Sheikh Sa'idu Ahmad Na'ibi Ringim

Sheikh Sa'idu Ahmad Na'ibi Ringim Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sheikh Sa'idu Ahmad Na'ibi Ringim, Tutor/Teacher, Nasarawa, Ringim.

Wannan shafi shi kaɗai ne ingantaccen shafin Sheikh Sa'idu Ahmad Na'ibi Ringim wanda bisa amincewarsa ɗansa Muhammad Sani Sa'idu yake gudanar da al'amuran sa a wannan shafi.

16/05/2026

Allah Ya karɓi ibadu,

Alhamdulillah. Insha Allah sati mai zuwa za'ayi Saukar Tafsir Ƙurɗubi a Zawiyyar Sheikh Sa'idu Ahmad Na'ibi dake Nasaraw...
06/12/2025

Alhamdulillah. Insha Allah sati mai zuwa za'ayi Saukar Tafsir Ƙurɗubi a Zawiyyar Sheikh Sa'idu Ahmad Na'ibi dake Nasarawa Ringim. Kuma Malam ya sanar da sanya Sabon Tafsir wato Tafsir Ɗabari.
Allah Ya sakawa Malam da Jannatul Firdaus da sauran Malaman mu, Amin.

Alhamdulillah. Insha Allah sati mai zuwa Sheikh Sa'id Ahmad (Na'ibi) zai fara karatun wannan Littafin. Asabar da Lahadi ...
01/06/2025

Alhamdulillah. Insha Allah sati mai zuwa Sheikh Sa'id Ahmad (Na'ibi) zai fara karatun wannan Littafin. Asabar da Lahadi a Babban Masallacin Juma'ah na Ringim 4-5pm . Allah Ya sakawa Malaman mu da alkhairi,

06/04/2024

JAWABI DAGA MALAMAI

Assalamu alaikum. Insha Allah Gobe Lahadi Sheikh Sa'id Ahmad Na'ibi zai gabatar da Muhadara mai taken "Mafi Kyawun Guzuri Tsoron Allah" a Jigawa State College of Education and Legal Studies Ringim da ƙarfe goma zuwa sha biyu na safe. Allah Ya yi mana jagoranci, Amin.

06/03/2024

Assalamu alaikum. Insha Allah Ranar Juma'a Sheikh Sa'idu Ahmad (Na'ibi) Zai fara gabatar da Tafsir na bana 1445/2024 a Babban Masallacin Jama'a na Ringim. Na Katutu kuma ranar Azumin farko.
Allah Ya yi mana jagoranci Ya azurta mu da Iklasi,

Muhammad Sani Sa'idu

16/04/2023

Assalamu alaikum. Insha Allah ranar Talata Malam Sa'idu Ahmad Na'ibi zai rufe Tafsirin da yake gabatarwa a Babban Masallacin Juma'a na Ringim daga ƙarfe 9:00 pm zuwa abin da ya sauwaƙa.
Allah Ya yiwa Malam jagora, Allah Ya sanya mu cikin ƴantattu a wannan wata mai albarka,

Muhammad Sani Sa'idu
25 Ramadan, 1444 A.H
16/4/2023 A.D

26/03/2023

Assalamu alaikum. Za'a iya sauraron Tafsirin Sheikh Sa'idu Ahmad Na'ibi kullum ƙarfe 9:00pm a gidan Rediyon FM Andaza 93.5 wadda Hon Shehu Sule Udi (Chairman Ringim Local Government) ya ɗauki nauyi.
Allah Ya saka da alheri, Allah Ya yi mana jagora,

19/03/2023

TAFSIR 1444 A.H
1. Tafsirin dare bayan Sallar Isha a Babban Masallacin Jama'a na Ringim za'a farashi Insha Allah gobe Litinin.
2. Tafsirin safe a ƙofar gidan Marigayi Malam Babba a Unguwar Katutu Ringim, za'a farashi ranar da aka fara Azumi Insha Allah.
3. Tafsirin Yamma wanda Malam Bashir yake gabatarwa a Masallacin ƙofar gidan Malam za'a farashi ranar da aka fara Azumi Insha Allah.
Allah Ya yi mana jagora, Allah kuma ya ƙarawa Malam lafiya da Imani da Iklasi, Amin.

06/01/2023

GAYYATAR WALIMA

DARUL-HADIS WAT-TAFSIR RINGIM. Wannan cibiya tana farin cikin gayyatar ku zuwa walimar saukar da akayi ta littafin 'Aunul Ma'abud Sharhu Sunan Abu Dawud' wadda Sheikh Sa'idu Ahmad Na'ibi ya karantar. Insha Allah za'a a gudanar da ita a Babban Masallacin Juma'a na Ringim, ranar Lahadi 15 Jumada-thani, 1444 A.H / 8 January, 2023 A.D da ƙarfe 4:30pm . Allah Ya bada ikon halarta, Allah Ya sakawa Malam da alkhairi,

Alhamdulillah. A yau Lahadi 8/6/1444 dai dai da 1/1/2023 Malamimu Sheikh Sa'idu Ahmad Na'ibi Ringim ya yi saukar Littafi...
01/01/2023

Alhamdulillah. A yau Lahadi 8/6/1444 dai dai da 1/1/2023 Malamimu Sheikh Sa'idu Ahmad Na'ibi Ringim ya yi saukar Littafin 'Aunul Ma'abud Sharhu Sunan Abu Dawud' Wanda Sheikh Abi-Dayyib Shamsul-Haƙ Al-Azimil Abady mutumin India ya rubuta Malam ya shafe shekaru 9 yana karantar da wannan Littafi wato tun daga December, 2013 zuwa January, 2023. Kafin wannan Littafi Malam ya karantar da 1.Sahihul Bukhari har sau biyu 2. Sahihu Musulmi tare da Sharhin Imam Nawawi 3. Tuhfatul Ahwazi Sharhu Jami'ut Tirmizi wanda Sheikh Abu Ali Abdul Rahman Bin Abdurrahim Al-Mubarakafori ya rubuta 4. Aunal Ma'abud Sharhu Sunan Abu Dawud wanda aka sauke yau.
Malam ya so a saka Sunan Nasa'i tare da Sharhin Imam Siyuɗi haka bai yiwu ba, amma cikin ikon Allah Sati mai zuwa Insha Allah za'a fara Littafin 'Al-I'ilam bi sunnatishi Alaihissalam Sharhu Sunan Ibn Majah wanda Sheikh Ala-uddin ya rubuta Malamin ƙarni na takwas amma kafin ya kammala Allah Ya yi masa rasuwa (Rahimahullah).
Malam yana gudanar da wannan karatu duk sati a Ranar Asabar da Lahadi ƙarfe 4:00 - 5:00 na yamma a Babban Masallacin Juma'a na Ringim. Allah Ya sakawa Malam da alkhairi ya jiƙan iyayensa da maƙaunatan su, Allah Ya ƙara masa Ikilasi da mu gaba ɗaya, Amin.

20/09/2022

DARASIN RAYUWA !
Ya kai Bawan Allah ! Ka guji yin zalunci da alfahari sabo da wata ni'ima da Allah ya yi maka, kafin ka anyi waɗan da s**a fika samun ni'imar duniya amma saboda zalunci da alfahari Allah ya halakar dasu ya ƙwace ni'imar tasu ya bawa wasu.
Ka duba Suratul Ƙasas aya ta 76-86 kaga bayanin da Allah maɗaukakin sarki ya yi dangane da Ƙaruna na zamanin Annabi Musa (A.S).
Allah Ya fahimtar da mu,

Address

Nasarawa
Ringim

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sheikh Sa'idu Ahmad Na'ibi Ringim posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Sheikh Sa'idu Ahmad Na'ibi Ringim:

Shortcuts

Share

Category