06/09/2026
ALHAMDULILLAH 🤗
Cikin ikon Allah Subḥānahu wa Ta’ala, a yau Lahadi, 6 ga Satumba, 2026, ɗalibi Abdullahi El-Maude ya bayar da haddarsa ta ƙarshe, kuma ya kammala haddar Alƙur’ani Mai Girma, Hizb 60.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya albarka cikin abin da aka haddace, Ya tabbatar da Alƙur’ani a cikin zuciyarsa, Ya saka wa malamai da iyaye da mafificin alkhairi.
Ya Allah, Ka sanya Alƙur’ani ya zama hujja gare shi ba hujja a kansa ba ranar Alƙiyama, Ka ba shi ikon karanta shi da dare da rana, Ka kuma sanya shi cikin waɗanda suke aiki da koyarwar Alƙur’ani.
Allah Ya sanya wannan cikar ta zama farkon wata rayuwa mai cike da ƙaunar Alƙur’ani da aiki da shi.
Aãmeen Ya Rabbal Aalameen.
Ammar Bin Yasir Qur'anic & Science Academy Zaria
Sunday, 6th September, 2026