12/03/2019
( ) : KARATUN HADISI DA AIKI DASHI SHINE ZAMA LAFIYA GA MUSULMI :
__________________________________________
: SADAKA TANA KAREKA DAGA ZAFIN WUTA:
yazo cikin bukhariy da Muslim daga adiyyi dan hatim yace:
Annabi (SAW) ya ambaci wuta saiya nemi tsari daga gareta saiya kawar da kansa cikin fushi sa'annan yasake ambaton wuta yakuma nemi tsarinta yakuma kawar da kansa cikin fushi sa'annan yace:
" KUJI TSORON WUTA KODA DA TSAGIN DABINO, IDAN BAKA SAMUBA TO DA KYAKKYAWAR KALMA".
(Bukhariy : 6023, Muslim :1016).
yazo cikin bukhariy da Muslim daga adiyyi dan hatim yace manzon ALLAAH (SAW) :
" BABU WANI DAGA CIKINKU FACE SAI UBANGIJINSA YAYI MAGANA DASHI BABU MAI TAFINTA TSAKANINSA DA TSAKANINSA, SAIYA DUBI DAMARS BAZAI GA KOMAI BA SAI ABINDA YAGABATAR DAGA AIKIN, YAKUMA DUBA HAGUNSA BAZAI GA KOMAI BA SAI ABINDA YAGABATAR, YAKUMA DUBA GABANSA BAZAI GA KOMAI BA SAI WUTA A SAITIN FUSKARSA, SABIDA HAKA KUJI TSORON WUTA KODA DA TSAGUN DABINO ".
(Bukhariy : 7512, Muslim :1016).
: Ahmad ya ruwaito kuma Albany ya ingantashi daga hakeem dan hizam lallai wani mutum ya tambayi manzon ALLAAH (SAW) akan SADAKA wanne yafi saiyace :
"A BAIWA MA'ABOCIN ZUMUNCI MAKIYI"
(Ahmad :14896, Albany : saheeh aljami'u: 1110).
: SADAKA WA DABBOBI:
_____________________________________
yazo cikin bukhariy da Muslim daga abiy huraira (R. A) lallai annabi (SAW) yace:
" YAYINDA WANI MUTUM YANA KAN HANYA KISHIR RUWA YAYI MASA TSANANI SAIYA SAMI RIJIYA SAIYA SAUKA CIKINTA YASHA RUWA SAIYA FITA SAI GA WANI KARE YANA LALLAGI YANA CIN KASA SABIDA KISHIR RUWA
SAI MUTUMIN YACE:
HAKIKA KISHIR RUWA YAKAI GA WANNAN KAREN IRIN HALIN NIMA NA FADA, S SAUKA CIKIN RIJIYAR YACIKA HUFFINSA (TAKALMI 'YAR CIKI) DA RUWA SAIYA SHAYAR DA KAREN, SAI ALLAAH YAGODE MASA YAKUMA GAFARTA MASA "
sai sukace ya ma'aikin ALLAAH :
Yanzu Muma muna lads game da dabbobinmu?
Saiyace:
" CIKIN DUK WANI MA'ABOCIN HANTA DANYE AKWAI LADA".
Bukhariy :2466, Muslim :2244).
a wata ruwaya ta bukhariy daga abiy huraira lallai annabi (SAW) yace:
" SAI ALLAAH YAYI MASA GODIYA SAIYA SHIGAR DASHI ALJANNAH".
(bukhariy :174).
yazo cikin bukhariy da Muslim daga abiy huraira (R. A) yace:
Annabi (SAW) yace:
" YAYINDA WANI KARE YAKE TA KEWAYA WANI RIJIYA, KIRIS KISHIR RUWA YAKASHE SHI, SAI WATA KARUWA DAGA CIKIN KARUWAN BANIY ISRAEL TA GANSHI SAI TA CIRE TAKALMINTA 'YAR CIKI SAI TA SHAYAR DASHI, SAI SAI GAFA MATA TA DALILINSA".
(Bukhariy :3467, Muslim :2245).
ﻃﺮﻳﻖ ﺍﻟﺼﺎﻟﺤﻴﻦ ﺍﻟﻰ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ
Via: Abu habibillah abdallah mustapha assalafiy Biu.