07/09/2023
BUTULCIN ƊAN ADAM...
Wata rana Annabi (S.A.W) ya ƙissanta wa Sahabbansa (R.A) wannan ƙissar:
"An yi wasu mutane uku a Banu Isra'il, guda ya kasance kuturu, guda kuma mai saiƙon kai (marar gashi), guda kuma makaho. Sai Allah (S.W.T) Ya yi nufin Ya jarrabe su, sai Ya aiko wani mala'ika zuwa ga kowannensu.
Sai mala'ikan ya fara zuwa wajen kuturun ya ce da shi, "Me ka fi so?"
Kuturu ya ce, "Ina so fatar jikina ta zama kyakkyawa, kuma wannan cutar kuturtar ta rabu da ni, mutane su daina gudu na kuma su daina ƙyamar zama da ni!"
Sai mala'ikan ya sanya hannunsa a jikin kuturun ya shafi jikinsa. Nan take sai ya warke, fatarsa ta zama mai kyau mai sheƙi.
Daga nan sai mala'ikan ya ce da shi, "Wacce irin dukiya ka ke so?"
Sai ya ce, "Raƙumma!"
Sai mala'ikan ya kawo masa wata taguwa mai ciki ya ba shi, ya ce da shi, "Ga ta nan, Allah Ya sanya maka albarka a cikinta!".
Daga nan sai mala'ikan ya je wajen mai saiƙon kai, ya ce da shi, "Me ka fi so?"
Mai saiƙo ya ce, "Ina so gashin kaina ya fito, domin mutane su daina yi min dariya suna min ba'a duk inda na nufa!"
Sai Mala'ikan ya shafi kansa, sai kyakkyawar suma ta fito masa, gwanin ban sha'awa.
Sai mala'ikan ya ce da shi, "Wacce irin dukiya ka ke so?"
Sai ya ce, "Shanu!"
Sai mala'ikan ya ba shi wata saniya mai ciki ya ce da shi, "Ga ta nan, Allah Ya sanya maka albarka a cikinta!".
Sai mala'ikan ya je wajen makaho, ya ce da shi, "Me ka fi so?"
Makaho ya ce, "Idanuwana su dawo don in rinƙa ganin komai!"
Sai Mala'ikan ya shafi idanuwansa, sai ganinsa ya dawo k**ar bai taɓa yin makanta ba. Sai mala'ikan ya ce da shi, "Wacce irin dukiya ka ke so?"
Sai ya ce, "Awaki!"
Sai mala'ikan ya kawo akuya mai ciki ya ba shi, ya ce da shi, "Ga ta nan, Allah Ya sanya maka albarka a cikinta!", sai ya tafi.
Ai kuwa sai Allah Ya albarkaci dabbobin nan nasu, kafin wani lokaci duk yankin ya cika da raƙuma da shanu da awaki na waɗannan mutane uku.
Bayan haka wata rana sai Mala'ikan nan ya zo a cikin sifar wani mutum mabuƙaci. Sai ya tafi wajen kuturun nan wanda a baya ya warkar da shi da izinin Allah, ya ce da shi, "Ya kai wannan attajiri, ka sani cewa ni dai talaka ne matafiyi, dukkan guzurina ya ƙare a hanya kuma dabbar hawana ta mutu. Yanzu ba ni da komai kuma ba ni da wata mafita sai Allah sai kai. Ka dubi girman Allah wanda Ya ba ka wannan kyakkyawar halitta da wannan tarin dukiyar, Ka ba ni raƙumi ɗaya wanda zan hau in ƙarasa garinmu!"
Jin haka sai mutumin nan ya ɗaure fuska, ya dube shi ya ce, "Tafi ka ba ni wuri! Ni nan ina da muhimman abubuwan da zan yi da wannan dukiyar, ba ni da wani abu da zan iya cirewa in ba ka daga ciki!"
Sai mala'ikan (a sifar mabuƙaci) ya ce, "K**ar ko na gane ka! Shin ba kai bane wannan wanda a baya ka kasance kuturu daga baya Allah Ya warkar da kai? Ba kai bane ka kasance matsiyaci wanda kowa yake gudunka, daga baya Allah Ya azurta ka?"
Mutumin nan ya ce, "Me kake cewa? Lallai ba ka da hankali. Ni wannan dukiyar duk da ka gani na gaje ta ne a wajen iyayena!"
Sai mala'ikan ya ce, "To, in ƙarya kake, Allah Ya mayar da kai yadda ka ke da farko!"
Sai ya tafi wajen wannan mutumin mai saiƙon kai, shi ma ya nemi taimako daga wajensa, shi ma k**ar yadda s**a yi da na farkon nan haka ta kasance, ya hana shi. Sai shi ma ya ce da shi, "Allah Ya mayar da kai irin yadda ka kasance a baya!"
A ƙarshe sai ya tafi wajen makahon nan. Ya ce da shi, Ya kai wannan attajiri, ka sani cewa ni dai talaka ne matafiyi, dukkan guzurina ya ƙare a hanya kuma dabbar hawana ta mutu. Yanzu ba ni da komai kuma ba ni da wata mafita sai Allah sai kai. Ka dubi girman Allah wanda Ya warkar da kai daga makanta, Ka ba ni akuya ɗaya wadda zan sayar in samu guzurin da zai ishe ni zuwa garinmu!"
Jin haka sai mutumin nan ya ce, "Babu shakka, ni a baya na kasance makaho, sai Allah cikin RahamarSa da kyautarSa Ya dawo min da ganina. Kuma na kasance matalauci, sai Ya azurta ni daga falalarSa. Yanzu ga shi bawanSa ya zo wajena da buƙata, ba zai yiwu a gareni in hana bawanSa abin da yake buƙata ba matuƙar na mallaki wannan abu! Ya kai wannan bawan Allah, ga dukiyata nan, ka ɗebi iya abin da ka ke so ka bar abin da ba ka so, ina rantsuwa da Allah ba zan taɓa dakatar da kai ba!"
Sai mala'ikan Ya ce, "Ka bar dukiyarka, ni ne mala'ikan nan wanda ya zo maka a baya, na zo ne don in jarraba ka, yanzu kam ka cinye jarrabawar!"
Daga nan sai Allah Ya bar wannan mutum da dabbobinsa, su kuma waɗancan biyun sai Allah Ya karɓe dukiyarSa, kuma Ya mayar da su k**ar yadda suke a baya."