tsokacin da na bayar a sama ya san ba shi da wata bukata ga hukuma, ba shi kuma tsoron komai daga gare ta. Shi ne ma wanda a kwanakin baya ya yi fito na fito da nada wanda bai dace ba a shugaban Jami'ar Madina har sai da aka cire shi. Amma ya san manhajin Ahlus Sunnah da yake tsananin girmama dokar da shugabanni s**a yi bisa Ijtihadi ko da kuwa sun yi kuskure wajen yin ta.
Yanzu idan a nan ne da sauri wani zai jawo masa cewa, Annabi (S) ya ce:
"لا طاعة لمخلوق في معصية الخالق"
Inda za ka

23/05/2020
20/05/2020

Alamomin daren laylatul qadr

09/04/2020
19/03/2020

هل تتف من باروس کورونا؟ لا تخف، اکثر من دعاء رسولﷺ

16/03/2020

Address

No 19 Jushin Gari Zaria City
Zaria
810241

Telephone

+2348050237825

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Markaz Abiyhurayratul Islamiy, Kamfa Jushin Gari Zaria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category