Majalisin malamai - Palladan Zaria

Majalisin malamai - Palladan Zaria WANNAN SAHAFIN ANBUDE SHINE DOMIN YADA HUDUBOBI, WA'AZOZI DA MUHADARORI MUSAMMAN NA MALAMANMU DAKE PALLADAN DA NIGERIA BAKI DAYA.

Assalamu ‘Alaikum wa Rahmatullahi wa BarakatuhuIna amfani da wannan dama domin sanar da al’umma cewa, za mu fara karatun...
18/05/2026

Assalamu ‘Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu

Ina amfani da wannan dama domin sanar da al’umma cewa, za mu fara karatun littafin Talkhīṣ Kitāb Aḥkām al-Uḍḥiyah wa al-Dhakāh (تلخيص كتاب أحكام الأضحية والذكاة).

Karatun zai gudana kullum bayan Sallar Asubahi, a cikin kwanaki takwas da s**a rage mana kafin Idi. Wurin karatun shi ne Masallacin Ƙofar Gidan Durum, Anguwan Fulani, Palladan, Zaria.

Wannan littafi ne da yake bayanin hukunce-hukuncen layya da yadda ake yanka a Musulunci, wanda babban malami Shaikh Muḥammad bn Ṣāliḥ al-‘Uthaimīn ya rubuta.

Ko da yake wannan rairaye-rairaye ne kawai na asalin littafin da ya kai shafuka 93, wannan taƙaitaccen sigar ba ta wuce shafuka 40 ba.

Alḥamdulillāh, mun karanta asalin littafin tare da babban malaminmu Shaikh Mukhtar Khalid Palladan – ḥafiẓahullāhu – a cikin kwanaki 4 kacal, daga 27/08/2017 zuwa 31/08/2017, wato shekaru 9 da s**a gabata. Ina addu’a Allah Ya saka masa da alkhairi.

Sannan duk wanda ke zaune a Palladan kuma yana son halartar karatun, kofa a buɗe take. Zai iya zuwa.

Fatan Allah Ya ba mu dacewa a duniya da lahira.

06/12/2025

Babbar shela ga sababbin manyan masoyana! Sulaiman Umar

Address

PALLADAN ZARIA
Zaria

Telephone

+2347068279386

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Majalisin malamai - Palladan Zaria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Majalisin malamai - Palladan Zaria:

Share

Category