Bintu Rasoul For Qur'anic Memorization and Islamic Studies Uba Adamawa

  • Home
  • Nigeria
  • Uba
  • Bintu Rasoul For Qur'anic Memorization and Islamic Studies Uba Adamawa

Bintu Rasoul For Qur'anic Memorization and Islamic Studies Uba Adamawa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Bintu Rasoul For Qur'anic Memorization and Islamic Studies Uba Adamawa, Uba.

Bintu Rasoul for Qur’anic Memorization & Islamic Studies
A makarantar Central Primary School, Uba – Adamawa
� Koyar da Al-Qur’ani, Hadisi, Fiqh & Tarbiyya
� Daukar darasi bisa manhaja mai tsafta da fahimta

Allah Yakaimu Maulana
11/06/2026

Allah Yakaimu Maulana

ABUJA QAFILATUL MAHABBAH

Topic:> SAQAFAR RAYA MAJALISUN UNGUWANNI Dan Tabbatar da Tsaro Da Haɗin kai A Unguwannin mu da Garuruwan mu

Date :> Juma'a 12-06-2026

Lokaci:> tsakanin Magriba Da Isha

Mai Muhadara :> Maulana Sheikh Prof. Ibrahim Maqari hafizahullah (Imam National Mosque Abuja)

Wuri :> Masallacin Juma'a Na Tunawa da Alh Sanusi Ɗantata dake Central Area Abuja

09/06/2026

With Qafilatul Mahabbah Islamic Foundation Uba Branch – I just made it onto their weekly engagement list by being one of their top engagers!

07/06/2026
Alhamdulillah.Makarantar Bintu Rasoul for  Qur'anic Memorization  and Islamic Studies Uba Adamawa, ƙarƙashin jagorancin ...
06/06/2026

Alhamdulillah.

Makarantar Bintu Rasoul for Qur'anic Memorization and Islamic Studies Uba Adamawa, ƙarƙashin jagorancin Imam Aliyu Ndotti, ta ɗauki nauyin gyaran Central Borehole na garin Uba Adamawa bayan ya samu matsala.

Wannan aiki wata ƙaramar gudummawa ce ta hidimtawa al'umma da neman yardar Allah (SWT), domin ruwa na daga cikin manyan buƙatun rayuwa.

Muna fatan wannan aiki zai zama abin koyi ga sauran makarantu, ƙungiyoyi, masu hannu da shuni, da ɗaukacin al'umma, ta yadda za mu riƙa haɗa kai wajen magance matsalolin da s**a shafi jama'a ba tare da jiran gwamnati kaɗai ba.

Ci gaban al'umma nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa gwargwadon ikon da Allah Ya ba shi.

"Muna roƙon Allah (SWT) Ya karɓi wannan aiki a matsayin sadaka mai gudana. Muna kuma kira ga sauran makarantu, ƙungiyoyi da masu hannu da shuni su yi koyi da irin waɗannan ayyukan ci gaban al'umma.

Idan wannan aiki ya burge ku, ku yi share kuma ku rubuta addu'arku a comment. Allah Ya saka da alheri. Āmīn."

06/06/2026

Walima program

05/06/2026

walima

Muna godiya  Mualana
02/06/2026

Muna godiya Mualana

31/05/2026

Musabaƙar Marayu da Ƙungiyar Ahlul Khair Uba ta gabatar.

Muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya Yusuf Jidda ya zama abin alfahari ga iyalansa da al’ummarsa, Ya ba shi ilimi mai amfani, lafiya, arziki na halal da kyakkyawan ƙarshe. Allah Ya sa ya zama Gorzon Izu na ɗaya, mai nasara a rayuwa da lahira.

Haka kuma muna addu’ar Allah Ya jiƙan mahaifinsa da ya rasu, Ya gafarta masa zunubansa, Ya yalwata masa rahama, Ya haskaka masa kabari, Ya sanya shi cikin mazauna Aljannar Firdausi.

Allah Ya ba Yusuf Jidda da iyalansa haƙurin jure rashin mahaifinsu, Ya ci gaba da tsare su, Ya albarkaci rayuwarsu da dukkan al’amuransu.

Amin Ya Rabbal Alamin. 🤲🏽

Address

Uba

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bintu Rasoul For Qur'anic Memorization and Islamic Studies Uba Adamawa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share