18/06/2022
KIRA GA MEMBOBIN AKAFSAN A MATAKIN FARKO DAMA DUK WANI DAN AS'HABUL-KAHFI | Daga Akafsan Management
Allah (SWT) cikin Surah al-Mujaadila, Aya 12, yana cewa;
( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نَاجَيْتُمُ الرَّسُولَ فَقَدِّمُوا بَيْنَ يَدَيْ نَجْوَاكُمْ صَدَقَةً ۚ ذَٰلِكَ خَيْرٌ لَّكُمْ وَأَطْهَرُ ۚ فَإِن لَّمْ تَجِدُوا فَإِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ )
المجادلة (12) Al-Mujaadila
"Yã kũ waɗanda s**a yi ĩmãni! Idan zã ku gãnã da Manzon Allah, to, ku gabãtar da ƴar sadaka a gabãnin gãnãwarku, wannan ne mafi alhẽri a gare ku, kuma mafi tsarki. Sai idan ba ku sãmi (abin sadakar ba), to, lalle, Allah, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai".
Faɗin Allah subhanahu wata'ala cewa; "A gabãtar da sadaka". Bawai don Annabi (ﷺ) mabuƙaci ne ba, Allah yace a gabatar masa da sadaka, a'a..! Allah (SWT) ya faɗi haka ne domin tsarkake muminai (Khairan Lakum Wa Aɗhar). Annabi (ﷺ) Mawadaci ne gaba ga duk wani abu da wani wanda ba Allah ba zai bashi, ya tabbata a tarihi cewa "Dandazon Mutane ne suke cin abinci a gidan Annabi (ﷺ) kullum". Wanda ba mawadaci ba, baza a sami haka daga gareshi ba. Ku rabu da maganar ana kwana arba'in ba a dora tukunyar abinci ba, a gidan Annabi (ﷺ), hankali bazai karɓi wannan ba. Wanda dandazon mutane suke jiransa domin ya basu abinda zasuci, kuma shine yake kwana arba'in ba ayi abinci a gidansa ba? Wannan ba gaskiya bane.
Kasancewar yanzu Annabi (ﷺ) baya tare damu a zahiri, wannan aya zata yi aiki kan waɗanda suke massala aikin da Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yayi. Kamar yadda ya tabbata a wani hadisi "Malamai sune magada Annabawa" da kuma faɗin Allah a cikin 'Suratu Taubah', ayar Sadaka, zuwa fadin Allah "Wa Fisabilillah" wadanda suke kan tafarkin daukaka addinin Allah. Wannan a bayyane yake cewa akwai Malaman da suke massala wannan gado na Annabawa, ko shakka babu Sheikh Abduljabbar Kabara ɗaya ne daga ciki, don haka;
AKAFSAN tana kira ga ɗaukacin Membobinta dama duk wani ɗan As'habul-kahfi kan kulawa ta sosai ga lamarin Sheikh Abduljabbar Kabara, k**ar yadda kowa ya sani, yanzu kusan shekara guda kenan Malam yana tsare, bayan buƙatu (magidanci, babban mutum, kuma babban malami) na yau da kullum da tsadar rayuwa, ga kuma Shari'ar da aka ɗauki lokaci ana fafatawa tsakanin Malam shi kaɗai da raunanan dake tare dashi, da kuma Gayyar Masu Mulki, Attajirai, Sarakuna, Hamshaƙan Malaman Maja, Ƴan Siyasa da Gwamnatoci, shari'a wacce take fara lissafi daga Miliyoyin Nairori, wanda zuwa yanzu ta lashe fiye da lissafin ƴan yatsu.
Aiki da ayar da muka kawo a farkon wannan rubutu (Suratul Mujadila, Aya ta 12), lallai kowannen mu yana ganawa da Malam kusan kowacce rana (ta hanyar Sauraron Karatukansa), ''Najwa" da akace a wannan aya, ana nufin neman wani ƙarin haske gameda lamarin addini. Wanda mu Ɗaliban Malam har yanzu da aka rufe makarantun, muna Saurarar karatukansa da ƙarfin ikon Allah, kuma muna samun haskake-haskake daga karatukan Malam da aka ɗauka a tsawon shekaru (na kusa da na nesa).
Don haka muke kira a ci gaba da bada gudunmawar neman albarka da tsarkaka (k**ar yadda Allah (SWT.) Ya fada a Alkur'ani mai girma.
Hanya ɗaya sahihiya itace, ta Account ɗin;
As'habul-kahfi Warraqeem Development Association, wato Asusun Banki Mallakin Jagoran As'habul-Kahfi, k**ar haka:
LAMBAR ASUSU (ACCOUNT NUMBER): 1140109791
SUNAN ASUSU (ACCOUNT NAME): Assahabulkahfi Warraqim Development Association
ASUSUN AJIYA (BANK): Polaris Bank
_______________
JAN HANKALI:
Duk wanda ya tura, yayi mana comment da hoton shedar tura kuɗin wato (teller, ko resit, ko screenshot na debiting alert a kasan wannan rubutu ( https://www.facebook.com/100141528415016/posts/573108557784975/). A shafin ƙungiya na Facebook.
Membobin AKAFSAN kuma da suke da register a wannana ƙungiya sai su tura ta WhatsApp group na ƙungiyar AKAFSAN, saboda ƙungiya za tayi documenting ɗin duk wanda s**a tura.
Allah ya bada ikon bayarwa, Amin.
AKAFSAN MANAGEMENT
18/6/2022