24/07/2025
To kenan kowa gabansa zai k**a kenan, har kowa ya cimma burin sa?
Ko kuwa kai kakeso a sanya gaba maimakon sa?
Kowanne daga ciki shashanci ne babba.
Tilas koda ba addinance zamu bi ba, sai mun sami jagora b***e kuma babu abin da zamuyi ba tare da kallon addinin mu ba.
Idan akwai gyara (cikin salon jagorancin kwankwasiyya), shin ka taba baiwa jagoran yaki karba?
Kada fa ta bayyana kaima kokarin gina kanka ya dau salon wawaye na sai sun rusa wani.
Wanne jagora talaka yake dashi kaf arewa tamkar RMK?
Wanene keda tsarin da ya taimaki dukkannin al'uma k**ar nasa?
Kaf arewacin kasarnan bayan Kwankwasiyya, wanne tsari ne tabbatacce cikin ikon Allah tsawon shekaru?
Kenan duk karyace, amma kullum Allah ke bata kariya da tagomashi har yau?
Kada ka baiwa masu kyamar abin da kake samun hujjojin kafawa kanka bayan sun gama gano ka da inda ka dosa.
Shawara ce!!!
Allah ya kara taimakon duk wani tsari dake nufin samarwa da al'uma saukin rayuwa kasata musamman talaka.
A yau, matsalar ‘yan Kwankwasiyya ba wai rashin yawan su ba ne — a’a, sai dai rashin tsayayyen shugabanci da fahimtar gaskiyar akidar. Sun mallaki dimbin matasa masu kuzari, amma an tsare su a cikin siyasar bauta: bauta ga mutum guda, ba ga manufa ba.
Kwankwasiyya ta fara ne da alƙawarin gyara rayuwar talaka, amma yau akasari ta zama tamkar ƙungiyar murna da yaɗa gumurzu, ba gina tsammani ba. Idan kana da tunani daban, kai abokin gaba ne. Idan kana tambaya, kai mai cin amanar tafiya ne.
Ana bukatar ‘yan Kwankwasiyya su farka daga mafarkin mutum ɗaya, su dawo yiwa al-umma mafarkin. Siyasa ba ta mutum ɗaya bace — siyasa ce ta gyara asibitoci, ta dawo da ilimi, ta kawo karshen yunwa da daukaka martabar ‘yan ƙasa.
Idan ‘yan Kwankwasiyya za su farka, su fahimci cewa tsarin da suke ciki yana hana su girma, to za su san cewa a yau ba wai zaman ‘yanci suke ba — suna zaman hana kansu ci gaba ne.
Dan Bello yace:
“Idan juyin juya hali ya tsaya a kan mutum guda, to bariki ne, ba sauyi ba.”