20/11/2025
Visit TikTok to discover videos! Watch, follow, and discover more trending content.
Skilled tailoring and embroidery services, creating quality outfits with care, style, and precision. Custom designs made to fit you perfectly.
20/11/2025
Visit TikTok to discover videos! Watch, follow, and discover more trending content.
16/10/2025
Praise be to Allah. Self-confidence is vital, as it earns you the trust of others. The world values individuals who demonstrate unwavering faith in their abilities.
12/06/2022
*💧Wani Daga Cikin Tabi'ai Yana Cewa :"Duk Wanda Zunuban sa s**a taru, to ya dinga shayar da ruwa, domin Allah ya Gafartawa Wanda ya Shayar da kare, to ya Kuwa Wanda ya Shayar da mutum mumini "💧*
Allah ya taimaka mana.
24/11/2021
NASIHA😭😭
Wani mutum ke kuka, sai wani ta tambayeshi dalilin kukan nashi. Sai yace:
Inada d'a d'aya, nayi iya bakin qoqarina wajen ilimantar dashi yadda zai zama wani babban mutum agaba.
Cikin ikon Allah yasamu wadannan certificate din👇
🌺 J.S.C.E
🌺S.S.C.E
🌺Bachelor's degree
🌺MSc.
🌺PhD
Amma!
Kwatsam ya kwanta rashin lafiya kuma likitoci sunce ba abinda zasu iya yimashi a yanayin dayake ciki don bazai wuce mintina talatin ba a duniyarmu.
Sai d'an nawa yace in daukomashi certificates din karatunshi sai nayi hakan.
Saiya kalleni yafashe da kuka yace:
"Baba wadannan Duk degrees dinane Amma Baka ta6a sani na koyi karatun Al Qur'ani ba.
Me zance da Allah? Bansan abinda zance mishi ba😭"
Mafi yawan cikinku bazakuyu sharing ba sbd ba labarin ban dariya bane ko na nishadi.
Idan kanada niyyar sharing kayi hakan saboda Duk Wanda ya karanta a sanadinka zaka samu lada.
Idan kuma yagani ya yad'a wasu s**a gani s**a karanta kaima akwai naka kason ladar.
MU KULA DA WADANNAN ABUBBUWAN👇
🌺mu dinga nazarin Al Qur'aninmu kamar yadda muke nazarin littatafanmu na boko
🌺muji tsoron Allah kamar yadda mukejin tsoron mutuwarmu ko mutane masu wani muqami ko mulki
🌺mu yawaita tuna Allah kamar yadda muke tuna sunanmu
🌺mu dinga addu'a don makamin muminice
Allah mai iko. Mai rayawa mai kashewa. Duniya ba wajen zama bane.
Amadadin duk members na wannan kungiyar agaji na Munazzzamatul fitiyanul islam muna mika ta'aziyyar rashin Shugaba kuma jarumi kiwa ya shaida wajen aikin allah ba a barin sa a baya. Yau an wayi gari babu shi 😢 allah ya gafarta mai ya kara wa iyalensa da yan agaji hakurin rashinsa.
Allah ya yafe kurakurensa ya haska kabarinsa
AMEEN THUMMA AMEEN
14/04/2021
ANYA ZAMU TSIRA A HAKA KUWA?
🍎 Naira 200 tayi mana yawa wajen bayar da sadaka, amma kuma tayi kadan wajen yin liki a biki ko gun wata sabga ta duniya!
🍎 Minti 60 na yin zikiri a masallaci ko a gida yayi mana yawa, amma minti 90 yayi mana kadan a wajen kallon kwallo!
🍎 Awa 1 ko 2 sun yi mana yawa a gurin daukar karatu, amma kuma sun yi mana kadan a wajen kallon fina finai!
🍎 Zaman karanta ayoyi 🕌20 na Al-qur'ni yakan yi mana kunci, amma cikin annashuwa mukan shafe kimanin awa 3 ko 4 muna karanta shafukan yanar gizo ko jaridu!⌨
🍎 Aguje mukan gaskata labarin jaridu,📰 amma idan an zo fagen Al-qur'ani da hadisin Manzon Allah (s.a.w) 🕋sai yawan shakka da tuhuma, musamman idan sun ci karo da son zuciyarmu!
🍎 Muna da son karanta labaran ban dariya a facebook ko whatsapp,📱 amma da zarar mun ci karo da "posting" na fadakarwa ko abin da ya shafi addinin musulunci🕌, sai mu tsallake!
🍎 Mukan saka talabijn🚊 a gaba na tsawon awanni muna kallo, amma sai mu kasa tsaiwa minti 15 muna kallon Gabas,🕋 domin yin ibada!
🍎 Haddar wakoki🎧 basa yi mana wuya, amma mukan ga wahalar haddar ayoyin Al-qur'ani mai girma!🕋 ALLAH Yakaramana imani ameen idan ka yarda da wannan tunasarwa to katura zuwa ga wasu Don su amfana
13/04/2021
01/01/2021
Wani Sarki Ne Ya Tara Waziransa Guda Uku, Ya Basu Buhu Yace: "Kowanne Ya Tafi Gidan Gona Ya
Samo Mini Kayan Marmari"
Wazirai S**a Tafi.
* NA FARKO: Ya Ce:"Ai Da Alama Sarkina Yana Son Ya Ci Ne, Saboda Haka Ya Dukufa Da Nemo Kayan Marmari Masu Kyau".
* NA BIYU: Ya Ce:"Ai Sarki Ba Wani Tsayawa Zai Yi Yana Kula Ba, Saboda Haka Bari Na Kwaso Masa Masu Kyau Da Marasa Kyau Da Danyu".
* NA UKU: Kuma Ya Ce:"Ai Kawai Sarki Bama Zai Duba Ba, Saboda Haka Bari Kawai Na Kwaso Ganyaye, Da Shara Na Cika Buhu".
Kwatsam!
Suna Dawowa Sai Sarki Yasa a Kai Su Kurkuku, Kada a Bawa Kowa Abinci Kowa Ya Ci Abinda Ya Kwaso Har Tsawon Wata Daya.
• To Anan Fa Waziri Na FARKO Yayi Ta Cin Kayan Marmarinsa Lafia Lau.
• Na BIYU Kuwa Yayi Nadama Saboda Ya Hado Da Marasa Kyau.
• NA UKU Kuwa Yaita Cin Shara Da Ganyen Da Yabo Har Ya Mutu.
TSOKACI: "Ku sanya a ranku cewa kune aka sa awannan kukurku (KABARI) kun ga duk abinda kuka
tsinko na Alkhairi ko Sharri a duniya shi xaku gani, Sabi da haka, Yan uwana masu daraja mu dage wajen kwaso
abubuwan alheri, domin samin sakamako mai kyau. Ya"Allah kayafe mana kurakuran mu ka haskaka qabarin mu kasamu a aljannah firdausi mata masu juna biyu kasauke su lafiya ya Allah ka aurar damu da gaggawa ameen
BARKAN MU DA JUMA A
09/12/2020
| Monday | 09:00 - 17:00 |
| Tuesday | 09:00 - 17:00 |
| Wednesday | 09:00 - 17:00 |
| Thursday | 09:00 - 17:00 |
| Friday | 09:00 - 17:00 |
| Saturday | 09:00 - 17:00 |
| Sunday | 09:00 - 17:00 |