07/11/2025
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Ga Dare nan ya shigo ku daure mu yawaita addu'oin neman zaman lafiya da aminci. Wawaye na cigaba da dariya, masu hankali na qara shiga damuwa.... Ya Allah karka kamamu da laifin Wawayen cikin mu.
Karku manta ance gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah...
Boko haram da irin haka aka fara wasu na dariya, haka kidnapping da haka aka fara mutane na dariya... Amma karshe babu wanda bai kuka ba. Don haka mu shiga taitayin mu.
................................................................
Kuskuren mutum ɗaya na iya jefa milyoyi a wahala da tashin hankali... Haka ne? To in hakane gareku masu cewa shugaban Amerika mahaukaci ne, ku sani muna addu'a ne kar haukan nasa ya shafe mu, domin haukan nasa na iya budemana kofofin bala'i. Komi nasu a tsare yake, bashi ne keyi ba kurum yayatawa yake amma long term plan ne tuntuni, kurum yanzu ne suke jin lokacin executing plan ɗin into Action.
Lahaula wa laquwata illa billah, Allah ka kawar da wannan musifar. Mu daure muyi sallar nafila raka'a biyu kafin mu kwanta, bayan mun idar mu mayar da goshi ƙasa mui sujjada muna masu fadin LA'ILA HA'ILLA ANTAS SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ ZALIMIN × 41 daga nan sai mu roki Allah kariya daga dukkan bala'i, ya tsaremu, ya tsare mana addinin mu tare da ƙasar mu.
.................................................................