Allah Ta'ala yasa ALQUR'ANI ya zamo hujja garemu ba akan mu ba.
Ma'abota Alqur'ani
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ma'abota Alqur'ani, College & University, Zaria.
**ALQUR'ANI DA MAKARANTAN SA**
Shehin Malami Ibrahim (almaqdisy)
Wata rana yayiwa Dalibin sa (Abbas addaym) Nasiha yana cewa dashi: "ka yawaita karatun Alqur'ani kada kayi wasa dashi, domin shi (Alqur'ani) yana sauqaqa maka duk abinda kake nema ne a rayuwar ka gwar-gwadon yadda kake karanta shi.
Ya Allah albarkacin sunayen ka kyawawa da siffofin ka madaukaka ka azurta mu da yawaita karatun Alqur'ani cikin abinda yayi saura a rayuwar mu.
MAKARANTA ALQUR'ANI ME GIRMA SUN RABAUTA DUNIYA DA LAHIRA.
Annabin rahma Manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata a gareshi: "Duk Wanda karatun ALQUR'ANI ko anbatona ya hana shi roqona wata buqata tashi to Ni kuwa, Zan bashi sama da abinda Na baiwa Masu roqona.
kuma falalar Littafin Allah akan sauran littattafai kamar falalar Allah Ta'ala ne akan abin halittan sa.
Daga Said bn Malik (Abu said alkhudree) Allah Ta'ala ya yarda dashi.
Hadisin Tirmizee (Hadisi ne me kyau).
FALALAR ALQUR'ANI MAI GIRMA
ya tabbata Manzon Allah tsira da amincin Allah sun tabbata gare shi yana cewa "lallai Allah Ta'ala yana daga darajar wasu Mutane da wannan ALQUR'ANI kuma ya qasqantar da wasu da shi."
--hadisin Umar dan Khadab*
--Riwar Muslim*
ya Hayyu ya Qayyum ka sanya mu cikin wadanda ALQUR'ANI me girma ke daga darajar su duniya da lahira
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Website
Address
Zaria