Masjid Abubakar Assiddeeq Goljaredi Magama Gumau Toro LGA Bauchi State.

  • Home
  • Nigeria
  • Toro
  • Masjid Abubakar Assiddeeq Goljaredi Magama Gumau Toro LGA Bauchi State.

Masjid Abubakar Assiddeeq Goljaredi Magama Gumau Toro LGA Bauchi State. This is a Mosque that preaches about Islam based on the Quran and Hadith.

Wa'azi na JIBWIS reshen Magama a wannan masallaci. Allah ya saka da alkhairi ya karba mana kyawawan ayyuka.
29/04/2026

Wa'azi na JIBWIS reshen Magama a wannan masallaci. Allah ya saka da alkhairi ya karba mana kyawawan ayyuka.

Rufe tafsirin mata na bana 27 Ramadan 1447/2026 tareda Uztaz Jamilu Abdullahi Secretary JIBWIS FAG Toro LGA da Alaramma ...
16/03/2026

Rufe tafsirin mata na bana 27 Ramadan 1447/2026 tareda Uztaz Jamilu Abdullahi Secretary JIBWIS FAG Toro LGA da Alaramma Khuzaima Sani.

Rufe tafsirin bana 27 Ramadan 1447/2026 tareda Uztaz Jamilu Abdullahi da Alaramma Suleiman Alkali.
16/03/2026

Rufe tafsirin bana 27 Ramadan 1447/2026 tareda Uztaz Jamilu Abdullahi da Alaramma Suleiman Alkali.

14/03/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Uzairu Sani, Abdurra'uf Idris Musa, Sani Muhammad, Mu'azu Salihu, Sani Sagiru

ZIYARAR RESHEN TILDE NA MATAIMAKIN SHUGABA II JIBWIS TORO LGA IMAM ALKALI LAWAL TAREDA UZTAZ JAMILU SECRETARY FAG TORO L...
12/03/2026

ZIYARAR RESHEN TILDE NA MATAIMAKIN SHUGABA II JIBWIS TORO LGA IMAM ALKALI LAWAL TAREDA UZTAZ JAMILU SECRETARY FAG TORO LGA.

tafsirin da Ustaz Jamilu Abdullahi (Sakataren JIBWIS, FAG Toro LGA) ya gabatar, an fito da muhimman fā’idodi daga aya ta...
28/02/2026

tafsirin da Ustaz Jamilu Abdullahi (Sakataren JIBWIS, FAG Toro LGA) ya gabatar, an fito da muhimman fā’idodi daga aya ta 220 kamar haka:
1️⃣ Halaccin amfani da dukiyar maraya da niyyar kyautatawa da bunƙasawa
Ayar ta nuna cewa wanda ke kula da maraya yana iya mu’amala da dukiyarsa idan:
domin gyarawa ne da bunƙasawa,
ba tare da zalunci ko cin dukiya ba.
Wannan bai takaita ga ciyarwa kawai ba; ya haɗa da:
saka jari a kasuwanci,
sayen abin da zai ƙara darajar dukiya (misali kadara),
duk wani abu da zai amfanar da marayan nan gaba.
👉 Dalili: “Wa in tukhāliṭūhum fa ikh’wānukum” — idan kuka haɗa dukiya da su, to ‘yan’uwanku ne (wato ana yarda idan alheri ne).
2️⃣ Halaccin ƙulla zumunci da maraya ta hanyar aure
Ayar ta nuna halaccin ƙarfafa dangantaka da maraya ta:
aurar masa da ‘yarka,
ko aurar da shi/ita ga ɗanka,
idan wannan yana cikin maslahar maraya kuma ba cutarwa ba.
Wato, kulawa da maraya ba ta hana zama danginsa ta aure.
3️⃣ Sabani kan auren marainiya da ke karkashin kulawa
Malamai sun yi sabani:
Imam Mālik: bai halatta mai kulawa ya auri marainiyar da ke karkashinsa ba (domin tsoron cin zarafi ko anfani da iko).
Imam Abū Ḥanīfa: ya halatta idan:
babu nufin zalunci,
an ba ta hakkinta cikakke (sadaki da yardarta).
👉 Dalilin sabani: haɗa aya 220 da aya 3 na Suratul-Nisā’i (wacce ta yi gargadi kan auren marayu da zalunci).
✅ Taƙaitaccen Darasi daga Aya 220:
Shari’a ta ba da dama a kula da dukiyar maraya cikin hikima.
Dangantaka da maraya ana ƙarfafawa, har da aure idan maslaha ce.
Amma an tsaurara gargadi kan duk wani yiwuwar zalunci ga maraya.
Domin karin bayani saurari tafsirin Mal na 09 Ramadan 1447/2026.

TAFSIRIN RAMADAN 1447H📖 Suratul-Baqarah – Aya ta 222🗓 11 Ramadan 1447H / 2026🎙 AA Malam Jamilu AbdullahiSecretary, JIBWI...
28/02/2026

TAFSIRIN RAMADAN 1447H
📖 Suratul-Baqarah – Aya ta 222
🗓 11 Ramadan 1447H / 2026
🎙 AA Malam Jamilu Abdullahi
Secretary, JIBWIS – FAG Toro LGA
✨ FA’IDODI DA DARUSSA
1️⃣ Sharancin Nisantar Saduwa lokacin Haila
An haramta saduwa kawai, ba a haramta zama tare da mu’amala da mace mai haila ba.
2️⃣ Haila Alama ce ta Haihuwa
Tana nuna lafiyar tsarin haihuwa ko yiwuwar samun haihuwa.
3️⃣ Bambanci: Haila – Nifasi – Istihada
Haila:
• Jinin al’ada na mace
• Yana hana sallah da azumi
• Mafi yawanci: kwanaki 6–7
Nifasi:
• Jinin bayan haihuwa
• Yana hana sallah da azumi
• Mafi yawa: kwanaki 40
Istihada:
• Jinin cuta (ba al’ada ba)
• Ba ya hana sallah ko azumi
• Mace za ta yi alwala ga kowace sallah
4️⃣ Amfanin Tsarki yayin Wanka
Ana son turare, auduga ko sabulu bayan haila domin tsafta.
5️⃣ Haramcin Saduwa ta Dubura
An haramta gaba ɗaya.
6️⃣ Allah na Son Masu Tuba
Tuba na kawo kusanci ga Allah.
7️⃣ Allah na Son Masu Tsarki
Masu kiyaye dokokin haila suna cikin tsarkaka.
8️⃣ Nau’ukan Tsarki Biyu
• Zahiri: wanka, alwala
• Ma’anawi: nisantar shirka da saɓo

📖 Tafsirin Suratul-Baqarah (218–219) — Faidodi da Darussa1️⃣ Aya ta 218:Aya ta yi bayani kan muminai masu gaskiya waɗand...
24/02/2026

📖 Tafsirin Suratul-Baqarah (218–219) — Faidodi da Darussa
1️⃣ Aya ta 218:
Aya ta yi bayani kan muminai masu gaskiya waɗanda s**a yi imani, s**a yi hijira, kuma s**a yi jihadi a tafarkin Allah.
Ta nuna cewa imani na gaskiya tare da aiki nagari yana kai mutum ga rahamar Allah da tsira daga sharrin duniya da lahira.
Darasi:
Jajircewa a kan imani da ayyukan alheri — musamman a lokacin gwaji da fitina — yana da lada mai girma a wurin Allah.
2️⃣ Aya ta 219:
Aya ta yi magana kan giya da dukkan nau’in abubuwan maye (khamr).
An bayyana cewa suna da wasu anfani kaɗan, amma illarsu ta fi anfani.
Darasi:
Duk wani abu da ke lalata hankali, jiki, ko zamantakewar mutum — kamar giya da kwayoyi — haramun ne kuma barazana ga rayuwa da al’umma.
3️⃣ Illar shaye-shaye:
Malam ya ja hankali kan cewa kwayoyi da giya na haddasa:
Lalacewar lafiya da hankali
Rugujewar tarbiyya da rayuwar iyali
Yawaitar laifi da rashin tsaro a al’umma
Fa’ida:
Kiyaye hankali da lafiya na daga manyan manufofin Shari’a (maqasid).
4️⃣ Kulawa da tarbiyyar yara:
An jaddada muhimmancin kulawa da yara da abokan hulɗarsu, domin shaye-shaye na yawan farawa ne daga matasa.
Fa’ida:
Tarbiyya da kulawa tun ƙuruciya na kare yara daga fadawa cikin lalacewar halayya da shaye-shaye.
5️⃣ Kira ga masu shagunan magani (Chemists):
Malam ya yi kira ga masu sayar da magunguna da su rika lura da masu sayen magungunan da ake amfani da su wajen maye (misali: tutolin).
Idan sun fahimci ana son amfani da su wajen shaye-shaye, su guji sayarwa domin kada su shiga cikin taimakon barna.
Fa’ida:
Hana kai ga haram (sadd-uz-zari’ah) wajibi ne — duk wanda ya taimaka ga barna yana da kaso a laifi.
💡 Saƙon Tafsiri:
Ayoyi 218–219 na koyar da:
Gaskiyar imani da jajircewa
Aiki nagari da neman rahama
Kiyaye hankali da lafiya
Kare yara daga lalacewa
Hana shaye-shaye da duk abin da ke kai ga maye
📚 Domin ƙarin bayani:
A saurari cikakken Tafsirin ranar 7 Ramadan da Malam ya gabatar tareda Alara ma Suleiman Alkali.

Uztaz Jamilu Abdullahi Secretary JIBWIS FAG Toro LGA.
23/02/2026

Uztaz Jamilu Abdullahi Secretary JIBWIS FAG Toro LGA.

21/02/2026

Jawabin mataimakin Shugaba II na JIBWIS TORO Imam Alkali Lawan Toro yayin bude tafsir na wannan shekarar 1447/2026 wanda Uztaz Jamilu Abdullahi ke gabatarwa.

15/02/2026

إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ
اللَّهُمَّ أْجُرْنَا فِي مُصِيبَتِنَا وَاخْلُفْ لَنَا خَيْرًا مِنْهَا

Da alhini da tawakkali ga Allah muke sanar da rasuwar matar Imam Alkali Lawan Goljaredi,wanda shi ne mataimakin Shugaba na II na JIBWIS, Toro LGA.

Marigayiyar ta kasance ’yar agaji ta Nisa’ussunnah a Masjid ABKR ASSDQ Goljaredi,haka kuma ɗaya daga cikin kwamitin Tafsirin Mata na masallacin.
Ta rasu ne a daren yau.

🕌 Za a yi jana’izarta:
Yau Lahadi, da ƙarfe 9:30 na safe
A ƙofar gidansu, Goljaredi — In shā Allah.

Muna roƙon ‘yan’uwa Musulmi da su halarta domin samun lada tare da yi mata addu’a.

Allah Ya gafarta mata, Ya jiƙanta da rahama, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zamo makomarta.

Allah Ya saka mata da alkhairi kan hidimar da ta yi wa addini.
Allah Ya ba mijinta, iyalai, da al’ummar Musulmi haƙurin jure wannan rashi.
Ameen. 🤲

Address

Goljaredi Magama
Toro

Telephone

+2348135667924

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Masjid Abubakar Assiddeeq Goljaredi Magama Gumau Toro LGA Bauchi State. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category