Makarantar Kimiyya Da Fasaha

Makarantar Kimiyya Da Fasaha

Share

An environment dedicated to learning, innovation, and technical advancement in Hausa language.

An kirkiri wannan makarantar domin ilimantar da mutane hausawa masu neman samun ingantaccen ilimin Kimiyya Da fasahar zamani. An tsara koyarwa da horaswa a yaren Hausa ta yadda zasu samu saukin fahimtar abinda ake koyar da su domin anyi da yaren su. An shirya koyarwar ta hanya mafi sauki wajen gane karatu wato mataki-bayan-mataki, daga karamin mataki har zuwa mataki na karshe.

20/07/2020

SHAFUKAN SADARWA NA YANAR-GIZO GUDA 10 DA ZAKA IYA SAMUN N42,000 ZUWA N127,000 DUK WATA

RUBUTU: KASHI NA TARA

Amazon Associates

Amazon Associates ko Amazon Amazon Affiliates tsarin hadin guiwa ne da Kamfanin Amazon wanda yake mallakar Jeff Bezos ne mutumin da yafi kowa kudi a duniya a halin yanzu.

An shirya wannan tsarin ne domin samun riba tsakanin kamfanin da kuma mutanenda ke cikin wannan shirin. Ribar kamfani itace zaka tallata kayansu domin a sayar kai kuma ribarka itace kudin da za’a biyaka.

Ya wannan shirin ke aiki?

Wannan tsarin k**a daga shigar shi har zuwa yanda yake aiki abu ne mai sauki sosai. Idan kanada ra’ayi da wannan tsarin kawai zakaje ne kayi rajista daga nan zasu baka “referral link” kuma shi wannan “link” din akwai “referral Id” naka a cikinsa ta yanda duk lokacin da wani ya tabo wannan link din to zasu gane cewa daga gareka yazo kuma duk abunda ya saye zaka samu naka kaso daga sayayyar da yayi.

Abu biyu da suke abin burgewa ne sosai a wannan kasuwancin:

* Na daya: abunda ake bukata ya zamana kanada BLOG ko Mobile App kafin fara wannan aikin amma idan kanada YouTube Channel itama zatayi lafiya kalau. Haka kuma, idan kanada Account a Facebook ko Twitter to zasu taimaka maka sosai wajen tallata kayan saidai idan kanada shafin da mutane ke biya sosai to zaka fi samun riba mai yawa.

* Na biyu: duk lokacinda ka tallata wani abu sai wani yabi ta link din to koda bai saye wannan abin ba to zaka samu naka kamisho. Misali: idan ka tallata Talabijin sai wani yabi tallar amma bai sayi talabijin din ba, kawai sai yaga wata salula ta birgeshi sai ya siya to zaka samu kaso a wannan salular da ya saya.

Idan kanada blog ko tashar YouTube da ake biya sosai to cikin sauki zaka iya samun dalar amurka dubu daya $1000 a wata, kwatankwacin N387,500.

Zaku iya shiga Amazon Associates ta wannan link https://affiliate-program.amazon.com/home

Allah yasa mu dace!

Rubutu na karshe zaizo bada jimawa ba akan YouTube.

Aminu Tanimu Arzika
20 Yuni, 2020

17/07/2020

SHAFUKAN SADARWA NA YANAR-GIZO GUDA 10 DA ZAKA IYA SAMUN N42,000 ZUWA N127,000 DUK WATA

RUBUTU: KASHI NA TAKWAS

Website Testing Jobs

Harkar Website Testing Job (Auna Rayuwa ko Lafiyar Shafin Yanar Gizo) ta hanyar yanda yake aiki, saurin aikin shi, tsarin zanenshi, dacewar shi da kuma yanayin tsaron shi.

Akwai kamfunna dayawa dake bukatar su san yadda mai ziyara ke ji yayin da yake amfani da shafinsu kafin su wallafa shafin ko kuma bayan sun walalfa domin suyi gyara ya yanda zai kasance daidai da jin dadin mai amfani dashi.

A matsayinka na mai gwaji, abunda kawai kake nema shine “Screen Recorder Software” wato manhajar da zakayi rekodin na shafin a yayinda kake ziyartar shafin sannan ka gaya musu iya fahimtar ka gameda shafin.

Daga nan, sai ka tura wannan rahoto naka, idan s**a diba s**a ga cewa yayi daidai da bukatar su to za’a biyaka.

Domin samun riba sosai a wannan sana’ar yanada kyau ka shiga kuma kayi rajista da shafukan da ake wannan aikin dayawa.

Ga biyar daga cikin wadanda s**afi shahara:

* https://www.usertesting.com/be-a-user-tester

* https://www.userlytics.com/tester/

* https://www.analysia.com/user.asp

* https://www.utest.com/

* https://trymyui.com/worker/signup

Allah yasa mu dace!

Rubutu na gaba zaizo bada jimawa ba akan Amazon Associate.

Aminu Tanimu Arzika
17 Yuni, 2020

13/07/2020

SHAFUKAN SADARWA NA YANAR-GIZO GUDA 10 DA ZAKA IYA SAMUN N42,000 ZUWA N127,000 DUK WATA

RUBUTU: KASHI NA BAKWAI

Proofreading

Idan ka iya yaren turanci sosai kuma kasan nahuwanshi to zamowa Proofreader shine babban zabi gareka.

Akwai dubbanin littatafai, rubuce-rubuce, Labarai, littafan hikaya da wallafe-walafe da sauransu a cikin shafukan Proofreading. Aikin da zakayi a cikin wannan kasuwancin na Proofreading shine, nema da kuma gyara kuskure ko ince kura-kurai a cikin wadannan abubuwan da na zayyano a sama dama wasunsu.

Domin yin wannan aikin kana iya samun dalar amurka goma zuwa hamsin ($10-50) duk awa daya (1hour) ko fiye da haka — Kimanin Naira 3,875 zuwa Naira 19,375 ko fiye da haka duk awa daya.

Bisa ga wannan, idan kasan ka kware sosai akan wannan aikin to zaka iya kafa naka karamin kamfani da zaka dinga aikin proofreading ko kuma kayi aikin a matsayin kwararren mai aiki (Freelancer) ta hanyar:

* https://fiverr.com/
* https://upwork.com/
* https://freelancer.com/
* https://indeed.com/
* https://craigslist.org/ da sauransu.

Duk da haka kuma, akwai kamfanoni dayawa da suke bayarda damar yin aikin Proofreading ga wadanda suke matakin farawa ko kuma tsaka tsaki.

Ga guda biyar daga cikinsu:

* https://proofreadingpal.com/
* https://editfast.com/
* https://wordvice.com/
* https://www.peopleperhour.com/
* https://www.wordy.com/

Allah yasa mu dace!

Rubutu na gaba zaizo bada jimawa ba akan “website testing job”, harkar auna lafiyar shafukan yanar gizo.

Aminu Tanimu Arzika
13 Yuni, 2020

12/07/2020

SHAFUKAN SADARWA NA YANAR-GIZO GUDA 10 DA ZAKA IYA SAMUN N42,000 ZUWA N127,000 DUK WATA

RUBUTU: KASHI NA SHIDA

RentAfriend

Amma akwai ban mamaki a wannan al’amarin, ta ya zan samu kudi kawai saboda na zamo abokin wani. To saurara kaji, wannan na faruwa ne kawai a RentAFriend.com

Wannan wani tsari ne da zaka iya hayar aboki a lokacin da ka shiga wata kasa ko gari kuma baka san kowa ba, to idan kayi rajista a RentAFriend zaka samu damar da zaka iya daukar wasu haya kuma su su yi maka abinda kake bukata ka biyasu. To a wannan zaka samu kudi idan wani ya daukeka haya.

Abubuwan da zaka iya yiwa wanda ya nemeka abota a RentAFriend:

* Yawon Shakatawa
* Kallon Fim
* Rakkiya zuwa cin abinci a wata restaurant
* Rakiyya zuwa wurin buki ko wani taro
* Koyarwa akan al’ada ko wata dabi’a
* Nuna masa gari ko kauyuka

Wannan shafin an tanadeshi ne kawai saboda abota da taimakawa abokantaka da abubuwan da aka lissafa. Ba zaka iya aiki dashi ta wasu hanyoyi na soyayya ko mak**ancin haka ba, duka an haramta wannan a RentAFriend.

Idan kanada ra’ayin aiki da wanna shafin kuma kanada gurin samun kudi dashi to kawai kaje kayi rajista a shafin, ka cike Sunanka, Adireshinka, Ra’ayinka, Lambar waya da za’a iya kiranka ko turama sako da wasu sauran bayanai sannan ka saka hotonka, duk lokacinda wani yazo ya duba yaga yanada ra’ayi dakai to zai nemeka ko ya kira wayarka ko ya turama sako ko kuma ya tura maka sako ta cikin sashen tattaunawa da RentAFriend s**a tanada.

Idan aka gayyace ka, kana iya cajin wanda ya gayyace ka daga dalar amurka goma ($10 — N3,874) ko fiye da haka, ya danganta da irin yanayin aikin da yake bukata da kuma lokacin da za’a bata. Idan kuma biki ne ko wani taro zaka iya kara farashi.

zaku iya shiga RentAFriend ta wannan link: rentafriend.com

Allah yasa mu dace!

Rubutu na gaba zaizo bada jimawa ba akan “StartProofReading”.

Aminu Tanimu Arzika
12 Yuni, 2020

10/07/2020

SHAFUKAN SADARWA NA YANAR-GIZO GUDA 10 DA ZAKA IYA SAMUN N42,000 ZUWA N127,000 DUK WATA

RUBUTU: KASHI NA BIYAR

Skillshare

Tabbas kanada wata baiwa. Hakika nasan akwai wata Baiwa ta wani ilimi da Allah ya h**e maka wadda idan ka sanarda wani ita, to zai samu cigaba a rayuwa. Idan kasan kanada wannan baiwar kuma kanada dabarar da zaka koyama wasu ita cikin faifan bidiyo, to wannan ne lokaci mai kyau da ya k**ata kashiga Skillshare.

Tsarin Skillshare tsari ne mai kyau sosai da kuma Inganci. Akwai sauki a wannan tsarin kwarai dagaske, ana samun kudi sosai sannan kuma ana amfanar da mutane.

Ya Skillshare yake aiki?

Idan kanada wani abu dakake iya koyarwa to Kawai zakayi rajista ne sai ka shirya ka dauki wannan karantarwa ta hanyar bidiyo sai ka daura bidiyon a Skillshare daga nan zaka fara samun kudi ba tareda ka sake wani aiki ba.

A Skillshare akwai dubbanin dalibai da suke koyon kwasa-kwasai kala daban-daban k**a daga dubarun kasuwanci, Zane, Kimiyya, lissafi da sauransu.

Ta wannan hanyar su kuma malamai suna koyarwa suna samun kudi abun su. Abin burgewa ga Karantarwa a Skillshare babu bukatar wani kwali ko takarda domin fara karantarwa, idan kasan ka iya kawai kayi sai ka daura, ana kallawa kana samun kudi, Dalibai na kara kallawa kana kara samun kudi.

A Skillshare akwai wasu Dalibbai da ake kira “Premium Students” to wadannan dalibban suna baka damar kara samun kudi sosai. Duk lokacinda “Premium Student” ya kalli bidiyo dinka na tsawon minti talatin (30mins) to za’a biyaka kudin wannan watan.

Iya tsawon mintuna da aka kalli bidiyo dinka iya kudin da zaka samu. Bayan kayi rajista, kanada damar gayyatar abokananka zuwa Skillshare kuma duk mutum daya yayi rajista da link dinka to zaka samu dalar amurka ($10) dai-dai da N3,873.

Akwai masu koyarwa a Skillshare dayawa da suke samun kudi kimanin dalar amurka $300 zuwa dala $100 kwatankwacin N116,200 zuwa N387,310 kowane wata. Wannan ba karamar dama ba ce, da fatar zamu gwada domin muci wannan gajiyar.

Zaku iya yin rajista a Skillshare ta wannan link https://skl.sh/2ZV5y3L

Allah yasa mu dace!

Rubutu na gaba zaizo bada jimawa ba akan “Get Paid for Being Someone’s friend (RentAFriend).

Aminu Tanimu Arzika
10 Yuni, 2020

09/07/2020

SHAFUKAN SADARWA NA YANAR-GIZO GUDA 10 DA ZAKA IYA SAMUN N42,000 ZUWA N127,000 DUK WATA

RUBUTU: KASHI NA HUDU

Swagbucks

Swagbucks shine shafin da yafi kowane shafi shahara da kuma samun amincewar mutane wajen biyan kudi domin yin kananan abubuwa a cikin shafin k**ar:

* Kallon bidiyoyi musamman masu tallace-tallace
* Bada amsa ga tambayoyin jin ra’ayi (surveys)
* Sayyayar kaya a shagunan yanar-gizo (online-shopping)
* Binciken shafukan yanar-gizo (web searching) domin zakulo wasu bayanai.
* Gayyatar abokai domin su shigo cikin tsarin (referrals)

Duka wadannan ayukkan ana biya idan kayi dai daga cikinsu saidai Swagbucks yazo da wani tsari na daban, saboda suna biya ne da Swagbucks Point (SB), su kuma wadannan “points” din duk guda dari (100) waton 100SB a matsayin dalar Amurka daya ($1) suke.

Abin burgewa gameda Swagbucks, zakayi abubuwan da ka saba yi ne kuma a biyaka. Alal misali, Da yawanmu mukan shiga Google ko Bing muyi bincike da na’urar bincikensu domin samun wani abu, to idan kayi bincike da na’urar bincike ta swagbucks biyanka za’ayi. Haka, Mukan shiga YouTube mu kalli bidiyo, to idan ka kalli bidiyon Swagbucks biyanka za’ayi.

Swagbucks sunada hadin guiwa da manyan shagunan yanar gizo k**ar su Amazon da Walmart da sauransu fiye da shaguna 1500. Idan kabi ta hanyar Swagbucks kayi sayayya a wadannan shagunan to zaka samu “SB Points” daidai sayayyarka.

Gameda amsa tambayoyin jin ra’ayi (surveys) suna da sauki sosai kuma sunada “SB Points” da yawa, kullum kana iya amsa tambayoyi dayawa kuma ka tara kudi da yawa daidai kwazon ka.

Har wa yau, Swagbucks sunada wani shafi da ake kira “Discover Offers” ko “Discover Deals” waton shafin samun damar-maki. Idan ka buda taska (Account) da Swagbucks kuma kayi nasarar shiga cikin shafin to a cikin wannan shafin zaka samu wasu damar-maki dayawa, zaka dinga ganin abubuwan da zakayi su baka SB Points masu yawa da kuma wasu ababen shaguna da aka rage wa farashi. Misali: akwai tambayar jin ra’ayi da zaka samu SB 15 to a cikin “Discover” zaka iya samun SB 100 gareta. Haka kuma, akwai abunda Amazon ko wani shago zasu saka a farashin dala $5 amma a cikin shafin “Discover” na Swagbucks zaka iya samunshi a dala $3 ko $3.5.

Da zarar kudinka s**a kai adadin da za’a iya cirewa to zaka iya cirewa ta PayPal ko kuma GiftCards.

Wannan shine takaitaccen bayani gameda Swagbucks. Domin samun wannan dmar zaku iya shiga swagbucks kuma kuyi rajista a kyauta ta wannan link https://www.swagbucks.com/p/register?rb=76586833

Allah yasa mu dace!

Rubutu na gaba zaizo bada jimawa ba akan Skillshare.

Aminu Tanimu Arzika
09 Yuni, 2020

07/07/2020

SHAFUKAN SADARWA NA YANAR-GIZO GUDA 10 DA ZAKA IYA SAMUN N42,000 ZUWA N127,000 DUK WATA

RUBUTU: KASHI NA UKU

Fotolia

“Fotolia” ko kuma “Adobe Stock” a yanzu. Shafin da kuka sani a matsayin Fotolia a dori yanzu ya canza suna zuwa Adobe Stock.

Idan ka kware a daukar Hoto, Bidiyo, Yin Zane ko zanen 3D ko kuma “Templates” da za’a iya saraffawa ayi wani aiki dasu kala dabam-dabam to tabbas Fotolia ce hanya mafi sauki da zaka saida wadannan hotunan masu kayatarwa da ka dauka ko ka zana. Sai dai dole ka kasance ka wuce shekara 18 sannan dukkan abubuwan da zaka daura su zamana mallakin ka ne.

Akwai ‘yan kasuwa da dama da wakilan kamfuna da suke neman irin wadannan abubuwan domin wallafe-wallafen su ko kuma sakawa a shafinsu na yanar-gizo, idan s**aci karo da aikinka kuma yayi daidai da abunda suke bukata to tabbas zasu biya domin suyi amfani dashi.

Domin farawa abunda kawai kake bukata shine ka shiga wannan shafin ka buda taskarka (Account Mallakinka) domin ka fara daura kayanka. Daga nan duk wanda ya gani kuma yanada ra’ayi zaiyi aiki da Fotolia ya biyaka sannan ya samu yayi amfani dashi kai kuma zaka dinga ganin abunda ka tara a allon bayanai na taskar ka. Duk lokacin da wani ya saye to zaka ga samunka ya karu.

Duk abunda ka sayar zaka samu naka kaso, idan ka sayarda hoto ko zane ko tsagwaron fayil na zane wanda za’a iya sarrafawa to zaka samu kaso 33% daga ciki sannan idan ka sayarda bidiyo zaka samu kaso 35%.

Da zarar kudinka yakai $25 ko N9,600 zaka iya cirewa ta hanyar amfani da PayPal ko Skrill.

Zaku iya shiga Fotolia kuma ku ci wannan gajiyar ta wannan link: https://contributor.stock.adobe.com/en/onboarding/sync-fotolia-1

Rubutu na gaba zaizo bada jimawa ba akan Swagbucks.

Aminu Tanimu Arzika
07 Yuni, 2020

06/07/2020

SHAFUKAN SADARWA NA YANAR-GIZO GUDA 10 DA ZAKA IYA SAMUN N42,000 ZUWA 127,000 DUK WATA

RUBUTU: KASHI NA BIYU

Fiverr: tabbas nasan kunsha jin wannan zancen “idan ka kware akan wani abu to kada kayishi a kyauta” to wannan shine aikin da Fiverr zai maka, idan kasan ka kware akan wani abu to tabbas kayi rajista da wannan shafin.

YA FIVERR YAKE AIKI?

Wannan abu ne mai sauki.

Idan kasan ka kware akan wani abu irin Zane ko Editin din hoto, Zana shafin sadarwa, samarda manhaja, hada sauti, bidiyo ko rubutu da dai sauransu to Fiverr shine babbar hanyar da zakayi amfani da ita wajen samun kudin shiga da sayarda wannan fasaha cikin sauki.

Matakin farin zakayi rajista da Fiverr wanda yake kyauta ne daga nan sai ka kirkiri abunda ake cema “gig” wato fasahar da kake so ka saida zuwa ga kwastomominka.

A Fiverr zai iya yimaka wuya wajen samun kwastomomin farin saidai Insha Allah idan ka karanta wannan rubutun zai zamo maka da sauki sosai wajen samun kwastomomi.

Kwastomomi a Fiverr suna duba tsokaci (Review) da aka aikewa mai aiki (Freelancer) da kuma awon-inganci (Rating) da akayi akan ayukkan ko wane mai aiki kafin su fara bashi aiki. Saboda haka dole ka jajirce kayi ayukka masu kayatarwa da za’a yaba.

A Fiverr akwai wani tsari da ake kira “Gig Extra” ta wannan tsarin zaka iya tara wasu kudi masu yawa bayan kudin aikinka. Yanda “Gig Extra” ke aiki shine: alal misali kana harkar zana shafukan sadarwa kuma ka saka cewa a cikin kwana 5 ko 7 kake kare aiki idan an baka, sai wani kwastoma yazo yace yana son aikin cikin kwana 3, to a nan “Gig Extra” zai baka dama ka cajeshi wasu kudi bayan na aikinka k**ar yadda ka saba.

Fiverr nada dadin aiki sosai kuma zaku iya tara ko nawa a wata kuma zaka iya debe kudinka ta amfani da katin ATM “credit ko debit card”domin cire kudinka.

Zaku iya shiga kuma kuyi rajista a Fiverr ta wannan hanyar http://www.fiverr.com/s2/d6bd8786c3

Rubutu na gaba zaizo bada jimawa ba akan Fotolia.

Aminu Tanimu Arzika
06 Yuni, 2020

05/07/2020

SHAFUKAN SADARWA NA YANAR-GIZO GUDA 10 DA ZAKA IYA SAMUN N42,000 ZUWA 127,000 DUK WATA

RUBUTU: KASHI NA DAYA

Wadannan shafuka da na zayyano a kasa sune shafukan sadarwa guda goma (10) da zaku iya samun kudi masu tsoka duk wata. Kafin mu ci gaba, akwai shafuka masu yawa da suke ikirarin cewa idan kayi abubuwa masu sauki zasu baka kudi, sam ko kadan wadannan ba irinsu bane, a duniyar nan babu abinda zakayi ka samu kudi cikin sauki dole sai an Jajirce.

1 • GoTranscript

2 • Fiverr

3 • Fotolia

4 • Swagbucks

5 • Skillshare

6 • Get Paid For Being Someone’s Friend

7 • Start Proofreading

8 • Website Testing Jobs

9 • Amazon Associates

10 • YouTube

_____________________________________________

1 • GoTranscript: Shafi ne da zaka samu kudi ta hanyar sauraren sauti(audio) ko kallon bidiyo(video) kana fassarawa ko rubutawa kana dorama sautin ko kuma bidiyon wannan rubutun dakayi.

Gameda yadda GoTranscript s**a wallafa, matsakaicin mai fassara a GoTranscript yana samun N63,750 duk wata yayinda manyan masu fassara ke samun akalla N510,000 duk wata.

Idan ka zamo mai fassara a GoTranscript aikinka shine kawai ka saurari sauti ka rubutashi a cikin wurin rubutu da aka tanada, duk aikin da kayi zaka iya samun N255 a duk minti 1.

Domin zamowa memba a GoTranscript kana bukatar samun nasara akan jarabawar Gwaji da sukewa duk wanda keda ra’ayin shiga wannan manhajar.

Idan ka samu zamowa memba a koda yaushe zaka dinga ganin ayyukan-da-ke tafiya a tsarin da s**ayi na aikin da aka fara sakawa aikin da za’a fara kammalawa.

Idan ka kammala aiki akwai kwararru da zasuyi duba akan aikin, idan akwai kuskure dole ka gyara sannan ka koma turawa kafin a aikawa ainihin mai aikin.

Idan kana wadannan ayyukan ana biyanka ko wane sati ta hanyar PayPal.

Duk da yake wannan aikin nada sauki amma ba irin saukin nan sosai ba, saboda wadannan sautukan zakaji wasu sautuka daga gefe masu ‘yar kwaramniya ko kuma guntuwar matsalar turanci amma ba wai ko wane sauti ba ne a haka, idan ka bincika zaka samu wadanda sautinsu yake radam.

Zaku iya ziyartar shafin ta nan: https://gotranscript.com/transcription-jobs

Rubutu na gaba zaizo bada jimawa ba akan Fiverr.

Aminu Tanimu Arzika
05 Yuni, 2020

26/06/2020

YANDA ZA’A CIKA NPOWER

Wannan bayanin nayi shi domin yan uwa su amfana tayanda zasu cika wannan Npower a saukake kuma yanda ya dace, kuma nayi fassara ne kawai daga yanda s**a bayyana ashafinsu na twitter.

Wannan shine official portal din:
www.npower.fmhds.gov.ng

Shi wannan portal din an tsara shi ne da gabobi guda 7 wayanda zanyi bayani, kuma hoton passport kar ya wuce 1mb:

1. VALID EMAIL ADDRESS: Dole ne mai son yayi applying wannan program ya samar da Email address wanda yake aiki dashi kuma yake duba sakonnin da aka aika mashi.

2. EMAIL CONFIRMATION: Bayanin da kasamar za’a tura shi zuwa Email dinka domin tantancewa da tabbatarda yana aiki.zaa tura ma link ne wanda zaka danna domin confirmation.

3. BVN: Da zarar kayi confirming Zaka ga inda zaka sa lambobi 11 na BVN dinka, sai kuma Ranar Haihuwarka wato date of birth ta wannan tsari dd/mm/yy, misali 26/06/2020.
ABIN LURA: idan BVN dinda kasa ba daidai take ba, to ba zaka wuce wannan sashe ba.

4. BIODATA AND CONTACT: Shi wannan bangare shine inda da zaka samar da bayanai akanka: Sunanka, Sunan mahaifinka da kuma wani sunan idan kana amfani da suna uku ne.
ABIN LURA: sunanda zaka sa yakasance a tsare k**ar yanda yake a BVN dinka wato Sunan mahaifi farko, sunanka ya biyo baya sannan wani suna idan akwai.

5. EDUCATION AND PROGRAM: Ta wannan page ne xaka sanya bayanan karatunka, kayi karatu ko bakayi ba, domin an samar da shirin ne domin kowa da kuma zabar irin Program dinda kake da shaawar zaka cika.

ABIN LURA: Program din N-tech da N-health na wadanda das**a kammala karatu ne ta wannan bagarorin, kuma N-health anfi bada karfi ne gamasu Bsc., HND, OND na kimiyyar lafiya k**ar MEDICINE, MICROBIOLOGY, NURSING, PUBLC HEALTH, BOTANY, MIDWIFE, PSYCOLOGY ko kuma wasu bangarori masu alaka da kimiyyar lafiya. zaka yi uploadind din DEGREE da NYSC certificate idan aka bukata.

6. EMPLOYMENT AND OTHER DETAILS: wannan zaka sanya wasu bayanai ne da kuma wata sheda (ID Card) daga waata hukuma ta gwamnati, k**ar DRIVING LICENCE, INTERNATIONAL PASSPORT, NATIONAL ID CARD KO VOTERS CARD

7. REVIEW AND SUBMISSION: wannan sine na karshe ida zaka ga baya nan da ka sanya sai kayi SUBMIT ABIN LURA: dakayi sunmit zaa baka wasu NUMBERS sai kwashe su ka adana
ALLAH YASA MU DACE

- Abdulsalam Aminu

25/04/2020

WATAN SAMUN FALALAR ALLAH

Watan Ramadana wata ne da Musulmai a duk fadin Duniya ke dukufa wajen Ibada domin samun falalar da ke cikin wannan watan, a saboda haka ne Dandalin Kimiyya Da Fasaha ke taya dukkanin musulmai a fadin duniya murnar riskar wannan watan tareda fatar zamu Dage sosai wajen Ibadah domin samun albarka da yafiyar Ubangiji a wannan watan. Mungode da yadda kuke karanta rubuce-rubucen mu. Allah ya karbi ibadunmu mu duka!

Sako daga:
Dandalin Kimiyya Da Fasaha
2 ga watan Ramadan, 1441 A.H

Want your school to be the top-listed School/college in Sokoto?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address


Abuja
Sokoto