20/09/2026
20 ga Satumba, 2026
Mai Girma,
Manomi Mohammed Umaru Bago
Gwamnan Jihar Neja
Gidan Gwamnati
Minna, Jihar Neja
Mai Girma Gwamna,
WASIƘAR TA’AZIYYA KAN MUMMUNAN RASUWAR MASU HAKAR MA’ADINAI TA GARGAJIYA 37 A MINNA
A madadin shugabanni da ɗaukacin ’ya’yan ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), reshen Jihar Neja, muna miƙa saƙon alhini da ta’aziyyarmu ga Mai Girma Gwamna, Gwamnati da al’ummar Jihar Neja, musamman iyalan masu hakar ma’adanai ta gargajiya guda 37 waɗanda s**a rasa rayukansu cikin mummunan yanayi yayin da suke tsare a hannun Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) a Minna.
Wannan lamari mai matuƙar tayar da hankali ya jefa jiharmu cikin baƙin ciki, tare da haifar da jimami da damuwa ga iyalan mamatan da sauran al’umma. Rasuwar matasa masu yawa a irin wannan yanayi mai cike da ayar tambaya babban abin takaici ne da ya shafi duk wani mai kishin ɗan Adam, ba tare da la’akari da bambancin addini, siyasa ko ƙabila ba.
Muna yaba wa Mai Girma Gwamna bisa matakan gaggawa da ya ɗauka, ciki har da ayyana zaman makoki na kwanaki uku da kuma haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya da hukumomin da abin ya shafa domin gano haƙiƙanin abin da ya haddasa wannan rasuwa. Muna roƙon a gudanar da cikakken bincike na gaskiya, mai adalci da ’yanci, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da hannu—ko ta hanyar ganganci, sakaci ko gazawar sauke nauyin da ke kansa—ya fuskanci hukuncin da doka ta tanada.
Duk da cewa gwamnati da hukumomin tsaro suna da halastaccen nauyin tabbatar da bin doka da kuma yaƙi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, duk mutumin da aka k**a ko aka tsare yana da cikakken haƙƙin a mutunta mutuncinsa, a kula da lafiyarsa kuma a kare rayuwarsa. Dole ne a ko da yaushe a gudanar da aikin tabbatar da doka cikin adalci, bin ƙa’idojin shari’a da kuma girmama haƙƙin ɗan Adam.
JIBWIS tana kira ga matasanmu masu alhini da daukacin mazauna Minna da su ci gaba da kasancewa cikin natsuwa, su guji tashin hankali da lalata dukiyoyin gwamnati ko na jama’a. Ƙarin asarar rayuka ko dukiyoyi zai ƙara tsananta baƙin cikin da al’umma ke ciki ne kawai. Muna kira ga kowa da kowa da ya bai wa binciken da doka ta tanada damar gudana, tare da ci gaba da neman adalci ta hanyoyin lumana da s**a dace.
Haka kuma, muna roƙon Mai Girma Gwamna da ya tabbatar da cewa iyalan mamatan sun samu tallafin da ya dace. Muna kuma bayar da shawarar a ci gaba da tattaunawa da shugabannin al’umma, ƙungiyoyin addini, wakilan matasa da sauran masu ruwa da tsaki domin dawo da amincewar jama’a, tabbatar da sulhu da kuma hana sake aukuwar tarzoma.
Malamai da ’ya’yan ƙungiyarmu a faɗin Jihar Neja za su ci gaba da yin addu’a ga mamatan, iyalansu da kuma zaman lafiyar jiharmu. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa mamatan, Ya yi musu rahama, Ya ta’azantar da iyalansu, Ya kuma ba su juriyar jure wannan babban rashi.
Allah Ya kare Jihar Neja, Ya shiryar da shugabanninta, Ya tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummarmu, Ya kuma kiyaye mu daga sake aukuwar irin wannan mummunan lamari.
Mai Girma Gwamna, muna sake miƙa ta’aziyyarmu da addu’o’inmu, tare da tabbatar maka da matuƙar girmamawarmu.
Naku cikin aminci,
Mallam Hassan Nuhu
Shugaba
Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS)
Reshen Jihar Neja