Al-Wesam For Qur'an

  • Home
  • Al-Wesam For Qur'an

Al-Wesam For Qur'an Al-Wesam For Qur'an cibiya ce da take yaɗa ilimin Alƙur'ani da dukkanin ɓangarorin shi cikin harshen Hausa.

Barka da Sallah! Muna taya dukkanin masoyanmu murnar wannan rana mai albarka. Muna roƙon Allah Ya sa mu kasance daga cik...
26/05/2026

Barka da Sallah!

Muna taya dukkanin masoyanmu murnar wannan rana mai albarka. Muna roƙon Allah Ya sa mu kasance daga cikin waɗanda aka yanta a wannan wata mai daraja, Ya kuma sa mu kasance masu riƙo da littafinsa mai tsarki a kowane lokaci. Barka da Sallah, Allah Ya sa mu dace. 🕌✨

"

22/05/2026

Baka karanta Alƙur'ani....😢

22/05/2026

Goron Juma'a
Mu sanyaya zukatan mu da Alƙur'ani 🩵💦

16/05/2026

Mu sanyaya zukatan mu da Alƙur'ani 🩵💦



Daurawa

15/05/2026

Mu sanyaya zukatan mu da littafin Allah 🩵💦

Ka yi ƙoƙarin haddace Alƙur'ani kafin ka bar duniya.Idan hakan bata samu ba, to ka mutu kana hanyar haddacewa. in sha Al...
13/05/2026

Ka yi ƙoƙarin haddace Alƙur'ani kafin ka bar duniya.

Idan hakan bata samu ba, to ka mutu kana hanyar haddacewa. in sha Allah, Allah zai cika maka ladan ka⛈️💧

Ladubba da Sunnonin Ranar Sallah (Eid-el-Fitr):• Yin Takbiri: Sunnah ne yin kabbara a cikin gidaje, masallatai, da kan h...
19/03/2026

Ladubba da Sunnonin Ranar Sallah (Eid-el-Fitr):

• Yin Takbiri: Sunnah ne yin kabbara a cikin gidaje, masallatai, da kan hanyoyi, tun daga daren Sallah har zuwa lokacin da liman zai fito don sallar. Daga cikin siffofin kabbara akwai: (Allahu Akbar, Allahu Akbar, La ilaha illallahu, Allahu Akbar, Allahu Akbar, wa lillahil Hamd).

• Yin Wanka da Sanya Turare: Ana so mutum ya yi wankan tsarki, ya tsaftace jikinsa, ya sanya turare, sannan ya sanya mafi kyawun tufafinsa don girmama wannan rana ta ibada.

• Cin Abinci Kafin Fita Sallah: Musulmi ba ya fita zuwa filin sallar Idi har sai ya ci dabino, kuma sunnah ne ya ci su guda ɗaya, uku, ko biyar (mara).

• Sallar Idi a Masallaci ko Filin Idi: Sunnah ne maza da mata har da yara su fita zuwa filin sallah domin halartar wannan alheri. Sallar Idi raka'a biyu ce,
ba ta da kiran sallah (Adhan) ko tada sallah (Iqama).
• Sauya Hanyar Tafiya: Ana so mutum ya bi ta wata hanya daban yayin tafiya sallah, sannan ya dawo gida ta wata hanyar daban.

• Bayar da Zakkar Fitir: Jaddada bayar da zakkar fitir kafin mutane su fita zuwa sallar Idi, domin ta zama tsarkaka ga mai azumi da kuma abinci ga mabuƙata.

• Nuna Farin Ciki da Taya Murna: Musayar gaisuwa da taya juna murna da kalmomi kamar "Eid Mubarak" ko "Taqabballahu minna wa minkum", da kuma nuna farin ciki da annashuwa a cikin gidaje.

• Ziyarar Zumunci: Ziyartar dangi, maƙwabta, da abokai domin ƙarfafa dankon soyayya da zumunci a tsakanin al'umma.

Eid Mubarak 🎉 🎊 🎈 “Barka da Sallah! Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya sa Alƙur’ani ya zama haske a rayuwarmu, Ya kuma sanya mu...
19/03/2026

Eid Mubarak 🎉 🎊 🎈

“Barka da Sallah! Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya sa Alƙur’ani ya zama haske a rayuwarmu, Ya kuma sanya mu daga bayinsa na ƙwarai.”

Zakatul Fitr 🌾"Manzon Allah (S.A.W) ya Farlanta Zakatul Fitr domin tsarkake mai azumi daga yasassun maganganu da kura-ku...
19/03/2026

Zakatul Fitr 🌾

"Manzon Allah (S.A.W) ya Farlanta Zakatul Fitr domin tsarkake mai azumi daga yasassun maganganu da kura-kurai, kuma abinci ne ga miskinai."

Bayanan Shari'a Game da Ita:

Ma'anarta: Sadaka ce tabbatacciya wadda ake bayarwa a madadin kowane Musulmi kafin a fita sallar idi, ga waɗanda s**a cancanta.

Hukuncinta: Zakatul Fitr wajibi ce.

Wane ne ke bayarwa?: Ta zama wajibi a kan kowane Musulmi; babba ko yaro, namiji ko mace, ɗa ko bawa.

Hikimarta: Tana tsarkake mai azumi (daga kura-kurai) kuma tana zama abinci ga miskinai (don su ma su yi murna ranar idi).

Lokacin bayarwa: Mafi kyawun lokaci shi ne fitar da ita a ranar idi kafin a fita sallar idi.

Yawan abincin: Gwargwadon Sa'i ɗaya na abinci (kamar masara, shinkafa, alkama), ko dabino, ko busasshen inabi, da makamantansu.

Address

Alhaji Malami Street Daurawa Quarters Tarauni Local Government

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al-Wesam For Qur'an posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Al-Wesam For Qur'an:

Shortcuts

  • Want your school to be the top-listed School/college?

Share