19/09/2026
SAKON TA’AZIYYA
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
Cikin alhini da jimami, Achievers Academy Zaria na miƙa sakon ta’aziyyarmu ga iyalan marigayiya Zulaihat Ɗanlami, tsohuwar malamar makarantar, wadda Allah Ya yi wa rasuwa bayan ta haihu da ’yan biyu (twins) a garin Zaria.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta mata, Ya jiƙanta da rahama, Ya sanya Aljannar Firdausi ta zama makomarta, Ya kuma sa yaran da ta bari su kasance cikin kariyar Allah da kulawarSa.
Allah Ya ba iyalanta, ’yan uwa, abokan arziki da dukkan waɗanda rasuwar ta shafa haƙurin jure wannan babban rashi.
Allah Ya jikanta, Ya kyautata makomarta, Ya kuma ba iyalan da s**a rage ƙarfin zuciya.
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.