Adamu Abdullahi

Adamu Abdullahi ╭╭═══════╬�╬═════════╮╮
If Knowledge is too Expensive, Try Ignorance DAN MAGANCE MATSALOLIN WAYOYIN HANNU DA COMPUTER KO BADA SHAWARA

http://aaadam36a.faa.im

10/04/2025

Ina buƙatar akoyamin yadda ake amfani da facebook, domin na jima bana hulɗa dashi sosai.

Jiya ba Yauba, Wasu anan Basa raye, Allah ya gafartawa dukkan Musulmi
10/04/2025

Jiya ba Yauba, Wasu anan Basa raye, Allah ya gafartawa dukkan Musulmi

Wannan Video zai nuna mana yadda zaka gyara kuskuren rubutun da kayi ko canza kalma, misali kayi rubutu shafi biyar sann...
15/08/2021

Wannan Video zai nuna mana yadda zaka gyara kuskuren rubutun da kayi ko canza kalma, misali kayi rubutu shafi biyar sannan akwai kalmar daka ke son canzawa, amma kuma tayi yawa acikin rubutun ka, to a wannan Video zaka ga yadda zaka canza alokaci ɗaya.

Wanda idan ka canza wannan kalma aduk inda take cikin rubutunka zata canza nan take.

Wannan Video zai nuna mana yadda zaka gyara kuskuren rubutun da kayi ko canza kalma, misali kayi rubutu shafi biyar sannan akwai kalmar daka ke son canzawa, ...

05/04/2017

WAYAR KA KIRAR ANDOID TANA ZAFI?

Mafi yawan masu waya kirar android suna kukan wayoyinsu suna zafi, kuma sun kasa Gane me ya Ke kawo wannan matsala, awannan rubutun zanyi bayani akan abubuwan da suke sa wayar zafi da kuma yadda zaka magance.

MEYASA ANDROID TAKE ZAFI
Akwai dalilai masu yawa da suke sa wayar android zafi.
1. WACCE CHAGER KAKE AMFANI?
Ya kamata ka rika lura da yanayin chajin da kake mata, wacce irin chaja kake amfani da ita wajen chaja wayar taka, Meye karfin batir din wayarka, shin chajar da kake amfani da ita zata iya chaja batir dinka, Meye adadin wutar da chajar take bayarwa takai dai-dai da taka, karka yi la'akari da girman jikinta, kawai ka duba nawa taka take bayarwa "Output".

Yayinda kayi amfani da karamar chaja wacce take fitar da wuta kadan sai kaga wayarka tayi saurin cika, amma cikin kankanin lokaci chajin naka zai kare, ko kuma kaji tayi zafi, ko kuma idan ka kashe wayar kaga chajin ya sauka dayawa, saika tabbatar da chajar da kake chaja wayarka tana bada wutar da batir dinka zai iya cajuwa ayadda yake bukata.

2. MUHALLIN CHAJI

Alokacin da kake kokarin yin chajin wayar ka matukar kasan tana zafi ko bata yi, to yayinda kake chajinta karka ajiyeta akan abubuwa kamar
i. Soson katifa, duk abinda yake dauke da soson katifa, karka dora wayarka akai, koda ajiyeta zakayi to ka ajiye wayarka a kan teburi ko kasa, saboda katifa tana rike iska, ta fitar da zafi, wannan yana karar da chajin waya ko yasa waya zafi sosai.
ii. Kayan wuta, karka ajiye wayarka akan abinda yake shima ajikin wuta yake, kuma yana zafi, kamar sitafileza, System Unit wanda aka fi sani da CPU, Yar yawo (Station wire) ko kan keyboard kodai wani abu da yake daukan zafi yayinda yake aiki, amma idan baya hade da wuta Alokacin saika ajiye akansa.

3. YANAYIN LOKACI DA MU'AMALA

Aduk lokacin da kake yunkurin sa waya chaji, karka dora ta achaji ahalin ta dau zafi, koda ta cika, minti kadan chajin zai kare, saika barta ta dan yi sanyi, Idan kuma kasan wayarka tana zafi to karka matsa amfani da ita yayinda rana tayi zafi, saboda zafin yana hawa (Temperature), musamman masu wayar Samsung, HTC, LG da sauran masu irin wannan dabi'a, yayin da baka kiyaye wannan matakin, waya tana daukan wata dabi'a, wato saita fara kashe kanta tana kunnuwa, da kanta, kuma batir dinka zai rika daukewa daga 30% ko 40%, Idan baka chanja wannan dabi'arba sai kuma kaga idan ta mutu sai takai ga amfara dora batir a Universal CHAGER/ Direct charger sannan zai tashi. Sai alura da yadda ake chaja waya, Yayinda kasa wayarka a chaji kaji tayi zafi zaka iya samun tsumma mai kyau, ka jika shi da ruwa saika goge wayar dashi, ko ka dora wayar acikinsa zata dawo dai-dai, amma tsumman ba ruwa ake sawa ya jike sosai ba ko fesa shi kayi shi kenan. Rashin kula da wannan matakin yana haifar da matsala ga waya.
i. Lalacewar batir ko ya kumbura
ii. Mutuwar waya na har abada
iii. Ta rika daukewa tana kunnuwa da kanta.
iv. Tabuwar power IC.
v. Sa waya ta fara zabar chaja
vi. Waya ta fara zabar batir wanda zai kunnata/Raina batir
vii. Saurin karewar chaji.
viii. Saukar chaji da 10-10%

Abin lura ga Power Bank
Masu chaji da power bank ku daina amfani da waya ahalin kun jona mata power bank, domin yana sa waya zafi, yana kashe batir yin hakan shima yana haifar da matsalolin da muka lissafo a Yanayin chaji da lokaci wato a na uku.

Masu manyan wayoyi ku rika mallakar powerbank wanda yake da girman wuta, karka sayi mai karamin Capacity, sannan ka nemi cable mai kyau, mai bada wuta, amfani da karamin Power bank akan babbar waya yana haifar da matsaloli kamar haka:-
i. Lalacewar batir ko ya kumbura
ii. Rashin saurin cika waya
iii. Ta rika daukewa tana kunnuwa da kanta.
iv. Tabuwar power IC.
v. Sa waya ta fara zabar chaja
vi. Waya ta fara zabar batir wanda zai kunnata/Raina batir
vii. Saurin karewar chaji.
viii. Saukar chaji da 10-10%

mu lura da wadannan baya nan. Kuma wasummu suna fama da wannan matsalar saika lura ka gyara zaka ga chanji insha Allah.

03/03/2017

GAYYATA GAMI DA ADDU'A

Ina GAYYATAR yan uwa zuwa wajen DAURIN aure na.

Adamu Abdullahi Idris
Da
Hauwa'u Yuseef Muhammad

Wanda za'ayi kamar haka;
RANA: Lahadi 5/3/2017
LOKACI: 10:00am
W/HADUWA: Gidan Malam Rabilu Mai Katako, No 15 Dan rimi B2, Rijiyar Lemo.

W/D/AURE: Gidan Alhaji Yuseef Muhammad, No 860 Layin jirgi, Opp. Makarantar Malam Usman, Gwammaja.

Allah ya bada ikon zuwa, ga wanda bai samu dama ba, yayi addu'a. Nagode.

Adamu Abdullahi Jagoran Duniyar Waya, Dan autan Duniyar Computer

22/05/2015

INA HACKERS DIN SUKE NE?

Adukkan abinda mutum ya koya na ilimi to tabbas akwai ranar da zaiyi wa addininsa ko akidarsa aiki dashi, akwai abubuwan da suke da muhimmanci ace duk kungiya akwai koda mutum daya ne mai wannan ilimi, saboda akwai ranar da wannan ilimi zaiyi amfani.

Ayau Hackers na Nigeria da sauran Hackers. Masu kishin addinin Islam, to tabbas yanzu wani nauyi ya doru akanku na ganin cewar kun kawar da duk wani website, ko account na social network, da suke amfani dashi wajen cin mutuncin Allah da Annabinsa, wajibi ne kuyi wannan aikin matukar kuna da sanin a wannan bangaren na hacking.

Wallahi wajibi ne kuyi amfani da wannan damar taku kuyi jihadi a shafukan sada zumunta, kuga kun kawar da duk. Wanda zai taba martabar addinimmu.

Wallahi duk wanda yake da sani akan yadda zaiyi Hacking, kuma yake ganin irin wadannan post. Din amma. Baiyi magana ba, kuma bai dauki matakin kawar da. Post. Dinba to tabbas imaninka yayi rauni.

Karka dauka idan ka rufe account na irin wadannan mutanan ka rika ganin kayi zalinci, babu wani zalinci da kayi,kai wallahi ko kansa. Ka sare, kayi jihadi, Allah zai baka lada, wallahi karka manta,manzon Allah matsayinsa awurin Allah, shi ne shugaban Manzonni.

Yanzu da za'a ce wani zai zagi shugaban kasar Nigeria mai jiran gado. Ko mai ci yanzu, wallahi, wallahi, wallahi, da yanzu hackers. Dimmu sunyi abinda ya kamata na. Abiyasu.

Hackers kunyi amfani da damarku lokacinzabe kunyi Hacked na INEC website, kunyi amfani da damarku kunyi. Hacked na BUK website bara, kunyi ne dan duniya ba dan ci gaba ba.

To ga aikin dole, wallahi, wallahi, wallahi duk wanda. Yake da yadda zaiyi ya kulle account na wani a internet amma. Bai kulle na masu akidar Haqiqa ba to tabbas bashi da imani, imaninsa yayirauni sosai.

Bama bukatar tura report zuwa ga mamallakan website, domin bazasu rufe alokacin daya dace ba, kawai arika Hack din duk wanda aka samu da cin mutuncin addinin Allah.

Muna godiya ga wadanda s**a kulle account na Adamu Haqiqa, muna son duk wanda akaga account dinsa da sunan Haqiqah ko koyana post din cin mutunciko baiyi ba agoge shi daga internet ko web ne dashi.

Ko sunansayana da kalmar Haqiqa ko babu matukar yana post na cin mutuncin addininmu akawar da shafinsa.

Allah ya taimakemu, Allah ya bada nasara, su kuma masu irin wadannan post, Allah ya shiryar dasu su dawo muslunci, muna maraba da shugowarsu muslunci matukar sunyi yunkurin shigarsa, idan kuma su suna. Ganin su musulmi ne, to. Allah kai ka fimu saninsu Allah ka. Shiryamana su, Allah ka basu ikon ganin gaskiya su bita.

Muna yi musu haka ne badan bama sonsu ba, wallahi muna sonsu, kullum burimmu shi ne, MUGUDU TARE MU SHIGA ALJANNA TARE, Allah ka karkato mana kansu su dawo dai-dai.

Allah wannan akida da s**a fahimta Allah ka basu ikon gane cewar Sheikh Inyass shima bawa ne, Allah ka basu ikon gane karyar da suke karantawa da tumasancin da suke fahimta. Dan matsayin annabi awurin Allah.

Dan Allah ayi Share na wannan post yana da muhimmanci,

20/11/2013

AMFANI DA GOOGLE SEARCH ENGINE:
http://duniyarcomputer.com

AMFANI DA LOKACI
Idan mutum zai binciki wani abu a internet kuma wannan abun ya kunshi lokaci, to, zaka iya yin amfani da abinda ake kira Date Range shi kuwa Date Range ana saka shine a wajen binciken abubuwan da aka san lokacin faruwarsu da kuma ana kokwanton daga lokaci kaza zuwa lokaci kaza ne abu kaza ya faru. Ko da yake shi amfani da wannan hanyar binciken tana da sharudda wanda sai an kiyaye su kafin a samu amsar da ake nema.
Misali wanda yake son yayi binciken abinda ya shafi wani littafi wanda bashi da hakikanin lokacin da aka wallafa wannan littafi amma kuma yasan bai wuce daga shekarar 2000 ba zuwa 2003. To, da farko dole ya rubuta sunan littafin sannan ya rubuta shekarar da yake tunanin itace aka wallafa shi, sannan ya rubuta karshen shekara. Harry Potter daterange:2004-01-13..2006-01-13

19/11/2013

AMFANI DA LAMBOBI A GOOGLE SEARCH ENGINE:
http://duniyarcomputer.com

Mutum na iya binciken abu a google ta hanyar amfani da lambobi wajen bincikensa.

A misalin mutum yana neman wani abu wanda kudinshi bai wuce kaza ba to zai iya amfani da wannan tsari wajen yin binciken.

Phone $40..$90 idan ka rubuta haka to google zai fito maka da wayoyin hannu wanda kudinsu bai gaza dala arba’in ba kuma basu wuce dala casa’in ba.

12/11/2013

VERSION NA ANDROID

Wannan shine jerin version na androd, wadanda ake iya amfani da su, da wadanda za'ayi amfani da su, sannan da wannan version zaka gane girman wayarka, da saurinta, da yadda zata tafiyar da ayyukanta.

Version na android wadanda basa BBM CHAT, saboda haka idan wayarka tana daga cikin masu wannan version to bata BBM CHAT/BLACKBERRY CHAT.

Domin gane version na wayarka, saika latsa Menu > Setting > About Phone. Zaka gani a wurin

:) . Cupcake (1.5),
:( . Donut (1.6),
:O . Eclair (2.0―˛―2.1),
;) . Froyo (2.2―˛―2.2.3),
:P . Gingerbread (2.3―˛―2.3.7),
8) . Honeycomb (3.0―˛―3.2.6),

Wadannan sune wayoyin kirar android da suke da version na android, saboda haka idan taka takai version 4.0 zata yi.

Domin gane version na wayarka, saika latsa Menu > Setting > About Phone. Zaka gani a wurin

•̃͡-̮•̃͡). Ice Cream Sandwich (4.0―˛―4.0.4),
•̃͡-̮•̃͡). Jelly Bean (4.1―˛―4.3),
•̃͡-̮•̃͡). KitKat (4.4)

Ko wanne version da yadda ya fara da kuma yadda ya kare.

08/11/2013

SANARWA!! SANARWA!!!

Agobe Asabar ne 09/11/2013 ''Sheikh Muhammad Bin Uthman Kano''

Zai gabatar da lecture a masallacin Khairul-Bariyyah, dake Sabon titin Dan rimi {Titin 'Yan babura} dake Rijiyar lemo, karamar hukumar Fagge, Kano state.

Lokaci Magrib zuwa Isha'

Allah ya bada ikon zuwa ameen

Address

Yankatako Kofar Ruwa Katsina Road Kano
Mariri
700007

Telephone

+2348188764577

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Adamu Abdullahi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Adamu Abdullahi:

Shortcuts

Share

Category