13/02/2026
Zaman lafiya mai ɗorewa na buƙatar haɗin kan kowa-Ministan Tsaro CG Musa
Babban Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya bayyana cewa ana iya cimma zaman lafiya mai ɗorewa ne kawai idan aka haɗa ƙoƙarin tsaro da bunƙasa tattalin arziƙi, daidaiton zamantakewa, da ci gaban ɗan Adam.
Ya ce yaƙi da matsalar tsaro da ƙauracewar jama’a daga gidajensu ba aikin gwamnati kaɗai ba ne, ya na buƙatar haɗin gwiwar duka sassan gwamnati, al’umma da kuma kamfanoni masu zaman kansu.
Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin wani taron kan ilimi da zaman lafiya da aka gudanar a birnin Legas.
A cewarsa, farfaɗo da rayuwar jama’a, gina al’ummomi, da ƙarfafa zaman lafiya a yankunan da rikici ya shafa dole ne su kasance tare da ayyukan tsaro. Ya kuma jaddada buƙatar ƙarfafa haɗin kai tsakanin gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu, kungiyoyin ci gaba da na farar hula.
Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya ta ƙuduri aniyar magance waɗannan ƙalubale ta hanyar sabbin dabaru masu haɗa kai da ɗorewa, domin kare jama’a, tabbatar da tsaro, da gina ƙasa mai wadata ga kowa.