30/11/2024
FALALAR AUREN BUDURWA !
Manzon ALLAH (saw) Yace':
"Ku auri budurwaye, don sun fi dadin baki (wajen magana mai kyau ko sumbata), kuma sun fi jefo ƴaƴa (yawan haifuwa), kuma sun fi yarda da abu kadan (imma a saduwa ko a abin Duniya)".
Saheehul Jamee'ee 2939
Daga jabir (RA) Yace': Na auri wata mace sai Manzon ALLAH (saw) yace dani, shin kayi aure? Sai nace eh..... Budurwa ko bazawara? Sai nace': Bazawara. Sai yace dani shin meyasa Baka auri budurwa ba, kayi mata wasa itama tayi maka wasa.
Muslim
Manzon ALLAH (saw) Yace'; Kada a ɗaura auren bazawara har sai an nemi yardar ta, kuma kada a aurar da budurwa har sai an nemi izinin ta, sai aka tambayi Manzon ALLAH (saw) menene izinin na ta yace. Izinin ta in tayi shiru. Muslim
Daga Anas (RA) Yace': Yana daga cikin Sunnah, idan namiji ya auri budurwa ya kwana a dakin ta kwana bakwai sa'annan ya raba musu kwanaki, in kuwa ya auri bazawara zai kwana a dakin ta kwana uku, sa'annan ya raba musu kwanaki. Bukhari da Muslim
Ummus salma (RA) tace': A lokacin da manzon ALLAH (saw) ya aure ta ya kwana adakin ta kwana uku.
A budurwan manzo (saw) yayi maka zaɓi, ya zaɓar maka mai addini.
Kuma Babu wanda zai zaɓi mace maabociyar addini face wanda daman zuciyar sa, yana rataye da addini.
Manzon ALLAH (SAW) Yace';
ana auren mace domin abu huɗu:- dukiyar ta, dangin ta, kyawun ta, da kuma addinin ta ka zaɓi maabociyar addini, hannun ka zayyi albarka.
Saheehut targeeb 1920
Manzon ALLAH (SAW) Yace'; Duniya kayan jindaɗi, amma mafi alkhairi kayan jindaɗin duniya, mace ta gari.
Saheehut targeeb 1912