02/07/2026
TARIHIN RAYUWAR FARFESA ANGO ABDULLAHI, CON: JAGORAN KUNGIYAR DATTAWAN AREWA, KUMA JAGORAN ILIMIN NOMA DA KIWO.
Daga Bangis Yakawada ✍️
Farfesa Ango Abdullahi, CON, na ɗaya daga cikin fitattun masana a fannin noma, tsohon Shugaban Jami'ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya ne, kuma fitaccen dattijon Arewa wanda ya shafe shekaru da dama yana ba da gagarumar gudummawa wajen bunƙasa ilimi, noma, shugabanci da ci gaban Najeriya. Har ila yau, shi ne Convener kuma Shugaban Kwamitin Amintattu (Board of Trustees) na Kungiyar Dattawan Arewa (Northern Elders Forum – NEF), inda ya kasance ɗaya daga cikin manyan muryoyin da ke kare muradun Arewa da Najeriya baki ɗaya.
Haihuwa da Farkon Rayuwa
An haifi Farfesa Ango Abdullahi a ranar 13 ga watan Disamba na Shekarar 1938, a garin tsohuwar Giwa da ke Karamar Hukumar Giwa, Jihar Kaduna. Ya taso cikin iyalai masu kishin ilimi da tarbiyya. Ya fara karatunsa a Kali Elementary School a shekarar 1944, sannan ya kammala firamare a Giwa Elementary School. Daga nan ya wuce Zaria Middle School kafin ya shiga fitacciyar makarantar nan da tayi shura wajen horas da manyan shuwagabannin Najeriya wato Barewa College, daje garin Zariya, inda ya yi karatu tsakanin shekarun 1953 zuwa 1958.
Karatunsa da Ƙwarewarsa
Bayan kammala karatun sakandare, ya ci gaba da neman ilimi a Nigerian College of Arts, Science and Technology, Zariya daga shekarar 1959 zuwa 1961. Daga bisani ya yi karatu a Jami'ar Ibadan tsakanin shekarun 1961 zuwa 1964.
Daga nan ya tafi Jami'ar Kansas State da ke Ƙasar Amurka, inda ya samu Digiri na Babbar Kwarewa (MSc) a fannin Noma a shekarar 1968, sannan ya kammala Digirin Digirgir (PhD) a fannin Agronomy a shekarar 1976.
Ayyuka da Gudummawa
Da ya dawo Najeriya, Farfesa Ango Abdullahi ya fara aiki a Institute for Agricultural Research (IAR), Samaru, inda ya yi fice wajen bincike da koyarwa har ya zama Farfesa tun yana da kusan shekaru 40, a duniya.
A shekarar 1979 aka naɗa shi Shugaban Jami'ar Ahmadu Bello (Vice-Chancellor), mukamin da ya riƙe har zuwa shekarar 1984. A lokacin shugabancinsa, jami'ar ta samu ci gaba sosai ta fuskar ilimi da gudanarwa.
Baya ga harkokin ilimi, ya shiga siyasa inda ya taɓa zama ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Zaria North West. Haka kuma ya kasance Mai Bai wa Shugaba Ƙasa Olusegun Obasanjo Shawara kan Harkokin Abinci da Tsaro tsakanin shekarun 1999 zuwa 2003.
Sarautarsa
Baya ga gudummawar da ya bayar a fannonin ilimi, noma da shugabanci, Masarautar Zazzau ta naɗa Farfesa Ango Abdullahi sarautar Magajin Rafin Zazzau wanda ya gaji magabatan sa a shekarar 2007 domin karrama irin hidimar da ya yi wa al'umma da ƙasa. Ya ci gaba da riƙe wannan sarauta har zuwa shekarar 2025, lokacin da ya ajiye ta da kansa saboda tsufa. Bayan ajiyewarsa, Sarkin Zazzau ya naɗa ƙaninsa, Alhaji Shehu Abdullahi, a matsayin sabon Magajin Rafin Zazzau.
Iyali da Zuriyarsa
Farfesa Ango Abdullahi ya gina iyali mai cike da ilimi da hidimar ƙasa, inda wasu daga cikin 'ya'yansa s**a yi fice a fannoni daban-daban.
Babban ɗansa, Marigayi Isah Ango Abdullahi, ya kasance ma'aikacin gwamnati wanda ya ba ƙasa gudummawa a ɓangaren tsaro da leƙen asiri. Kafin rasuwarsa, ya yi aiki a Hukumar Leken Asiri ta Ƙasashen Waje a Najeriya wato (Nigerian Intelligence Agency – NIA) da ke Abuja. Ya rasu a shekarar 2022, inda rasuwarsa ta haifar da alhini ga iyalansa, abokansa da duk waɗanda s**a san shi.
Daga cikin sauran 'ya'yansa akwai Hon. Mohammed Shamsuddeen Ango Abdullahi, wanda ya kasance ɗan Majalisar Wakilai na Tarayya a Majalisa ta Bakwai daga shekarar 2011 zuwa 2015, inda ya wakilci mazabar Birnin Gwari/Giwa ta Jihar Kaduna.
Haka kuma akwai Hon. Sadiq Ango Abdullahi, wanda yake ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya a halin yanzu, yana wakiltar mazabar Sabon Gari ta Jihar Kaduna tun daga shekarar 2023.
Matsayinsa a Yanzu
A matsayinsa na Convener kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na Kungiyar Dattawan Arewa (Northern Elders Forum – NEF), Farfesa Ango Abdullahi ya ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan dattawan Najeriya masu ba da shawarwari kan harkokin siyasa, tsaro, zaman lafiya da ci gaban Arewa.
Har ila yau, yana ci gaba da kira ga gwamnati da al'umma da su ba noma muhimmanci, yana mai jaddada cewa bunƙasa noma da samar da wadataccen abinci su ne ginshiƙan bunƙasar tattalin arzikin Najeriya.
A tsawon rayuwarsa, Farfesa Ango Abdullahi ya kasance abin koyi ga ɗalibai, malamai, manoma, shugabanni da matasa. Gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa ilimi, noma da shugabanci ta sanya sunansa cikin jerin fitattun mutanen da s**a taka muhimmiyar rawa a tarihin Najeriya.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara wa Farfesa Ango Abdullahi lafiya, nisan kwana da albarka. Ya saka masa da alheri bisa irin gudummawar da ya bayar ga ilimi, noma da ci gaban Najeriya, Ya kuma jiƙan yayansa Marigayi Alhaji Samaila Abdullahi Yakawada, da Ɗansa Isah Ango Abdullahi da rahama, Ya gafarta masu kura-kuransu, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsu da sauran Al'ummar Musulmai baki daya. Amin.