Imam warshan Qur'anic class

Imam warshan Qur'anic class We are here to spread the rules of Qur'anic recitation in the imam warsh way of recitation.

10/12/2025

TARIHIN IMAM WARSHU A TAKAICE
Sunanshi: Abu Saeed Usman bn Sawed Al Misry, Malaminsa Nafiul Madany Shine Ya Masa Laqabi Da Warshu Saboda Tsananin Farin Fatarsa,.
An Haifeshi A Misra A Shekara Ta 110H, Sai Ya Tafi Madina Wajen Imam Nafiul Madany, Har Yayita Saukan Qurani, Sai Ya Koma Misra Yayita Koyar Da Mutane Na Tsawon Lokaci.
Ya Rasu A Misra A Shekara Ta 177 H. Allah Gafarta Masa.

*  FALALAR ADDUA'A RANAR ARFA !@ A Ranar Arfane Allah ke Amsa/Karbar Adduan Bayinsa Na Neman Samun Wani Alheri Ko Neman ...
12/06/2024

* FALALAR ADDUA'A RANAR ARFA !

@ A Ranar Arfane Allah ke Amsa/Karbar Adduan Bayinsa Na Neman Samun Wani Alheri Ko Neman Mariya/Tsari Daga Wani Sharri.

@ Komai Girman Bukatarka In Dai Ranar Arfane To Kawai Ka Tsaya Da Gaske Ka Roka A Wajen Mawadacin Da Yake Bayarwa Nada Lissafiba, Wanda Saboda Wadatarsa Cikakkiya Da Zai Ba Was Kowani Bawa Abunda Ya Roka To Da Babu Abunda Zai Ragu A Cikin Wadatarsa Sai Kwatankwacin Irin Abunda Yake Makalewa A Jikin Allura In Aka Tsoma Alluran A Teku .

@ Kar Kayi Sakaci Da Addua A Wannan Rana Ta Arfa ,Don Ba Karamar Dama Bace Allah Ya Nuna Maka Wannan Rana, Kuma Ba Karamar Nasara Bace Ace Ka Tsaya Da Gaske Ka Dage Wajen Addua Ma Kanka Da Kasarka.

Allah Bamu Ikon Yin Addua Daidai Ya Kuma Karba Mana.

Wassalamu Alaikum.

ALLAHU AKBAR! ALLAHU AKBAR!!LAILAHA ILLALLAH!ALLAHU AKBAR! ALLAHU AKBAR!!WALILLAHIL-HAMD.Sune zikirorin da akeyi a kwani...
09/06/2024

ALLAHU AKBAR! ALLAHU AKBAR!!
LAILAHA ILLALLAH!
ALLAHU AKBAR! ALLAHU AKBAR!!
WALILLAHIL-HAMD.

Sune zikirorin da akeyi a kwaniki uku ko hudu na babban sallah.

Kuma sune zikirorin da akeyi akwanaki goma na watan zulhijja(watan lahiya) tun daga ran daya ga wata ake fara yinsu.

Ibnu kathir ya rawaito acikin tafsirinsa na suratul-hajji cewa:Ibnu Umar da sauran sahabbai sun kasance acikin kwanaki goman nan suna bi cikin kasuwa suna yin wannan kabbarori a fili don tunatar da mutane.

Allah bamu ikon koyi dasu.

Munayi wa dukkan musulmai fatan alheri, da adduar Allah ya biya wa kowa bukatunsa na alheri, ya yaye masa damuwarsa, ya ...
29/03/2024

Munayi wa dukkan musulmai fatan alheri, da adduar Allah ya biya wa kowa bukatunsa na alheri, ya yaye masa damuwarsa, ya bunkasa masa arzikinsa, ya albarkaci iyalansa, kar Ku manta da falasdinawa, mutanen zamfara, katsina, Kaduna Maiduguri acikin adduoinku, asha ruwa lafiya.

GARABASA! GARABASA!! GARABASA!!!KA ZO KA SAYA KAFIN WANI YA RIGAKA.CIKI DA PARLOUR HUDU DA BAYAN GIDA ACIKIN KO WANI DAK...
31/07/2023

GARABASA! GARABASA!! GARABASA!!!
KA ZO KA SAYA KAFIN WANI YA RIGAKA.
CIKI DA PARLOUR HUDU DA BAYAN GIDA ACIKIN KO WANI DAKI, DA DAKIN YARA SHIMA DA BAYAN GIDANSA, DA WAJEN KIWO, DA RIJIYA DA FILIN PARKING A KOFAR GIDAN.
LOCATION: BAYAN VOCATIONAL ANAN CIKIN GARIN BAUCHI.
FARASHI:?????
IN KANA BUKATA KA KIRA: 08148014077,09072310360.
WSLM

Address

Ilelah Street Bauchi State Of Nigeria
Wuntin Dada

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Imam warshan Qur'anic class posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Imam warshan Qur'anic class:

Shortcuts

Share

Category