28/07/2025
SAHABBAIN SHEHU TIJJANI A TAIKACE.
TARIHIN MAULANA SHEIKH ABU-HAMID MUHAMMAD AL-ARABI AL-SA'IH.
Maulana Sheikh Abū-Hāmid Muhammad al-‘Arabī al-Sā’ih, wani shahararren waliyi ne kuma malami na darikar Tijjaniyya, wanda aka haifa a garin Meknes, ta kasar Maroko, a yanzu a cikin shekarar 1814 Miladiyya (1229 Hijiriyya). Ya fito daga zuriyar Sayyidina Umar al-Faruq ne. Ya taso cikin zuriyar malamai, inda ya haddace Alkur’ani tun yana yaro kuma ya zurfafa a fannonin ilimin Hadisi, Fikihu (Malikiyya), da kuma Sufanci (Tasawwuf).
Malamansa da Darikar Tijjaniyya
Ya yi karatu a wajen fitattun malamai irin su Sidi Abdulkadiri al-Kawhan da Sheikh al-Sharif Walid al-Iraqi, kuma ya karɓi izinin ɗariƙar Tijjaniyya daga wajen shahararrun waliyyai da s**a haɗu da Shehu Tijjani ko almajiransa kai tsaye, ciki har da Halifa Sheikh Aliyu Tamasin.
Ayyukansa da Gudummawar sa
Sheikh al-‘Arabī ya yi fice wajen rubuce-rubuce, inda rubutunsa da ya fi shahara shi ne littafin Bughyat al-Mustafid, sharhi ne na waƙar sufaye “Munyat al-Murīd”. Wannan littafi ya zama ɗaya daga cikin muhimman tushe na darikar Tijjaniyya. Ya bayyana muhimman matsayi na ruhaniya kamar muƙamin Khātam al-Wilāyah al-Muhammadiyyah wanda ya kawo tabbacin muƙamin na Maulanmu Sheikh Ahmad Tijjani shi ne cikamakin waliyyan wannan al’umma.
Ya kuma kafa Zawiyya a Rabat, babban birnin Maroko, wacce har yanzu tana ci gaba da kasancewa cibiyar ilimi da tarbiyya.
Ya rasu a Rabat a shekara ta 1892 (1309 Hijiriyya).
Basaraken gibrima saraky Gombe