03/05/2021
FALALAR SALLAR WALAHA
DAGA
MUHAMMAD SANI SA’IDU
[email protected]
Saƙo kawai: 09031705769
1 RAJAB, 1442 A.H/ 13 FEBRUARY, 2021 A.D
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu, tsira da aminci su tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad da iyalan sa da shabban sa da waɗanda s**a biyo bayan su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Ya ƴan’uwa musulmai ! Sallar walaha tana da falalar gaske kuma lokacin da ake yinta shi ne lokacin da rana ta fara zafi, ya danganta da irin yanayin da aka wayi gari da shi. Amma za'a iya ɗauka kamar ƙarfe goma shine abin da yafi domin rana ta take da zafii a wannnan lokacin. Amman idan mutum yana da uzuri. Zai iya yinta ƙasa da ƙarfe goma, saboda a riski falalar da ake nema domin gudun wofantar da ita ga sashen masu sakko su bar gida. Sannan Annabi (S.A.W) ya ambaceta da sallar masu neman tuba inda yace: “Sallar masu neman tuba lokacin da ɗan dalo yake ƙonewa”. Muslim ne ya rawaito.
Daga Aisha (R.A) ta ce: “Manzon Allah (S.A.W) yana sallatar walaha raka’a huɗu kuma yana daɗa abin da Allah ya so”. Muslim ne ya rawaito.
Daga Abi Zar (R.A) Daga Annabi (S.A.W) Ya ce: “Yana wayar gari akan kowacce gaɓa ta ɗayanku ladan sadaka, kowanne tasbihi sadaka ne, kowacce Alhamdullah sadaka ce, kowacce Hailala sadaka ce, kowacce Kabbara sadaka ce, umarni da kyakkyawa sadaka ne, hani da aikata mummuna sadaka ne, yana isuwa daga wancan Raka'a guda biyu da zai yisu na walaha”. Muslim ne ya raiwato.
Daga Abi Huraira (R.A) ya ce: “Maƙaunaci na (S.A.W) ya yimin wasiyya da Azumin kwana uku a kowanne wata, da raka’oin walaha, da yin wutiri kafin na kwanta”. Bukhari da Muslim.
A ƙarshe, ina roƙon Allah (S.W.T) ya sanya wannan aiki ya zamanto tsarkakakke, kuma ya sanya shi ya kasance mai sauƙi ta yadda musulmai da yawa za su amfana da shi, Amin. Sannan ina roƙon duk wanda ya amfana da wannan fa’ida da ya yi min addu’a ta alheri da iyayena da malamaina da maƙaunatan mu.