Arewa student's orientation forum Asof Gwale chapter

Arewa student's orientation forum Asof Gwale chapter I create this page for awaness of a student

AMFANI ILIMI AIKI DASHI

16/07/2026

AN MAGANCE MATSALAR NETWORK ƊIN JAMB!

Hukumar JAMB Ta Kawo Ƙarshen Matsalolin Da Ake Fuskanta Na Network A CAPS, Da Sauran Ayyukanta.

Daga Yanzu: Zaku Iya Ziyartar Kowacce CBT Centre Mafi Kusa Da Ku, Domin Sauya Courses Ko Makarantu; Uploading Ɗin O'Level Results; Cire Original JAMB Results; Duba Admission Status - Da Makamantansu, Ba Tare Da Fuskantar Wata Tangarɗa Ba.

✍️ Miftahu Ahmad Panda

WhatsApp - 08121124840.

Kar rashin aiki a ƙasar nan ya sa ka daina neman ilimi.Kar girman kwalinka ya sa ka raina ƙaramin sana'a.Kar kuma rashin...
16/07/2026

Kar rashin aiki a ƙasar nan ya sa ka daina neman ilimi.
Kar girman kwalinka ya sa ka raina ƙaramin sana'a.
Kar kuma rashin hanya ya sa ka daina neman aiki.
Ci gaba da ƙoƙari, domin nasara tana zuwa ga masu juriya, dagewa da addu'a.

~Comr. Murtala Kabir Bichi

16/07/2026
15/07/2026

DAMAR GABATAR DA AYYUKANKU NA CAC POST-INCORPORATION!

A Pandancy Global Technologies Ltd, Muna Gabatar Da Kowanne Irin Aikin CAC Na Post-Incorporation, Wanda Ya Haɗarda Gyare-Gyare Da Aikace-Aikacen Da Ake Yi Bayan Rijistar:

• Muna Biyan Kuɗin Jaddada Rijistar Sana'o'i, Kamfanoni, Ƙungiyoyi da Foundations Na Shekara Shekara (Annual Return)

• Muna Sauya Sunan Business, Kamfani, Ƙungiya ko Foundations

• Muna Sauya Daraktan Kamfani, Share-Holder, Business Proprietor, Association Trustee ko Gyara Bayanansu (Idan An Samu Kuskure A Yayin Shigarwa)

• Muna Fito Da Takardun Rijistar CAC Da S**a Yi Ɓatan Dabo

• Muna Ƙara Share-Capital, ko Rage Share-Capital Ɗin Kamfani

IDAN KUNA BUKATAR KOWANNE DAGA CIKIN AYYUKANMU:

Ku Tuntuɓemu Ta Manhajar WhatsApp: 08121124840.

Ko Ku Ziyarci Ofishinmu, Da Ke: C011, Digital Hub Plaza, Sharada Phase III, Kano.

15/07/2026

AN FARA CONVERTING ƊIN JAMB ZUWA DIRECT ENTRY (DE)

Converting ɗin JAMB UTME zuwa Direct Entry (DE), dama ce da hukumar JAMB take bayarwa ga ɗaliban da s**a rubuta jarrabawar JAMB UTME, kuma suke da mallakin sakamakon kammala karatun Diploma (ND), NCE, IJMB, JUPEB, HND ko Degree a gefe guda, ta sauya tsarin neman Admission ɗinsu zuwa Direct Entry (DE) da ake farawa daga Aji 2 (Level 200), saɓanin gurbin karatun masu JAMB UTME da ake farawa daga Ajin Farko na Jami'a (Level 100).

Hakan na faruwa ne, sakamakon rashin samun nasarar ire-iren waɗannan ɗalibai a jarrabawar JAMB UTME ɗin da s**a rubuta, ko kuma ɗaukar JAMB ɗin kawai a matsayin hanya ta samun "JAMB Number" (ga ɗaliban da s**a yi karatu lokacin da babu JAMB Admission).

• A INA AKE CONVERTING ƊIN JAMB UTME ZUWA DE ?

Ana converting ɗin JAMB UTME zuwa Direct Entry ne a JAMB State Offices, ko Zonal Offices Kaɗai.

• SU WAYE S**A CANCANCI CONVERTING ƊIN JAMB ƊINSU ZUWA DE A 2026 ?

Ba kamar yadda abin yake kasancewa a shekarun baya ba, a wannan shekara ta 2026 hukumar JAMB ta iyakance ɗaliban da s**a kammala karatun Diploma, NCE ko Degree a shekarar 2026 kaɗai a matsayin waɗanda zasu ci gajiyar tsarin conversion (ma'ana banda waɗanda s**a kammala karatu a shekarun 2025, 2024, 2023, 2022, 2021, 2020, 2019 da makamantansu).

• MENENE MAFITA GA ƊALIBAN DA S**A KAMMALA KARATU A SHEKARUN BAYA ?

Kasancewar an rufe rijistar Direct Entry (DE), ga kuma JAMB ta ɓullo da wannan sabon tsari, toh babu wata mafita da ta wuce jinkirtawa zuwa shekarar 2027 domin rijistar JAMB UTME kawai.

Sai Dai, Ɗaliban Da S**a Fara Karatunsu Na Higher Institutions A Shekarun 2020, 2019, 2018 Da Shekarun Bayansu, Sunada Damar Yin JAMB Regularization (As Undisclosed Admissions).

KU AIKA MANA TAMBAYOYINKU A MANHAJAR WHATSAPP - 08121124840.

RUBUTAWA: Miftahu Ahmad Panda

WhatsApp - 08121124840

Address

Gwarzo Road
Sabon Gari

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa student's orientation forum Asof Gwale chapter posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Arewa student's orientation forum Asof Gwale chapter:

Shortcuts

Share