Shuwari Primary School Old Boys Association -Spsoba

Shuwari Primary School Old Boys Association -Spsoba An Association for all students who attended shuwari primary school graduants from the day of its establishment up to date.������

26/04/2026
26/04/2026

Allah yasa mudace duniya da lahira yadoramu akan azzalumai nagida dana waje.

26/04/2026

TURƘASHI: Budurwa ta kai ƙarar tsohon Saurayinta Brekete Family bayan ya yaudare ta ya karɓi bashin Miliyan 6 a wajenta zai kammala ginin da za su zauna amma daga baya ya Auri wata daban

Wata matashiya ta bayyana yadda tsohon saurayinta ya yaudare ta ta ranta mashi kuɗi har Naira miliyan 6.6 bayan ya yi mata alkawarin aure.

Matashiyar ta kai ƙorafi a gidan rediyon Brekete Family, inda ta bayyana cewa sun daɗe suna soyayya, kuma saurayin nata yana tabbatar mata da cewa zai aure ta.

A cewarta, saurayin ya rinƙa lallashinta har ta karɓo kuɗi Naira miliyan 4.6 daga wajen mahaifinta ta bashi da nufin zai kammala ginin gidan da za su zauna bayan aure. Sai dai daga baya, mutumin ya auri wata mace daban.

Duk da aurensa da wata, a cewar matashiyar tsohon Saurayin nata ya sake dawowa ya yi mata ɗaɗin baki ta sake ranta masa Naira miliyan 2, wanda ya kai jimillar kuɗin zuwa Naira miliyan 6.6.

Ta ce duk ƙoƙarin da take yi na neman ya biya ta kuɗinta abu ya ci tura, domin mutumin ya ƙi biya tare da katse hulɗa da ita gaba ɗaya.

A ƙarshe, matashiyar ta bayyana cewa dole ta sayar da filinta domin ta biya bashin da ta karɓo daga mahaifinta.

Me zaku ce akai? Ya kuka kalli labarin?

25/04/2026

**Da DUMI-DUMI**
Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce shugaban Amurka Donald Trump ba shi da wani hujja da zai hana Iran haƙƙinta na nukiliya, yayin da Washington da Tehran ke ci gaba da rashin jituwa kan batun nukiliya.
Wannan na zuwa ne a matsayin martani bayan shugaba Trump yace Iran zata bayarda dukkan uranium data tace zuwa AMURKA

25/04/2026

DA DUMI-DUMI: Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi wa Netanyahu kakkausar s**a.

Kana yin abin da kake so domin kasashen yamma suna kare ka kuma suna goyon bayan ka. Kada ka yi mana magana game da kare hakkin dan adam. Ba ka damu da mutane ba matuƙar su Musulmai ne kuma Larabawa.

Kana magana ne kawai game da dokokin duniya idan ya dace da muradunka, amma abin da ke faruwa a Iran da Lebanon ba ya damunka, kuma ba ka ambace shi ba.

Shin mashigar Hormuz ta fi muhimmanci fiye da yaran Iran 170 da s**a rasa rayukansu saboda Trump da Netanyahu? Shin akwai wanda zai yi ƙarfin halin gurfanar da su a gaban ku?

Ba ka girmama dokoki, amma kana tsoron masu iko kuma kana la'akari da su. Iko shine harshen Iran na yanzu, don haka nan ba da jimawa ba za ka biya kuɗin duk wannan a hannun Iraniyawa.

Kuma ina gaya wa duniya baki ɗaya: idan kana son zaman lafiya na gaske, dole ne ka kawar da Netanyahu da jiharsa.

Ku Shigo Jaridar ATV Hausa Domin Samun Sahihan Labarai.

25/04/2026

Ko ka tsani Real Madrid, dole ka amince da girman su a gasar Zakarun Turai (Champions League). Ko tsohon dan wasan Barcelona da Arsenal, Thierry Henry, ya kasa boye al'ajabinsa akan yadda Madrid take canzawa idan dare yayi a Turai!

Ga abinda yake cewa: 👇

"Zanyi magana ne tsakanina da Allah, kuma kamar yadda kuka sani, ni masoyin Barca ne na gaske. Amma dole mu jinjinawa Real Madrid. Babu wanda ya yi tunanin hakan zai faru (kwallon Manchester City), kuma babu wanda ya taba tunanin Fede Valverde zai ci ƙwallaye uku (hat-trick).
Ina son yin magana ne akan kokarin dukkan yan wasan kungiyar. Kowa yana taya kowa fada a fili. Gaskiya ban san me suke shafawa a jikin rigar su ba. Watakila idan na saka rigar Real Madrid gashin kaina zai dawo, saboda akwai wani abu na musamman da suke sawa a jikin rigar.
Idan suna wasan Champions League, ban san me suke shafawa ba... yan wasan su daban suke komawa. Dole mu basu girman su. A cikin dukkan kungiyoyin da s**a kai zagaye na 16, ban yi tsammanin ganin irin wannan bajinta daga Real Madrid ba. Kuma ko da hakan yana min zafi, dole ince: An kyauta, kun nuna bajinta." Duk an cire su a gasar yanxu Amma sunyi kokari sosai

Yaya kuke ganin wannan 'Aura' ta Real Madrid a gasar zakarun Turai? Har ma tsoffin makiyan su sun fara amincewa da sarautar su!

Kamar yadda aka sani: REAL MADRID TA KASANCE, TANA NAN, KUMA ZATA CIGABA DA ZAMA SARKIN TURAI!! 🏆🔥

25/04/2026
24/04/2026

Tsohon tauraron Faransa, Paul Pogba, ya fito fili ya yaba wa abokin ƙasarsa Kylian Mbappé, yana mai cewa duk batun kyautar Ballon d'Or lokaci ne kawai—domin a ganinsa, Mbappé ya riga ya zama mafi kyawun ɗan wasa a wannan kakar.

Pogba ya ce: “Gare ni, Mbappé shi ne mafi kyawun ɗan wasa a kakar bana.”
Wannan magana tasa na nuna cikakken goyon baya ga tauraron da ke ci gaba da haskawa a duniya.

Ya kuma nuna mamaki da irin yadda Mbappé ya fara rayuwarsa a sabuwar kakar, inda ya zarce adadin kwallayen da manyan ‘yan wasa irin su Cristiano Ronaldo da Ronaldo Nazário s**a ci a farkon kakarsu.

A cewarsa: “Ya zura fiye da kwallaye na Cristiano da R9 a kakarsa ta farko… zai ci gaba da hawa sama, ban yi mamaki ba.”

Wannan kalamai na Pogba na nuna cewa Mbappé na kan hanyar zama ɗaya daga cikin mafiya girma a tarihin kwallon kafa.

A ƙarshe, sako ya fito fili—Mbappé bai tsaya ba… kuma duniya na iya ganin mafi girma daga gare shi nan gaba.

22/04/2026

Ronaldo Yana daf da lashe kofina guda Biyu a bana a Al Nassr.

Wafiyya Hausa

Address

No 3 Goni Yusuf Street Shuwari Via Hausari Ward Nguru LGA
Nguru

Telephone

+2347032858048

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Shuwari Primary School Old Boys Association -Spsoba posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category