24/08/2025
HAKKIN MIJI AKAN MATA DA HAKKIN MATA AKAN MIJI
Gabatarwa
Aure wata babbar alaka ce ta soyayya da amana tsakanin ma’aurata. Addinin Musulunci ya gindaya hakkin kowane ɓangare domin tabbatar da zaman lafiya da jituwa a cikin iyali. Wannan rubutu zai bayyana hakkin miji akan mata, hakkin mata akan miji, da kuma hakkin tarayya tsakanin ma’aurata, domin a sami fahimtar juna da zaman lafiya mai ɗorewa.
1. Hakkin Miji Akan Mata
Ga wasu hakkokin da mata ke da su a wurin mazajensu:
1. A ciyar da ita gwargwadon iko.
2. A tufatar da ita daidai hali.
3. A shayar da ita.
4. A samar mata da kayan kwalliya.
5. A samar mata da kayan tsafta.
6. A samar mata da gurin kwana.
7. A kula da lafiyarta.
8. A biya mata bukatar saduwa.
9. A ilmantar da ita.
10. A girmama ta.
11. A mutunta ta.
12. A tausasa mata.
13. A yaba mata da abinci, kwalliya ko tsafta.
14. A nuna damuwa da ita.
15. A sakar mata fuska da murmushi.
16. A gaya mata kalmomi masu daɗi na yabo.
17. A zauna da ita ana hira da tattaunawa.
18. A kira ta da suna mai daɗi.
19. A yi mata kyauta ba zato ba tsammani.
20. A fita da ita wajen unguwa ko taro ko tafiya.
21. A taimaka mata da aikin gida ko ɗan ƙaramin abu.
22. A barta ta zabi abincin gida a wasu lokuta.
23. A barta ta zabi tufafinta.
24. A mutunta iyayenta da danginta.
25. A bata hakuri idan an yi mata ba daidai ba.
26. A yaba mata idan ta yi daidai.
27. Kada a zageta ko a muzantata a gaban yayanta.
28. Banda duka.
29. Banda zagi.
30. Banda saurin fushi.
31. A kasance mijin mai tsafta.
32. A kasance miji mai kula da goge baki.
33. A kasance miji mai kwalliya.
34. Kada ya kasance mai almubazzaranci.
35. Kada ya kasance mai kwauro.
36. Kada ya kasance mai shan taba.
37. Kada ya kasance mai shan giya.
38. Kada ya kasance mai yawon dare.
39. Kada ya kasance mai neman mata.
40. Kada ya kasance miji mai hira da wasu mata a gabanta.
41. Kada ya kasance mai yawan faɗa.
42. Kada ya kasance mai kauracewa shimfidar iyali.
43. Kada ya kasance mai nuna rashin damuwa da halin iyali.
44. Kada ya kasance mai tsananin kishi.
45. Kada ya kasance mai yawan zagi.
46. A nuna cewa an gamsu da ita.
47. A bata damar faɗin ra’ayinta.
48. A yi shawara da ita akan harkokin gida.
49. A dinga sumbatar ta lokaci zuwa lokaci.
50. A yi wanka tare a wasu lokuta.
51. A rera mata waka ko kirari.
52. A yi wasa da guje-guje.
53. Kada ya kasance mai zargi.
54. Kada ya kasance mai mugunta.
55. Kada ya kasance mai kushe.
56. Kada ya kasance mai bakin ciki da abin da iyali ke da shi.
57. Kada ya kasance mai ragwanci.
58. Ya kasance mai lafiya wajen biyan bukatar aure.
59. Ya kasance mai kaunar yayansa.
60. Ya kasance mai girmama kawaye da aminan matarsa.
Hakkin Mata Akan Miji.
Ga wasu hakkokin da mazaje ke da su a wurin matansu:
1. Ta riƙe masa amana.
2. Ta yi masa biyayya a duk abin da ba sabawa Allah ba.
3. Ta kula da dukiyarsa.
4. Ta kula da sallah da addu’a don zaman lafiya.
5. Ta girmama shi a gaban idonsa.
6. Ta kare girmansa a bayan idonsa.
7. Ta so abin da yake so, koda ba ta so ba.
8. Ta ƙi abin da yake ƙi, koda tana so.
9. Ta damu da abin da ya damu da shi.
10. Ta kau da kai daga abin da ya ƙi.
11. Ta yi fushi da duk abin da ya yi fushi da shi.
12. Ta yarda da abin da ya yarda da shi.
13. Idan ya bata ƙanana ta ga babba.
14. Idan ya bata da yawa ta yi godiya.
15. Ta farka kafin ya farka.
16. Sai ya yi bacci kafin ta yi.
17. Ta yi hakuri idan ya yi fushi.
18. Ta yi taushi idan ya yi tsauri.
19. Ta lallashe shi idan ya hasala.
20. Kada ta nuna raki a gabansa.
21. Kada ta yi kuka alhali yana dariya.
22. Kada ta yi dariya alhali yana kuka.
23. Kada ta tsaya kai da fata sai ya mata wani abu.
24. Kada ta matsa masa da buƙatu.
25. Kada ta ɗauke shi tamkar yaro.
26. Kada ta riƙa masa gyara barkatai.
27. Kada ta kushe tsarinsa.
28. Kada ta zuga shi a gaban danginta.
29. Ta girmama shi a wajen kawayenta.
30. Ta nuna masa abu mai kyau.
31. Ta ɓoye abu mummuna.
32. Idan ya kawo wata damuwa, ta taimaka masa.
33. Idan baya son wani abu ta daina.
34. Ta kwantar masa da hankali lokacin damuwa.
35. Ta sassauta masa idan yana bakin ciki.
36. Ta tsaya masa idan yana rashin lafiya.
37. Ta taimaka masa lokacin da yake buƙatar taimako.
38. Idan yana cikin kunci ta sassauta buƙatu.
39. Ta yi masa rakiya lokacin fita ta tarbe shi idan ya dawo.
40. Ta tausasa harshe lokacin magana.
41. Ta tsaftace gida iya iyawarta.
42. Ta tsara dakinta yadda zai birge.
43. Ta yi masa bankwana idan zai yi tafiya.
44. Ta yi ado gwargwadon iyawarta.
45. Ta bayyana halaye masu kyau.
46. Ta yi ishara mai hikima.
47. Ta bayyana kanta a matsayin mace.
48. Ta yi murmushi da lafazi mai kwantar da rai.
49. Ta cika zuciyarsa da soyayya da kwalliyarta.
50. Ta ja hankalinsa da abin da yake so.
51. Ta mayar da alheri idan ya mata mummuna.
52. Ta yafe masa idan ya yi mata laifi.
53. Ta karɓi uzurinsa.
54. Kada ta yi sallar nafila sai da izininsa.
55. Kada ta ɗauki azumi sai da izininsa.
56. Kada ta fita daga gida sai da izininsa.
57. Ta iya girki kala-kala.
58. Ta nisanci kazantar jiki.
59. Kada ta shigar da wani gida sai da izininsa.
60. Kada ta nemi saki ko rabuwa haka kawai.
Hakkin Tarayya Tsakanin Ma’aurata.
Hakkin da ya haɗa su duka kuwa sun haɗa da:
1. Nuna juna kauna da soyayya.
2. Taimakon juna a farin ciki da bakin ciki.
3. Kowa ya gyara kansa da tsafta.
4. Kowa ya kasance mai kishin ɗayan.
5. A sami amincewa juna.
6. A bawa juna hakkokin jin daɗi gwargwadon shari’a.
7. Kyakkyawan zamantakewa tsakanin juna.
8. Hakuri da juna.
9. Amincewa da juna.
10. Faranta juna rai.
11. Yin shawara tare.
12. Girmama iyayen juna da danginsu.
13. Taimakon juna idan aka shiga jarabawa.
14. Kada su tona asirin juna a waje.
15. Kada su ci amanar juna.
16. Kada su bayyana mu’amalar auratayya.
17. Akwai gado tsakaninsu idan ɗaya ya rasu.
Kammalawa
Aure ibada ce mai tsarki, wadda ake buƙatar ma’aurata su fahimci hakkin juna domin zaman lafiya da tsira. Idan aka kiyaye waɗannan hakkoki, za a samu iyali nagari, ƙasa nagari, da al’umma nagari.
Allah ya ba mu ikon kiyaye hakkin juna, ya cika zukatanmu da soyayya da kauna da girmamawa a tsakaninmu.
Mallam Aminu Ibrahim Daurawa