16/01/2015
ABINDA AKESO KAYI KAFIN KAFITA ZUWA SALLAN JUMA'A
1-SHAFA TURARE IDAN KANA DASHI AMMA BANDA WANDA YAI HARMA DA AIKIN HAJJI KUMA BANDA MATA:
Hadisi ya tabbata daga Salman daga Annabi s.a.w cewa: Babu wani mutum dazai wanka ranar Juma'a, yayi tsarki gwargwadon iko, shafa mansa, ya shafa Turarensa, sannan yafita ba tareda yaraba tsakanin mutane biyuba, yayi sallarsa da aka wajabta masa(Juma'a), sannan ya saurara lokacinda Liman yake Huduba, face Allah yagafarta masa laifukansa na wannan Juma'ar har zuwa Juma'a mai zuwa, duba sahihul Buhari 883, Abu Dauda 1113, Darimi 1541, Bagawi 1058.
Hadisai da dama sunyi bayanin haramcin mace tafita idan ta shafa Turare, nadaga ciki Hadisin Zainab Saqifiyya daga Annabi s.a.w cewa: Idan dayanku zata Masallaci to kada tasanya Turare awannan daren, Muslim 443, Nasa'i 260/2. Awannan Hadisin anyi amfanine da dare wanda hakan yana nuna halascin zuwan mata Masallaci da daddare, amma umurnin da akayi yananan akoda wani lokaci kamar yanda Hadisai masu yawa s**a nuna. Duba Sahihu fiqhu sunnah mujalladin farko shafi na 507