24/03/2026
UMMUL-QURA QUR'ANIC FOUNDATION, ZARIA
Assalamu alaikum wa rahmatullah, Iyayen/Malamai da Sauran Yan uwa masu daraja.
Alhamdulillah, muna farin cikin sanar da ku cewa an gudanar da Walimar Sallah cikin nasara da kayatarwa matuƙa. Haƙiƙa taron ya kasance cike da albarka, nishadi da ilmantarwa.
Daga cikin Manyan Malaman mu Masu Albarka da s**a Sami halarta akwai:
• Sheikh Ahmad Tamim
• Ass. Prof. Jameel Zarewa
• Ass. Prof. Kabir Asgar
• Dr. Abdurrahman Sani Yaƙub
• Sheikh Abu Uwaisat
• Sheikh Umar Sani Yaƙub
• Sheikh Hassan Yamusa
• Malam Usman Abubakar Magaji
• Sheikh Anas Abubakar Albarkawa
• Sheikh Mahmoud Aminu Dantsoho
• Malam Hayatu Garba Dabo
• Goni Auwal Buna
• Da sauransu
Haka kuma, an samu halartar Alarammomi Makaranta Al-Qur'ani, Daliban Ilimi da Sauran Ƴan uwa.
Muna miƙa saƙon godiya ta musamman gare ku, iyaye masu daraja, bisa irin goyon baya, haɗin kai da gudummawar da kuka bayar wajen tabbatar da nasarar wannan walima. Ba tare da ku ba, da hakan ba zai yiwu ba.
Allah Ya saka muku da mafificin alheri, Ya ƙara haɗa kanmu, Ya kuma sanya albarka a cikin wannan aiki namu.
Wassalamu alaikum wa rahmatullah.
Sanarwa:
Hukumar Makaranta