Huffazul Qur'an Tv

Huffazul Qur'an Tv

Share

إن الذين يتلون كتب الله وأقاموا الصلوة وأنفقوا مما رزقنهم سرا وعلانية يرجون تجرة لن تبور🌹❤️

16/07/2026

Yaranmu Masu Capacity ❤️
Abbas Nuruddeen Bin Muazz(Mihsaan)
Asmau Nuruddeen Bin Muazz(Amnah)

Photos from Huffazul Qur'an Tv's post 16/07/2026

Ya Allah kasa Alqur’ani ya Cecemu Baki daya 🥹🤲

15/07/2026

Wata Rana a Garin Zaria yayin wata ziyara da Gwani Usman Lawal Zurmi Na Allah ya kawo mana 👏❤️

Goni Na’allah Mazan Sheeka 🔥

15/07/2026

Tomorrow 👏✅

15/07/2026
15/07/2026

Kitabullah

14/07/2026

💔😪 Akwai Mutane da Ba Za Ka Taɓa Mantawa da Su ba... Yar' Uwa Hafiza Bahijja Adam na ɗaya daga cikinsu.

Lokaci yana tafiya, amma wasu mutane suna barin tarihi mai kyau da ba zai taɓa gogewa daga zukatan waɗanda s**a san su ba.
Hafiza Bahijja I. Adam ta kasance ɗaya daga cikin irin waɗannan mutane.

Mun haɗu ne a tafarkin Alƙur'ani har na zama Ɗan' gida a gidansu haka itama Hafiza Maryam (Aryam Suf )har zumunci ya kullum s**a zama kamar jini ɗaya, ƙaunar Alƙur'ani da neman yardar Allah.
Wannan ita ce alaƙar da ta fi ɗorewa kuma ta fi albarka.

Mu duka mun taso a Madrasatu Asfa Sunnah Wa'tahfizul Qur'an Samaru Zaria, tare da jagorancin Sheikh Dr. Yusuf Audi Bala (Asfa Sunnah), Mlm Faisal, Mlm Umar Yarima da Sheikh Rabiu Assudaniy Samaru.
A can muka koyi Alƙur'ani, tarbiyya, haƙuri da kishin neman ilimi.

A cikin wannan tafiya ne Hafiza Maryam da Hafiza Bahijja s**a zama ƙawayen juna.
Sun kasance suna ƙarfafa juna wajen haddar Alƙur'ani, suna yin gasa cikin neman ƙaratu, ba don ɗaukaka ba, sai don neman yardar Allah.
Wannan kishin alheri shi ne ya sa s**a kasance abin koyi ga sauran ɗalibai.

Yar' Uwa Bahijja ta kasance mai son halartar duk wani taron Iimin Alƙur'ani ko daura na Addini, za ka ga tana cikin masu halarta, cikin ladabi da tawali'u. Sau da yawa muna haɗuwa bata gajiyawa Sam.

A wani taron Huffazul Qur'an Tv kusan nanne ganin karshe da Huffaz na jahohi da dama s**a santa, Sun yi hotuna cikin farin ciki da annashuwa... amma ashe Allah ne kaɗai Ya san cewa wasu daga cikin hotunan nan za su zama hotunan ban kwana. 💔

Mutuwa gaskiya ce da babu mai tsere mata. 🥹
Amma abin da mutum yake bari a baya shi ne kyawawan ayyukansa da kuma addu'ar mutanen kirki.

Yar' Uwa Bahijja ta rayu cikin biyayya, kunya, ladabi da hidimar Alƙur'ani. Wannan shi ne tarihin da za mu ci gaba da ba da shaida a kanta.📌🥹

Muna fatan Allah Ya karɓi dukkan ayyukanta na alheri, Ya sanya Alƙur'anin da ta rayu da shi ya zama haske a kabarinta da mai cetonta a ranar Alƙiyama.💔😪🤲

Ba za mu taɓa mantawa da ke ba, 'yar'uwa. Duk lokacin da muka tuna tarurrukan Alƙur'ani, za mu tuna murmushinki, jajircewarki da ƙwazonki.😪

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙanki da rahama mai yalwa, Ya gafarta miki kura-kurai, Ya faɗaɗa miki kabari, Ya haskaka shi da hasken imani, Ya sanya Alƙur'ani ya zama hujja a gare ki, Ya kuma haɗa mu da ke a Aljannatul Firdaus.💔😪🤲

Allah Ya jiƙan dukkan Huffaz da malamai da s**a riga mu gidan gaskiya, Ya kyautata mana ƙarshenmu, Ya sa mu cika da imani da Alƙur'ani. Āmīn Yā Rabbal-'Ālamīn. 🤲😪

Kamaludeen Abubakar

14/07/2026

ALLAHU AKBAR ✊

MASANIN ALQUR'ANI KUMA WAYAYYE DAN BOKO

Rayuwar Jiya da Kuma ta yau kenan Tabbas Saidai Ataya
Alhafiz Dr Abubakar Muhammad Ribah Murna Kan yanda Kullum Rayuwarsa tana kan Addini 🤩

Wannan Hoton andaukeshi ne Ashekarar 1994 Lokacin da Alhafiz Abubakar Ribah yatafi Jahar Neja Don Musabaqar Alqur'ani Mai Girma a waccan Shekarar,

Dayan Hoton Kuma an dauke shine a wannan shekarar ta 2026 Baifi sati biyun ba ma da daukar wannan hoton a wurin walimar Aure a garin Zuru dake Jahar Kebbi A Nigeria 🤩

Mahaddaci Alqur'ani mai Girma 💯
Kuma wayayye Dan Boko ✍️

Dacta Abangaren Karatun Boko Kuma Masanin Makamar Addini Wato Fiqihun Musulunci ✊

Allah yaqarawa Rayuwa Albarka Sheikh ✊
Yasa Alqur'ani Mai Girma ya chechemu baki daya Gobe kiyama...🤲
Ameen ya Hayyu ya Qayyum 🤲

Want your school to be the top-listed School/college in Zaria?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address


Zaria