13/06/2026
Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da rasuwar Manjo-Janar Rabe Abubakar (Rtd), wanda ya rasu yayin da yake hannun 'yan bindiga duk da ƙoƙarin da gwamnati da hukumomin tsaro s**a yi na ganin an kuɓutar da shi cikin koshin lafiya.
A cewar sanarwar da Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida, Dr. Nasiru Mu'azu, ya fitar, marigayin ya rasu ne sak**akon matsalolin lafiya da s**a haɗa da ciwon s**ari da hawan jini, yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane.
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana alhininsa kan wannan babban rashi, inda ya jajanta wa iyalan marigayin tare da jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da haɗa kai da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen matsalar 'yan bindiga da tabbatar da hukunta masu hannu a irin waɗannan munanan laifuka.
Allah Ya jiƙan Manjo-Janar Rabe Abubakar (Rtd), Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Allah Ya bai wa iyalansa da al'ummar Katsina haƙurin jure wannan babban rashi.
Matsalar tsaro na ci gaba da karɓar rayukan manyan mutane da talakawa a ƙasar nan, lamarin da ke buƙatar ƙarin matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma.