31/05/2025
HAQIQANIN KAR6A66EN HAJJI(A MAHANGAR MAKARANTAR FODAWIYYA)
Kasani yaa kai Dan'uwana (Allah yahaskaka rayuwarka da hasken saninsa) cewa aikin HAJJI wajibine kamar yadda Shehummu Uthmanu Dan'fodiyo (QS) yake cewa
Farilla tana kammu muyi anniya,
Ta HAJJI da sharadi idon mun iya,
Akul babu iko muzam tambaya,
Ina masu ikon gwadin dukiya,
Suba masu himmar ziyara tasa.
Kamar yadda Shehummu yafada (cikin wadancan baituka) HAJJI yanada sharudda wadanda suke kwayar da ake nema cikin kowace kar6a66ar ibada. Sharuddan sune kamar haka:
Afarko yakamata kayi farin'ciki da murna akan wannan Babban arziqi da Allah yamaka Shehummu (QS) yana cewa:
Inason ganin masu tasamma Sharqa,
Zuwa Makka wallahi nazam mashuqa,
Kamar inbi hanya muzo duk haqiqa,
Akul n***a masu zuwa ca haqiqa
Dada inyi begen Ziyara tasa.
Lallai kasani ba'a saduwa da soyayya da yardar Allah sai an kakka6e zuciya daga sha'a'wowi, da dukkanin abinda ba ubangiji ba, ma'ana dole in za'aje wurin Allah a fita daga Ni'nanci shine dukkanin dabi'un Dan'adamtaka da duk wata sifa wadda zata hana mutum kar6a kiran'Allah (na haqiqa),da saduwa da hasken dakinsa mai'tsalki. Idan akasamu "Lura" saita haifar da "Bege" mai girma cikin zuciya akan amsa kiran'Allah, dakuma kusanci da hasken dakinsa mai'tsalki, sabida farin'cikin haduwa da masoyi, dakuma kwasar kyauta ta masoya, wadda masoyi yakewa masoyinsa inya kawomasa ziyara, kamar yadda Shehummu yake fada:
Kutashi mu shirya dason Rabbana,
Akul nin nufaci gabas inyi murna
Kamar na nusaci wurai-rai nasa.
Wannan Begen shi yake sabbabama masoyi dalilan haduwa da masoyinsa, tunanin son haduwa da masoyinsa shizai sabbaba masa yin "Niyya" wadda itace kakka6ema Zuciyar'sa daga soyayyar Danginsa da Garin'sa da mazumuntansa domin Dangi, gari, da wasu mazumunta wanda masoyinsa ya tanadar masa, kaga dole ne ya katse dukkanin hijabai(abinda zai hanashi cimma burinsa) ta hanyar qoqarin maida al'huqqan mutane wadanda suke a hannunsa, dakuma neman tuba ga Allah akan kura-kuransa dakuma yin Guzuri wanda shine farantattar zuciya mai cike da soyayya wadda tazo domin ganawa da masoyi, inko ba wannan guzurin ba to zai zama(shi mahajjaci) tamkar matafiyi da yayi guzurin danyen abinci wanda ya lalacemishi a lattonda yake tsananin jin yunwa.
Akan hanyarka(Al'haki ne akanka) Yawaita tunawa da masoyi da irin kyakkyawan tarbo da lale-marhaban wanda yashirya domin tarbonka a dakinsa mai'tsalki, inko hakane, yazama wajibi gareka kashagaltu da Godiya da yawaita ambaton masoyi domin cimma burinka na kwalli dashi, kuma wajibine kaza6i "Tufafi" mafi kyau wato sune lizimtar qanqan dakai da kaiwa matuqar-qurewa wurin sa6ama al'ada ta biyewa kyale-kyalen duniya da Taqama, domin duk wanda ya maida Alfahari da son Toton'duniya abin sha'awarasa tou, tamkar yayi hannun rigane da saduwa da masoyinsa, kaga kenan dolene kakomkomtama rayuwarka kyautata fuskantar Allah (SWT) domin kasancewarka cikin wadanda yakira s**a kar6a kiransa sannan suke kwadayin debe kewa dashi.
Wurin Ihiraminka kasani cewa yanzu kam ka kar6a kiran masoyinka don haka, kajaddadama kanka cewa saura kadan kasadu da masoyinka don haka kaqara shagaltuwa da yawan ambato, tunawa dakuma godemishi, kamar yadda Shehummu yake fada:
Dayin Istigfari ga mai gafara,
Kaza rabbi shi'at abin dogara,
Kabar bin wani nai kasamu Ka tsira,
Shiyoba bushara da baiwa tasa.
Idan kashiga garin Makka yanada muhimmanci kasani cewa kana cikin alherin masoyinka, don haka kaqara zage damtse wurin Godiya, tunawa dakuma neman kusanci da masoyi. sannan kashiga cikin nutsuwa ta hanyar qoqarin cusama Zuciyar'ka girman masoyinka, haqiqa ganin masoyi a wannan mahangar shizai saka karibatu da kwalli da hasken wannan dakin da aka gayyaceka acikinsa. Kewayar da zakayiwa dankin'Allah itace sallarka domin haka kakaame ga barin yin magana da motsi mara kan gado da qoqarin shagaltuwa da yawan ambato da tunawa da masoyinka kamar yadda bayinsa Mala'iku sukeyi acikin baitul'maamuri...
Tafiyarka tsakanin Safa da Marwa Shine kai-komo cikin ladabi da soyayyar masoyi dakuma kyakkyawan fata akan kar6ar ibada daga gareka. A tsayuwarka wurin Arfa katuna da tsayuwarka aranar gobe gaban masoyinka domin amsa tambayoyi, hakanan kayi mu'amala da dukkanin Musulmi cikin soyayya da jinqayi, sabida niyyarku daya, Ubangijin'ku daya, al'qiblarku daya, tufafinku iri daya, kayimusu uzuri inda kuka sa6a a fahimta, kuma ku hadu dasu akan abinda ya hadaku(KALIMAS SHAHADAH).
Idan yazamana Zuciyar'ka ta cika da hasken masoyinka sabida fita daga Ni'nanci toh Shedan zai maida himma yaga ya lalata kyakkyawar mu'amalarda take tsakaninka da masoyinka, kamar yadda Babban malami Sheikh Nasiru Kabara yake cewa:
"Musan Shedan yana nan yayi bukka
Cikin hadaratu don gaba da Allah".
Domin haka wajibine gareka kanemi tsari daga sharrinsa. Sannan kayi niyya da yankan dabbarka akan sabunta kusanci ga Ubangijin'ka domin hakan yana qara bayyana irin cikakken miqa-wuya da yardar dakayima masoyinka.
ZIYARAR GARIN SHUGABA(SAW)....
Anan yakamata ka qara godema Allah akan wannan Babbar ni'ima domin bayin'Allah waliyyai dayawa sunso susami irin wannan alziqi Allah bai qaddara ba, kamar yadda Shehummu Uthmanu Dan'fodiyo (QS) yake cewa:
قد كدت شوقا أن أطير لقبر** ما لي سرور دون زورة سيدي
أوطار قلبي أن أزور دياره * دمعي يفيض لفقد هذا المرشظ
Sannan kashiga cikin ladabi, farin'ciki da nutsuwa domin kana gaban wanda masoyi mai tsananin tausayinka,. sannan kayi masa sallama cikin girmamawa dashida sahibansa, Yar'sa da sauran al'ummar'sa ta baqi'a.
وقل السلام عليك يا خيرالورى * والصاحبين لقدأتيت مريدا
sannan kawuce dausayin al'jannah kazauna cikin shagaltuwa da bege da tuntunin cikin girma da matsayin masoyinka.....
وفي روضة عند ذاك المقام* وكن شاكرا حيث ثم المرام
Kayi farin'ciki da murna domin indai Hajjinka irin wannan ne tou, lallai zaka koma tamkar sabon jinjirin da aka haifa, Shehummu Uthmanu Dan'fodiyo (QS) yana cewa:
Zumaina Musulmi ku zauna kuji,
Inayin kirari gamai Agaji,
Yabonai garan bakujin na gaji,
Munanan da burin zuwa Makka HAJJI,
Muzo har Madina ZIYARA tasa.
Idon yayi sa'a shizo ko da kau,
zuwa Makka ko Daiba rai shiy qalau,
Ga dadi walau Qudsu inzan darau,
Akul ma shi samu ina dammaha kau,
Ana kaishi haqqan garai don nasa.
Ga dadi ga wasu irin haihuwar can,
Wadansu qafafunsu sun kaisu har can,
Wadansu ga burinsu kullum suzo can,
Cikin zuciyata inason zuwa can,
Garai ingano kou Madina tasa.
Muradi cikin ranga nau sabitina,
Ga latton Ina falke ko nayi kwana,
Nufata ganin Ahama shi'at bukina,
Dada nayi roqo ga Allahu Raina,
Akaishi shizo can ziyara tasa.
ALLAH YAQARA HASKAKA ZUKATANMU DA HASKEN SANINSA.
ALLAH YAQARA SANAR DAMU ILIMINDA BAMUDA MASANIYA AKANSA ALFARMAR SHEHUMMU UTHMANU DAN'FODIYO (QS)