05/02/2024
Tsakanin Dr. Ahmad Gumi da Sayyid Qutb da Izalah da Ikhwan al-Muslimeen
*Dr Ibrahim Lawal Soro*
(Tshohuwar Ajiya, 30. 07. 2017 CE)
Bana tsakkar samuwar barbarar tunani da k**anceceniya a tsakanin Dr. Ahmad Gumi da Sayyid Qutb, k**ar yadda aka samu tsakanin Kungiyar Izalah da Ikhwan al-Muslimeen, daga cikin abubuwan da za su bayyana maka haka akwai:
1. Sayyid Qutb Bakhawarije ne a bangaren mu'amala da mahukunta, haka da Dr. Ahmad Gumi, kurarinsa na fin karfin gwamnati da gagararta bai yi nisa gabarinka ba.
2. Sayyid Qutb Bamu'utazile ne dangane da al'amuran da s**a shafi qaibi; yana gabatar da hankali a kan nakali, haka ma Dr. Ahmad Gumi, domin yana kore shigar Aljani a jikin Dan Adam, kuma yana karyata tasirin sihiri da sauransu.
3. Sayyid Qutb mazagin Sahabban Manzon Allah [R. A] ne, ya zagi 'Uthmaan Bn 'Affaan da Mu'aawiyah Bn Abee Sufyaan [R. A], k**ar yadda Dr. Ahmad Gumi ya sa Mu'adh Bn Jabal [R. A] da cin mutunci.
4. Duk irin aika-aikar Sayyid Qutb da bidi'o'insa kungiyar Ikhwaan al-Muslimeen da ya kasance jigo a cikinta ba ta taba furta kalma ta barranta da shi ba, k**ar yadda Kungiyar Izalah ba ta taba jefar da kalma da nisantar da kanta gabarinsa Dr. Ahmad Gumi a kungiyance ba, kuma martanin wasu malaman kungiyar gare shi ba ya wakiltar kungiyar a zahiri, shi ya sa tasirinsa ya yi karanci a wajen Yan Kungiyar da suke ganinsa har yanzu a matsayin Malaminsu.
5. Matukar mutum ya yi imani da tsare-tsaren Kungiyar Ikhwaan al-Muslimeen da manufofinta shi kenan, domin ba ta damuwa da akidah da tafarkin da yake dauke da ita, hakika irin wannan salo Kungiyar Izalah ta k**a, musamman a baya-bayan nan, batun Dr. Ahmad Gumi bai yi nisa gare ka ba!
Watarana Malaminmu Sheikh Dr. Muhammad Sa'eed Raslaan [H. A] ya taba cewa dangane da Sayyid Qutb:
"Sayyid Qutb kundin bidi'o'i ne."
Ma'ana yana tattare da bidi'o'i kala-kala na jiya da yau. Idan ka bibiyi lamarin Dr. Ahmad Gumi za ka iske ba shi da maraba da nasa, shi ne yau a cikin wannan bidi'ar gobe a cikin waccar, ya rasa matsaya guda daya hatta a kan bidi'anci, dama haka halin wadanda suke gabatar da hankali a nakali yake a kowane zamani da muhalli.