Muazu bin jabal I p s hotoro

Muazu bin jabal I p s hotoro Makaranta muazu bin jabal i.p.s hotoro .primary islmiyya tahfiz dare& asuba wadannan sashi suna karatu domin inganta rayuwar yayanku

29/06/2023

Wannàn makaranta zatayi sauka ranar asabar 8/7/2023 muna gayyatar yan uwa musulmi

01/05/2023
27/08/2022
18/08/2022

GA AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYIN KAMAR HAKA
1. Akwai wasu Manyan Annabawa guda uku (3) wadanda Kansu bai ta'ba yin furfura ba.
(Sunayensu yazo acikin Suratu Maryam A.S ) Suwaye wadannan??
ANSWER:
Wadannan Annabawan sune
1) ANNABI HARUNA
2) ANNABI ISMA'I'll
3) ANNABI IDRIS
2. Akwai wasu Annabawa guda Uku (3)
wadanda basu taba yin Aure ba har s**a koma ga Allah (Su ma sunayensu yazo ajere acikin Suratul An-aam). Meye sunansu?
ANSWER:
Wadannan Annabawan sune:
1) ANNABI YAHAYA
2) ANNABI ISAH
3) ANNABI ILIYAS
3. Akwai wasu Annabawa guda biyu, (2)
Sarakuna ne kuma Manzanni ne. Daya daga cikinsu shiya haifi dayan. Meye sunansu?
ANSWER:
Wadannan Annabawan sune:
1) ANNABI DAUDA wanda shi ya haifi
2) ANNABI SULEIMAN
4. Akwai wasu Annabawa Mursalai guda (2) Wa da Qani ne. Shi Qanin an bashi Littafi da Mu'ujizozi. shi kuma yayan an bashi Fasahar harshe. Meye sunansu?
ANSWER:
Wadannan Annabawan sune:
1) ANNABI MUSA (shine karami ) Allah ya bashi littafi mai suna "ATTAURA" kuma ya bashi mu'ojuzoji misali sarrafa "SANDA" Sai kuma
2) ANNABI HARUNA (Shine yayan) Allah ya bashi FASAHAR HARSHE
5. Akwai wani Annabi Mursali (Ba Annabi Adamu bane) amma duk wanda ka gani abayan Qasa, to Jikansa ne. Wani Annabine?
ANSWER:
Wannan Annabi Shine:
Adamu na biyu wato ANNABI NUHU A.S
6. Annabi Ya'aqubu yana da wani suna wanda Allah ya ambaceshi dashi acikin Alqur'ani. Kuma har yanzu ana kiran Zuriyarsa da wannan Sunan.. Shin wanne suna ne wannan?
ANSWER:
An kira su da "ALI YAKUBU" a suratul Maryam, amma kuma an bashi sunan "ISRA'I'll" zuri'ar sa kuma BANU ISRA'ILA
7. Akwai wata halitta wacce Allah yai mata Wahayi. ita ba Mutum bace, ba Aljan bace, kuma ba Mala'ika bace. Shin wacce Halitta ce wannan?
ANSWER:
Wadannan Halittu sune:
1) TURURUWA da kuma
2) QUDAN ZUMA
Allhamdullahi Mungode
Allah yakara mana fahimtar Alqur,ani alfarman Wanda yazo dashi wato ANNABI S.A.W

Katura Zuwa Group 3 Kachal Domin Al'umma Su Amfana ❤️

Address

Hotoro Bye Pass Nass Kano
Nasarawa
226

Telephone

+2348076203727

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muazu bin jabal I p s hotoro posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category