Alkitabu wassunnah

Alkitabu wassunnah Qur'ani da Sunnah bisa fahimtan magabata na kwarai

31/08/2026
13/08/2026

Ana karanta harafin "Hamza ٱ" wacce tazo a farkon kalma (kuma ba tare da ta ɗauki harakat ba, wato fataha, kasra ko domma ba) ta hanyoyi 2:

1) Idan harafi na ukun kalman domma ya ɗauka, to za ayi mata domma ne kaman karanta "ٱتلُ" sai ya zama (Utlu).

2) Idan kuma harafi na ukun kalmar Fataha ne ko kasra to za a karanta Hamzar da kasra ne. Kaman "ٱصبِر" (Isbir) kamar "ٱقرَأ" (Iqra')

*Bayani:* Irin wannan hamzar ita ake ce ma Hamzatul wasli (Al-hamza ta sadarwa) kuma tana zuwa ne a matsayin alifun "ٱ" da kaman kan harafin Sadun a saman ta. Bata ɗaukan hamza a sama ko ƙasan ta. Ana fara ƙirgan kalmomin ne daga kan ita hamzar. Kuma dole ya zamto akan harafin hamzar za a tashi da karatun.

Misali; ٱتل zaka lura da abinda Lamun ta dauka ne. ٱصبر abinda Ba'un ta ɗauka, ٱقرأ abinda Ra'un ta ɗauka.

04/06/2026

Ku aika salatin ku ga fiyayyen halitta ﷺ

Muna gode ma Allah ﷻ da ya bamu ikon shaida wata Juma'ar.

27/05/2026

Eid Mubarak 🎊🎉

Taqabbalal Lāhu minna wa minkum

26/05/2026

Mafificiyan addu'a itace addu'an ranan Arfa, kuma mafificin abinda annabi ﷺ ya faɗa da annabawan da suke kafin shi: La ilaha illal Lahu wahdahu la sharika lah lahul mulku wa lahul hamd wa huwa ala kulli shai'in qadir.

18/05/2026

وقال الشيخ ابن عثيمين رحمه الله :
" هذا الحديث – يعني حديث ( لقد ضم القبر سعدا ضمة..) - مشهور عند العلماء ، وعلى تقدير صحته : فإن ضمة الأرض للمؤمن ضمة رحمة وشفقة ، كالأم تضم ولدها إلى صدرها ، أما ضمتها للكافر فهي ضمة عذاب والعياذ بالله ، فإن النبي صلى الله عليه وسلم أخبر أن الإنسان إذا دفن أتاه ملكان يسألانه عن ثلاثة أصول : من ربك ؟ وما دينك ؟ ومن نبيك ؟ فالمؤمن يقول : ربي الله ، وديني الإسلام ، ونبيي محمد ، أسأل الله أن يجعل جوابي وجوابكم هذا ، أما المنافق أو المرتد - أعاذنا الله وإياكم من هذا – فيقول : هاه هاه لا أدري ، سمعت الناس يقولون قولاً فقلته ، فيضيق عليه القبر حتى تختلف أضلاعه والعياذ بالله ، يدخل بعضه في بعض من شدة الضم ، ففرق بين ضم الأرض للكافر أو المرتد وضمها للمؤمن ." انتهى باختصار .

📕" لقاءات الباب المفتوح " (لقاء رقم/161، سؤال رقم/17) .

Ibnu Uthaimin (R) yace:«Muna rokon Allah ya tabbatar da mu da ku, Mutum yana bacci cikin dare ko cikin yini alhal yana a...
14/05/2026

Ibnu Uthaimin (R) yace:
«Muna rokon Allah ya tabbatar da mu da ku, Mutum yana bacci cikin dare ko cikin yini alhal yana amintacce, ko da zai farka baccin sai ya kasance amana an cire ta daga zuciyarsa, don haka ne ma aka shar'anta ma mutum yayi bacci cikin zikiri, haka kuma ya farka cikin zikiri ... Sai dai fa wanda baya kwanciya cikin zikiri ana jiye masa tsoron a cire amana daga zuciyarsa idan ya farka»

Sharhin Sahihu Bukhari na Ibnu Uthaimin.

18/04/2026

Ku ji tsoron Allah !!!

Ba a ga jinjirin watan Shawwal a Nigeria ba. Don haka sallah sai ranar Juma'a 20 ga Maris.
18/03/2026

Ba a ga jinjirin watan Shawwal a Nigeria ba. Don haka sallah sai ranar Juma'a 20 ga Maris.

15/03/2026

Daren Lailatul Qadr

Ubayyu Ɗan Ka'ab yana rantsewa yace irin wannan daren na 27 shine daren Lailatul Qadr. Muslim ya ruwaito.

Don haka ku ajiye duk wani abu mai janye hankali. Ku duƙufa da addu'o'i musamman faɗin: Allahumma innaka afuwwun tuhibbul afwa fa'afu ani.

Ku sanya Nigeria cikin Addu'a, Allah ya bamu tsaro.

Address

Zaria
KITAB

Telephone

2348108760179

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Alkitabu wassunnah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category