01/01/2026
SAƘON GODIYA
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai.
Hukumar Markazu Sheikh Jibril Musa Kurmin Bomo na miƙa godiya ta musamman ga
Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari, kuma ALGON CHAIRMAN KADUNA STATE,
Sheikh Muhammad Jamil Abubakar Albani,
saboda karamci, kulawa da goyon bayan da ya nuna mana.
Muna matuƙar jin daɗi da alfahari da halartar taron Saukar Alƙur’ani Maigirma na makarantarmu da ya yi, tare da tawagarsa, lamarin da ya ƙara wa taron armashi, daraja da ƙwarin gwiwa ga malamai, ɗalibai da al’umma baki ɗaya.
Haka kuma, muna godiya ƙwarai da gaske bisa gudummawa da ya bayar domin tallafa wa harkokin ilimi da hidimar Alƙur’ani. Wannan gudummawa ta nuna irin kishin addini, ilimi da ci gaban al’umma da Shugaban yake da shi.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka masa da alheri, Ya ƙara masa lafiya, hikima da nasara a jagorancinsa, Ya kuma albarkaci dukkan ayyukansa na alheri. Allah Ya sa wannan gudummawa ta zamo sadaka jariya a gare shi. Ameen.
Mungode ƙwarai.
Sa hannu:
Hukumar Gudanarwar
Markazu Sheikh Jibril Musa
Kurmin Bomo