Muhammad Shugaba College of Qur'anic Sciences, Sokoto, Nigeria

Muhammad Shugaba College of Qur'anic Sciences, Sokoto, Nigeria Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Muhammad Shugaba College of Qur'anic Sciences, Sokoto, Nigeria, Education, Gidan Fulani Area Sokoto, Sokoto.

Makarantar MUH'D SHUGABA makarantace da aka assasa a shekarar 2022 wacce a halin yanzu take da sassa uku da ake karatu a ciki
1- Sashen JEKA-KA-DAWO (DAY)
2- Sashen KWANA (BOARDING)
3- Sashen ONLINE

za ku iya tuntubarmu a wannan lamba+2347063504549

21/09/2026
Makarantar mu mai albarka
14/09/2026

Makarantar mu mai albarka

14/09/2026
MAKARANTAR Muhammad Shugaba College of Qur'anic Sciences, Sokoto, Nigeria ZA TA SAKE ƊAUKA ƊALIBAN QIRA'AT (SASHEN ONLIN...
26/04/2026

MAKARANTAR Muhammad Shugaba College of Qur'anic Sciences, Sokoto, Nigeria ZA TA SAKE ƊAUKA ƊALIBAN QIRA'AT (SASHEN ONLINE)

A duba sauran bayanai a Comment Section 👇👇👇

YAU MUN SAMU ZIYARA TA MUSAMMAN A MAKARANTARMU Yau lahadi 28-07-1447H (18-01-2026) Alh Faruku Attahiru M.D/CEO Annur Mul...
18/01/2026

YAU MUN SAMU ZIYARA TA MUSAMMAN A MAKARANTARMU

Yau lahadi 28-07-1447H (18-01-2026) Alh Faruku Attahiru M.D/CEO Annur Multi-media Ltd kuma Chairman Sokoto Professional Printers ya kawo ziyara a makarantar mu ta Muhammad Shugaba a mazauninta da ke Unguwar Nakasari a nan birnin Sokoto

Ya zo ya ga makaranta kuma ya ga ɗalibai ya saurari karatun wsu daga cikinsu kuma yi musu jawabi tare bada kyauta ta musamman domin a siya wa dalibai minti

A lokacin da yake jawabi Alh. Annur ya shawarci hukumar makaranta da ta dubi yiyuwar fito da wasu hanyoyi da zaa kiyar da daliban wannan makaranta musamman masu Boarding Sana'o'i daban-daban domin su samu wasu karin hanyoyin dogara da kansu bayan sun gama karatu Haka kuma ya bada tabbacin cewa zai bada iya kokarinsa domin tabbatar da hakan

A namu ɓangare shuwagabannin makaranta mun karbi wannan shawara tare da sanar da shi yunkurin da muka fara yi na koyar da wadannan yara sanaoi

Haƙiƙa mun yi farinciki da wannan ziyara Muna addu'a Allah ya saka mishi da alkhairi ya albarkaci kasuwancinsa

✍🏻 Habibu Shugaba
Shugaban makarantar Muhammad Shugaba College of Qur'anic Sciences, Sokoto, Nigeria

SASHEN ONLINE NA MAKARANTAR MUHAMMAD SHUGABA YA BADA IJAZA GA ƊALIBAI KARO NA BIYU                     Watan December 20...
30/12/2025

SASHEN ONLINE NA MAKARANTAR MUHAMMAD SHUGABA YA BADA IJAZA GA ƊALIBAI KARO NA BIYU
Watan December 2025

A wannan wata na December da muke ciki ne makarantar Muhammad Shugaba College of Qur'anic Sciences, Sokoto, Nigeria ta ba wa dalibanta da ke karatu Kaitsaye da masu karatu Online Ijazah bayan kammala karatunsu da riwayoyi daban-daban

Wannan shine karo na biyu tun bayan buda wannan Makaranta a shekarar 2022

Idan ba'a manta ba a watan December na shekarar 2024 lokacin da ake musabaqar National a jihar Kebbi ne muka fara bada Ijazah ga daliban da s**a kammala karatunsu da riwayoyi daban-daban a wannan Makaranta daga 2022 zuwa 2024

Sai kuma a wannan shekarar ta 2025 muka sake gabatar da Ijazah karo na biyu ga daliban wannan makaranta da s**a kammala karatun Qira'at dinsu daga January 2025 zuwa December 2025

Mun kaddamar da fara rabon Ijazah din ne a Garin Maiduguri inda aka yi musabaqar National karo na 40

Babanmu kuma malaminmu Sheikh Dr Muhammad Sani Abdullahi Jos ne ya kaddamar da bada wadannan IJAZAT

Lokaci ya yi da za'a sake daukar sabbin dalibai da za su yi karatu a shekarar 2026 In Sha Allah

A duba karin bayani a comment section 👇👇👇

✍🏻 Habibu Shugaba
Shugaban Makarantar Muhammad Shugaba, Sokoto

.             MUN CANJA SUNAN MAKARANTA                   السلام عليكم ورحمة الله وبركاته Muna sanar da ɗaukacin al'umma...
02/09/2025

. MUN CANJA SUNAN MAKARANTA
السلام عليكم ورحمة الله وبركاته

Muna sanar da ɗaukacin al'umma cewa mun canja sunan makarantar mu
daga
Ibn Aljazari College of Qur'anic Sciences

Zuwa
Muhammad Shugaba College of Qur'anic Sciences

Wannan ya faru ne sakamakon wasu dalilai da kuma shawarwari

Saboda haka daga farkon wannan wata na September 2025 sunan wannan makaranta tamu ya canja zuwan *MUHAMMAD SHUGABA COLLEGE OF QUR'ANIC SCIENCES*

Dukkanin sassan wannan makaranta guda uku
1- Sashen Boarding
2- Sashen Jeka-ka-dawo
3- Sashen Online
za su ci gaba da amsa wannan sabon suna

Muna addu'a Allah ya sa wannan canji ya zamo alkhairi ga wannan makaranta, malamanta, ɗalibanta da ma sauran al'ummar musulmi

Mun gode da irin goyon baya da kuma shawarwari da hadinkai da kuke bamu wurin tafiyar da wannan makaranta

✍️ Habibu Shugaba (Shugaban Makarantar Muh'd Shugaba)
Tuesday
09-03-1447
02-09-2025

Address

Gidan Fulani Area Sokoto
Sokoto

Telephone

+2348034468543

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muhammad Shugaba College of Qur'anic Sciences, Sokoto, Nigeria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Muhammad Shugaba College of Qur'anic Sciences, Sokoto, Nigeria:

Shortcuts

Share

Category