Masoyiyar Prof Ibrahim Maqary

Masoyiyar Prof Ibrahim Maqary Wannan shafi ne na ambaton Manzon Allah SAW... Babu komai acikin sa sai soyayyar Manzon Allah SAW da bayin Allah salihai.
(2)

Mun wayi gari da wani bidiyo na wani mutum da ya yi karatun Hausa har zuwa matakin Degree da Master’s a Jami’ar Bayero K...
23/09/2026

Mun wayi gari da wani bidiyo na wani mutum da ya yi karatun Hausa har zuwa matakin Degree da Master’s a Jami’ar Bayero Kano (BUK), yana bayyana cewa wai Maulana Prof. Ibrahim Maqary ɗalibinsa ne.

To, bari mu ɗan waiwaya kan wasu muhimman abubuwa domin a fahimci maganar da kyau.

Da farko dai, abin da ya kai Maulana Prof. Ibrahim Maqary Jami’ar Bayero Kano shi ne karatun PhD, wato digiri na uku, a Sashen Larabci.

Binciken PhD ɗinsa kuwa ya kasance ne a kan Diwanin Maulana Sheikh Ibrahim Niass RTA, musamman waƙoƙin yabon Manzon Allah ﷺ da abin da s**a ƙunsa na ma’anoni da ilimi.

Kuma, bisa bayanan da aka bayar, Maulana ya kammala wannan bincike na PhD cikin shekaru biyu.

Yanzu tambayar ita ce:

Ta yaya mutumin da ya zo Jami’a domin yin PhD a fannin Larabci zai zama ɗalibin wanda ya yi Master’s a fannin Hausa?

Shin saboda an gayyaci mutum zuwa wajen PhD defence ne, ya zauna ya saurara, hakan kawai zai sa a ce mai binciken ya zama ɗalibinsa?

Idan haka ne, to akwai buƙatar a bayyana mana: a ina aka haɗu a matsayin malami da ɗalibi? A wane mataki ne ya koyar da shi? Kuma a wane fanni?

Domin abin da aka sani shi ne, Maulana ya kasance yana karatun Larabci, yayin da shi kuma yake da ƙwarewa a Hausa. Fannonin karatun ba ɗaya ba ne, kuma kasancewar mutum a Jami’a ko halartar defence ɗinsa ba ya nufin kai ne malamin da ya koyar da shi.

Abin da ya fi dacewa shi ne a bambanta tsakanin malamin da ya koyar da mutum da kuma wanda ya kasance a wani taro ko defence na bincikensa.

Idan kuwa akwai hujjar cewa Maulana Prof. Ibrahim Maqary ya kasance ɗalibinsa a wani lokaci, to a kawo hujjar a fili: yaushe? A ina? Wane darasi ya koya masa? Kuma a wane mataki?

Domin a harkar ilimi, ba a gina ikirari da zato. Ana gina shi ne da takardun karatu, tarihin ilimi da hujja.

Abin mamaki kuma shi ne, mutumin da yake cewa Maulana ɗalibinsa ne, shi ne Maulana ya kai matsayin Professor, yayin da har yanzu ake ta jiran a ji irin wannan ci gaban ilimi daga gare shi.

A ƙarshe, bai kamata mu mayar da wannan magana ta zama batun son rai ko ƙiyayya ba. Abin da ake buƙata shi ne gaskiya da hujja.

Idan Maulana Prof. Ibrahim Maqary ɗalibinsa ne, a kawo hujja.

Idan ba ɗalibinsa ba ne, to a daina jingina wa mutum abin da ba shi da tushe.

Ilimi yana buƙatar gaskiya, kuma gaskiya tana buƙatar hujja.

Banbancin Maulana Prof. Ibrahim Maqary da Wasu Malamai Wajen Zurfin Ilimin Addini da Fahimtar SaDa farko dai, Maulana Pr...
23/09/2026

Banbancin Maulana Prof. Ibrahim Maqary da Wasu Malamai Wajen Zurfin Ilimin Addini da Fahimtar Sa

Da farko dai, Maulana Prof. Ibrahim Maqary ya taso ne a cikin gida da aka gina bisa ilimi da ilmantarwa, ba gidan sharholiya ba. Ilimi shi ne sana’a da abin alfaharin gidan su. Tun yana ƙarami, ya saba da karatu, bincike da zama tare da malamai. Saboda haka, karatu da neman ilimi s**a zama wani ɓangare na rayuwarsa tun daga ƙuruciya.

Tun bai kai shekara 20 ba, ya riga ya haddace manyan fannoni da ake koyarwa a zauruka, musamman Fiqhu, Luga da sauran rassan ilimin addini. Ba wai iya karanta littattafan kawai ya yi ba; ya haddace su, ya karanta su a gaban malamansa da iyayensa, kuma ya samu tarbiyya da horo na ilimi tun yana ƙarami.

Sannan bayan tafiyar sa Masar, yayi karatu gurin Malaman Masalkacin Azhar, aciki harda Sheikh Muhammad Mutawal Al-sha'arawiy. Sannan a can ne ya haɗu da Shehinsa wato Maulana Sheikhul Islam Sharif Ibrahim Saleh Alhussainiy Rta inda ya karanci fannonan Addini Muslunci a hannusa kuma ya bashi ijazar cewa ya kware a fannonin.

Bayan zurfafa ilimin Alƙur’ani, haddarsa, ruwayoyinsa da Tafsirinsa, Maulana ya kuma haddace hadisai masu yawa waɗanda s**a taimaka masa wajen fahimtar Alƙur’ani da fassara ma’anoninsa.

Bugu da ƙari, kasancewarsa masani a ilimin Hadisi ya ba shi damar sanin matsayin ruwayoyi da bambance sahihi da marar inganci.

Haka kuma, Maulana masani ne a fannin Usulul-Fiqhi. Wannan fanni yana da matuƙar muhimmanci wajen fahimtar nassoshi, sanin yadda ake fitar da hukunci daga dalilai, da kuma fahimtar ƙa’idojin da malamai s**a gina hukuncin shari’a a kansu.

Saboda haka, fahimtar Maulana game da nassoshi da yadda ake amfani da su wajen kafa hujja tana da zurfi fiye da yadda mutum zai iya fahimta idan bai yi zurfin karatu a wannan fanni ba.

Bayan haka, akwai fannin Maqasidush-Shari’a—wato fahimtar manufofi da hikimomin da Shari’a ta ginu a kansu. Wannan ma wani muhimmin fanni ne da yake taimakawa wajen fahimtar dalilin da ya sa Shari’a ta umurci yin wani abu ko ta hana wani abu.
Wanda bai yi zurfin karatu a wannan fanni ba, yana iya ganin wasu bayanan Maulana kamar sabon abu, alhali kuwa magana ce da aka gina ta bisa ƙa’idojin ilimi da fahimtar manufofin Shari’a.

Saboda haka, banbancin Maulana Prof. Ibrahim Maqary da wasu daga cikin malaman da suke ƙalubalantar sa ba wai kawai yawan karatu ba ne; akwai banbanci wajen faɗin fannonin ilimin da aka yi zurfi a cikinsu, fahimtar nassoshi, sanin matsayin ruwayoyi, Usulul-Fiqhi da Maqasidush-Shari’a.

Wani lokaci, mutum zai ji Maulana ya faɗi wata mas’ala da ba ta saba da abin da ya sani ba, sai ya yi gaggawar ƙin yarda da ita. Amma idan ya koma ga littattafai, ya bincika maganganun malamai da hujjojin da aka kafa mas’alar a kansu, sai ya gano cewa abin da Maulana ya faɗa yana da tushe na ilimi.

A nan ne ake gane cewa ba duk abin da ya saba da abin da muka sani ba ne yake zama kuskure. Wani lokaci, abin da muke buƙata ba gardama ba ce, sai dai komawa ga littattafai da bincike.
Domin a fagen ilimi, jahilci kan sa mutum ya ƙi abin da bai sani ba; amma masani yana komawa ga hujja kafin ya yanke hukunci.

Allah Ya ƙara wa Maulana Prof. Ibrahim Maqary lafiya, ilimi, hikima da basira, Ya kuma cigaba da amfanar da al’umma da ilimin sa.

Binciken PhD na Maulana Prof. Ibrahim Maqary Kan Diwanin Maulanmu Shehu Ibrahim Niass RTADiwanin Shehu Ibrahim Niass RTA...
23/09/2026

Binciken PhD na Maulana Prof. Ibrahim Maqary Kan Diwanin Maulanmu Shehu Ibrahim Niass RTA

Diwanin Shehu Ibrahim Niass RTA littafi ne mai dauke da baitocin yabo da Shehu ya yi ga Manzon Allah SAW. Shehu Ibrahim Niass ya shahara da baitoci masu tarin ilimi, soyayya ga Annabi, da sirrikan Sufanci. Ana kiran littafin da suna Dawawinu Sitt - yana da dubban baitoci a cikin harshen Larabci.

To, idan aka ce Prof. Ibrahim Maqary yayi PhD Thesis dinsa akan Diwanin, ana nufin:

1. Binciken ilimi mai zurfi: Ya dauki Diwanin a matsayin maudu'in bincikensa na digirin digirgir (PhD) a Jami'ar Bayero University Kano a shekarar 2009. Wannan shi ne bincike mafi girma a jami'a.

2. Abin da ya bincika: A PhD din ba karanta Diwanin kawai ba ne, sai dai:

Fassarar Larabci da ma'anoni

Salon adabi da fasahar wakoki

Ilimin tauhidi da Sufanci dake ciki

Hujjoji da Shehu ya kawo daga Al-Qur'ani da Hadisi

3. Muhimmancinsa: Wannan ya nuna cewa Prof. Maqary ba malamin addini kawai ba ne, malami ne mai bincike (academic) wanda ya haɗa ilimin addini na zaure (da ya karanta a Nigeria, Masar Senegal da Mauritania) da ilimin jami'a na zamani a Al-Azhar da BUK.

A takaice, ya zabi Diwanin Shehu Barhama ne saboda shi ne mafi girman aikin adabi na Sufanci a Yammacin Afirka, kuma yayi bincike mai zurfi don fito da darussan dake ciki ga al'umma.

Allah ya bamu fahimta mai yawa ya bamu albarkar sa.

Shifa wannan tsohon da yake ta surutu Hausa ya karanta, shikuma Maulana Prof Arabic yayi, kuma iya Phd yaje BUK yayi. Ba...
23/09/2026

Shifa wannan tsohon da yake ta surutu Hausa ya karanta, shikuma Maulana Prof Arabic yayi, kuma iya Phd yaje BUK yayi.

Banda ruɗewa da hauka irin ta tsohon nan tayaya Ɗan Arabic me Phd zai zama Dalibin Wanda ya karanci Hausa? kuma ma Dalibin ka dayazo yin Phd kuma ya riga ka gama Phd har ya zama Professor shekaru masu yawa baya, amma kai saboda daqiqanci da rashin basira har yanzu kananan wuri ɗaya.

Anya wannan tsohon beda tabin hankali kuwa???

Yana daga cikin alamomin son Annabi SAW:Kaji kanajin daɗi da nishaɗi idan an ambaci sunansa mai girma.Kuma zuciyarka tan...
23/09/2026

Yana daga cikin alamomin son Annabi SAW:
Kaji kanajin daɗi da nishaɗi idan an ambaci sunansa mai girma.
Kuma zuciyarka tana cike da farin ciki da annashuwa idan ka ji an ambaci sunansa mai daraja.

Muyi salati ga Manzon Allah SAW

Sayyiduna Rasulullahi SAWShine Arzikin halittun farko da na qarshe. Shiyasa ruwaya ta tabbatar cewa lokacin da Annabi Ad...
22/09/2026

Sayyiduna Rasulullahi SAW
Shine Arzikin halittun farko da na qarshe. Shiyasa ruwaya ta tabbatar cewa lokacin da Annabi Adam yaci daga itaciyar da aka hane shi, sai da yayi tawassuli da Manzon Allah SAW sannan aka karbi tubar sa.

Muyi salati ga Manzon Allah SAW

Dole mu tashi tsaye muqara jajircewa wajen qara yaɗa Soyayya da girman Manzon Allah SAW a zuqatan mutane.Domin addini ga...
21/09/2026

Dole mu tashi tsaye muqara jajircewa wajen qara yaɗa Soyayya da girman Manzon Allah SAW a zuqatan mutane.
Domin addini gaba ɗaya ya ginu ne abisa Soyayya da girmama Manzon Allah SAW.

An ruwaito daga Ibn Abbas ya ce: Lokacin da Abdul-Muttalib ya tafi da ɗansa Abdullahi domin ya nema masa mata, sai s**a ...
21/09/2026

An ruwaito daga Ibn Abbas ya ce:

Lokacin da Abdul-Muttalib ya tafi da ɗansa Abdullahi domin ya nema masa mata, sai s**a wuce ta wajen wata bokanya daga mutanen Tabala, Bayahudiya ce wacce ta karanta littattafai, ana ce mata "Fatima 'yar Murr al-Khath'amiyya". Sai ta ga hasken Annabta a fuskar Abdullahi, sai ta ce: "Ya kai saurayi, kana da sha'awar ka sadu da ni yanzu? Zan ba ka raƙuma ɗari?"

Sai Abdullahi ya ce da waƙa:

> Haramun kuwa, mutuwa ta fi kusa da ni fiye da shi,
> Halal kuwa, ba halal ba ne sai na tabbatar da shi.
> To fa yaya game da al'amarin da k**e nema?
> Mai karamci yana kare mutuncinsa da addininsa.

Sannan ya tafi tare da mahaifinsa, sai mahaifin nasa ya aurar masa da Aminatu 'yar Wahab dan Abdu Manaf dan Zuhra. Wacce a tarayyar aure Hasken Manzon Allah SAW ya shiga cikin ta daga tsatson Sayyiduna Abdullahi Rta.

Allah Ya ƙawata Manzon Allah SAW da adon rahama. Don haka, kasantuwar Sa ma rahama ne; dukkan kyawawan ɗabi'unSa rahama ...
20/09/2026

Allah Ya ƙawata Manzon Allah SAW da adon rahama. Don haka, kasantuwar Sa ma rahama ne; dukkan kyawawan ɗabi'unSa rahama ne, kuma siffofinSa ma rahama ne ga halittu.

Muyi salati ga Manzon Allah SAW

A duk lokacin da kake zikiri, to Allah na tare dakai yana ambaton ka.Shiyasa ake son samun cikakken natsuwa da halartar ...
20/09/2026

A duk lokacin da kake zikiri, to Allah na tare dakai yana ambaton ka.
Shiyasa ake son samun cikakken natsuwa da halartar zuciya a lokacin ambaton Allah, domin dacewa da cikakken hasken zikiri na ganawa da Allah.

Allah ya raya mu a tafarkin zikiri.

Address

Zaria

Telephone

+2349033097708

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Masoyiyar Prof Ibrahim Maqary posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share