Al-Muhajirina Wal-Ansar Da'awa Sokoti

Al-Muhajirina Wal-Ansar Da'awa Sokoti Da'awa

18/09/2026

DON ALLAH MINENE AMFANIN IRIN WANNAN TSUFAN???

Muna ganin wani malami yana cewa: wai yanzu sun girma, abubuwan da s**a rika yi lokacin da suke matasa idan s**a sake yin su yanzu sun koma baya, kuma ba su ragawa tsufansu ba.
To amma abin al'ajabi da takaici, a daidai wannan lokacin sai gashi an ganshi a gidan ɗan siyasa (a gidan Abdul'aziz Yari DG Campaign na tinubu) yana yi masa addu'ar samun nasara!
Yana tsoron magana a kan aƙidojin Sunnah ko karanta ingantattun Hadisan Annabi (S.A.W) saboda kada 'yan bidi'a su zage shi ko su soke shi. Amma bai ji tsoron komawa gidan 'yan siyasa da tsufansa yana yi musu raraka ba!

Menene amfanin a ce ba a zage ka ba wajen kare Sunnah da karanta Hadisin Manzon Allah (S.A.W), amma kuma ka yarda a zage ka, a soke ka, a kuma watsa maka mutunci a idon duniya saboda an ganka a gidan 'yan siyasa kana neman abin duniya da tsufanka?

Tsufa cike da girmamawa shi ne ka tsaya a kan gaskiya da karanta littattafai har karshen rayuwarka.

Shi kuwa wanda ya guje wa zagin saboda addini amma ya karɓi zagin saboda siyasa, ya rasa kwarjinin ilimi da cikar mutunci!

11/09/2026

Address

Sokoto
DA'AWA

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al-Muhajirina Wal-Ansar Da'awa Sokoti posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Al-Muhajirina Wal-Ansar Da'awa Sokoti:

Shortcuts

Share