08/08/2026
Shugaban Ƙungiyar Izala ta Ƙasa, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, ya gayyaci al’ummar Musulmi zuwa wani babban taron ƙarawa juna ilimi mai taken “Bambance-Bambance Tare da Zaman Lafiyar Jama’a.”
Taron zai kasance haɗin gwiwa ne tsakanin Ƙungiyar Haɗa Kan Musulmai ta Duniya (Rabitatul Alamil Islamiy) mai cibiya a ƙasar Saudiyya da Ƙungiyar Wa’azin Musulunci ta Ƙasar Najeriya (Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah – JIBWIS).
Za a buɗe taron ne a ranar Talata, 11 ga Agusta 2026, da misalin ƙarfe 9:00 na safe, sannan a kammala ranar Laraba, 12 ga Agusta 2026, da misalin ƙarfe 2:30 na rana.
Bayan taron, za a gudanar da Wa’azin Ƙasa a harabar Masallacin JIBWIS da ke hedikwatar ƙungiyar a Utako, Abuja, daga yammacin Laraba zuwa daren Alhamis.
Sanarwar ta ce ana sa ran halartar manyan baki da s**a haɗa da malamai, gwamnonin jihohi, ministoci, ’yan majalisun tarayya da na jihohi, sarakuna, ‘yan kasuwa da sauran al’ummar Musulmi daga Najeriya da ƙasashen waje.
An bayyana Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin babban baƙon musamman, yayin da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, zai kasance Uban Taron.
Haka kuma, ana sa ran manyan malamai daga ƙasashe daban-daban na duniya za su halarci taron, insha Allah.
Sanarwa: Sakataren JIBWIS na Ƙasa, Sheikh Dr. Muhammad Kabir Haruna Gombe, ta hannun Ofishin Kwamitin Labarai na Babban Taron.