GONI BUKAR ABBA AJI

GONI BUKAR ABBA AJI

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from GONI BUKAR ABBA AJI, Tutor/Teacher, pompomari sabon fege damaturu, Maiduguri.

Photos 11/08/2015

Wani lakani ne zan bayar wanda nake fatar in
samu lada mai wanda yayi aiki da shi shima ya
samu lada. Wanda kuma ya turawa dan uwansa
shima ya samu lada.
HADISI NA FARKO
Manzon Allah (S.A.W) ya na cewa Wanda ya
karanta Qulhuwallahu Ahad kafa 10x Allah ya yi
masa Alkawarin zai gina masa kata faren gida a
gidan Aljanna sai Sayidina Umar ya ce Ai to in
haka ne sai mu dinga yawai tawa sai Manzon
Allah ya ce Allah shine mai yawaitawa Allah
shine mai tsabtacewa.
HADISI NA BIYU
Manzon Allah ya na cewa duk wanda ya karanta
suratul Kahfi a ranar jumaa Allah zai cika masa
hasken sa har zuwa wata jumaa mai zuwa yana
cikin haske yana cikin farin ciki.
HADISI NA UKU
Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce duk wanda ya
haddace ayoyin goma na farkon kahfi Allah zai
kiyayeshi daga fitinar dujal.
HADISI NA HUDU
Manzon Allah yana cewa Wanda ya karanta
ayatal kursiyu bayan kowace Sallah ta farillah ba
abinda zai hana shi shiga Aljanna sai in bai mutu
ba.
HADISI NA BIYAR
Idan kazo zaka kwanta a shimfidar ka da
daddare to ka karanta kulya ayyuhal kafirun to
bazaka mutu mushriki ba a idan ka mutu a
wannan dare.
HADISI NA SHIDA
Wanda ya yi alwala, bayan ya kare alwala sai ya
ce Ash-hadu wahadahu lasharika lahu wa anna
muhammadan Abduhu wara suluhu. Allahumma
Jaalni minattauwabina wajaalni minal
mutadhahhirina.
Duk wanda ya fadi wannan bayan gama Alwalar
sa to zaa bude masa kofofin Aljanna guda
takwas ya zabi wadda ya ke son shiga.
HADISI NA BAKWAI
Wanda ya yi alwala bayan ya kammala alwalar
sa kaf, sai ya ce Subhanakallahumma
Wabihamdika ash-hadu allah Ilaha illallah anta
astagfiruka waatubu ilaika.
Zaa rubuta wannan acikin wata takarda bazaa
bude ba sai ranar lahira ya ga alkhairin da ke
cikin ta.
HADISI NA TAKWAS
Wani sahabi ya ke cewa wata rana muna tare da
manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallama sai
wani mutum daga cikin sahabbai ya ce Allahu
Akbar kabira, Walhamdulillahi kasira,
Wasubhanallahi bukratan waasila, Sai manzon
Allah ya ce wanene cikin ku ke fadar wannan
kalma sai ya ce ni ne Ya rasulullah sai manzon
Allah ya ce nayi mamakin wadan nan kalma da
ka fada, anbude rofofin sama gaba daya saboda
wannan kalma da ka fada. Sai Abdullahi Dan
Umar ya ce tun daga wannan rana kullum sai na
fadi wannan kalma, ban taba tsallake wata rana
ko wani lokaci da bana fadar wannan kalma ba.
HADISI NA TARA
Wata rana mun kasance muna Sallah a bayan
manzon Allah (S.A.W) da Annabi ya dakko daga
rukuu sai ya ce Samiallah Liman Hamidahu sai
wani mutum daga cikin sahabbai ya ce Rabbana
Walakal Hamdu, Hamdan Kasiran Mubarakan Fihi
da aka gama sai Manzon Allah ya waiwayo sai
ya ce Wanene ya fadi wannan sai mutum ya ce
Ni ne ya manzon Allah Sai manzon Allah ya ce
Naga malaika talatin da yan kai suna rigagato
wazai rubuta wannan aiki yaje ya gayawa Allah.
HADISI NA GOMA
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce Wanda
ya yi sallar nafila rakaa goma sha biyu tsakanin
dare da rana Allah zai gina masa gida a cikin
gidan Aljanna.
HADISI NA SHADAYA
Wanda ya kiyaye yanayin nafila rakaa hudu
kamin sallar azahar da kuma rakaa hudu kamin
sallar laasar to Allah zai haramta masa shiga
wuta.
HADISI NA SHA BIYU
Manzon Allah Yana cewa Allah ya jikan wanda
ya jikan wanda ya yi sallar nafila rakaa hudu
kamin laasar.
HADISI NA SHA UKU
Wanda yake karanta ayoyi goma da daddare to
bazaa rubuta shi cikin gafalallu ba wanda ya ke
karanta ayoyi dari to zaa rubuta shi cikin masu
bauta ga Allah, wanda kuma ke karanta ayoyi
dubu a cikin dare kullum to zaa rubuta shi daga
cikin masu arzikin lahira.
HADISI NA SHA HUDU
Wanda da yi Sallar nafila a cikin duhu inda
bawanda zai ganshi to Allah zai linka masa sau
ashirin da biyar na sallar da zai yi wani ya
ganshi.
HADISI NA SHA BIYAR
Annabin tsira ya ce Wanda yayi sallar walha
(Sallar hantsi/Luha) rakaa hudu kuma yayi rakaa
hudu kamin sallar laasar, Allah zai gina masa a
cikin aljanna.
HADISI NA SHA SHIDA
Hakika malaiku suna yin salati ga wadanda suke
cika sahun farko, idan s**a ga wata kafa a cikin
Sallah suna cikata basa barin ta kuma Allah zai
cika darajar sa da kimarsa da martabar sa.
HADISI NA SHA BAKWAI
Babu wani Bawa da zai yi sujada ga Allah face
Allah ya rubuta masa lada ya kankare masa
zunubi ya kuma daukaka masa daraja don haka
mu yawaita sujjada.
HADISI NA SHA TAKWAS
Wanda yayi sallar asuba a cikin jami sannan ya
zauna yana ta salati yana ta ambaton Allah bai
bari ba harsai da rana ta fito, sannan ya tashi
yayi sallar walha rakaa biyu to Manzon Allah ya
ce Kamar yayi hajji cikakkiya! Kamar yayi umura
cikakkiya! Kamar yayi umura cikakkiya! Kamar
yayi umura cikakkiya! hajji cikakke! hajji cikakke!
hajji cikakke! Haka Annabi Muhammad Sallalahu
Alaihi Wasallama ya mai maita.
HADISI NA SHA TARA
Manzon Allah ya ce wanda ya yi Sallah arbain a
cikin jami maana kwana takwas jami bai tsere
masa ba, sallolin nan biyar a jere duk da shi ake
kabarta kabbarar harama, to Allah zai rubuta
masa kubuta daga musibu guda biyu na farko
Allah zai rubuta masa kubuta daga wuta bazai
shiga wuta ba, na biyu kuma Allah zai rubuta
masa kubuta daga muna funci bazai mutu muna
fuki ba.
HADISI NA ASHIRIN
Sallar da Allah ya fi so itace sallar asuba ta
ranar jumaa a cikin jami, kuma duk wanda ke
abin da Allah ke so to Allah zai so shi, idan
kuma Allah Ya so shi
HADISI NA ASHIRIN DA DAYA
Wanda ya ce Subhanallahil azim Wabihamdihi,
zaa dasa masa wata bishiya a cikin gidan
Aljanna wadda zai ginda tsinkar alkhairin ta.
HADISI NA ASHIRIN DA BIYU
Manzon Allah ya wanda ya ce, duk wanda ya
karanta Subhanakallahumma Wabihamdika Ash-
shadu Allah Ilaha Illah anta astagfiruka waatubu
ilaika, a wajen jira ko inda ake shiririta ko shirme
bayan sun gama kamun su watse ya karanta
wannan zai zame masa kaffara bisa ga kura
kuran da ya tafka a wurin.
HADISI NA ASHIRIN DA UKU
Manzon Allah (S.A.W) ya ce Hakika fadar
Subhanallahi, Walhamdulillahi, Walaila ha
Illallahu, Wallahu Akbar, tana girgijewa mutum
zunubai kamar yanda bishiya take girgije ganyen
da yake zubuwa a kasa. Don haka mai makon
mutum ya zauna yana hira to ya yi ta fadar
wannan don Allah ya girgije masa zunubain sa.
HADISI NA ASHIRIN DA HUDU
Manzon Allah (S.A.W) ya ce idan dayan ku ya
gajiye bazai iya tarawa kansa lada dubu ba to
yayi Subhanallahi sau dari sai a rubuta masa
lada dubu ko a kankare masa laifuffuka guda
dubu.
HADISI NA ASHIRIN DA BIYAR
Manzon Allah (S.A.W) ya ce hakika Allah ya zabi
wasu kalmomi uku wanda ya nace musu to zai
samu alkhairin duniya da lahira sune
(Subhanallah, Walhamdulillah, Wallahu Akbar.
Wanda ya ce Subhanallah zaa bashi lada 20 a
kankare masa zunubi 20 Wanda ya ce
Alhamdulillah zaa bashi lada 30 a kankare masa
zunubi 30 wanda Allahu Akbar zaa bashi lada 20
a kankare masa zunubi 20.
HADISI NA ASHIRIN DA SHIDA
Manzon Allah (S.A.W) ya ce Bana gaya maka
wani abu wanda ya fi haka alkhairi? Kace
Subhanallah, Walhamdulillah, Walailaha Illallah,
Wallahu Akbar, zaa dasa maka bishiya a cikin
gidan Aljanna da kowace kalma da ka fada.
HADISI NA ASHIRIN DA BAKWAI
Manzon Allah (S.A.W) ya ce Wanda ya yi ruwa
da kudi bai ba dasu sadaka ba kuma ya yi rowa
da dare bai tashi yayi tsayuwar dare ba, to ya
lazimci wannan kalma sai ta tsaya masa a
matsayin sadakar da bai yi ba da tsayuwar dare
da ya kasa bai yi ba Subhanallahi Wabihamdihi
ya yi ta fadar wannan sai ya zamu a bakacen
kudin da bai bayar ba a bakacen daren da bai yi
tsayuwa a cikin sa ba.
HADISI NA ASHIRIN DA BAKWAI
Manzon Allah ya ce wanda zai shiga kasuwa sai
ya ce Lailaha illallahu wahdahu lasharikalahu,
Lahul mulku, walahul Hamdu, Yuhyi wayumitu,
wahuwa hayyulla ya mutu biyadihil khairu
wahuwa ala kullhi shaiin kadir. Allah zai rubuta
masa lada million daya ya goge masa zunubi
million daya zaa daukaka darajar sa million daya
sannan zaa gina masa gida a cikin gidan Aljanna.
HADISI NA ASHIRIN DA TAKWAS
Manzon Allah ya ce bana gaya maka abin da ya
fi ambaton Allah ka da daddare da rana ba?, to
kace Alhamdulillahi Adadama khalaka,
Alhamdulillahi mila ma khalaka, Alhamdulillahi
adada mafissamawati wama filardhi
Alhamdulillahi adada ma aksa kitabuk,
Walhamdulillahi ala ma akhsa kitabuk,
Walhamdulillahi adada kulli shaiin,
Walhamdulillahi minha kulli shaiin, kuma ka ce
Subhanallahi Adada ma halaka, Subhanallahi mila
ma halaka, Adada mafissamawati Wama filardi,
Subhanallahi ala ma ahsa kitabuk, Subhanallahi
adada kulli shaiin, Subhanallahi minha kullhi
shaiin, Subhanallahi wanda ya fadi wannan wato
yafi kowane irin ambaton Allah da zakayi fadin
duniyar nan Inji Manzon Allah.
HADISI NA ASHIRIN DA TARA
Manzon Allah (S.A.W) ya ce wanda ya min salati
kafa 10 lokacin da ya wayi gari, ya yimin salati
kafa 10 lokacin da ya yammatu, cetona zai
riskeshi ranar Alkiyama.
HADISI NA TALATIN
Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam Ya ce
wanda ya ce radhitu billahi rabban Wabil
Islamidinan Wabi Muhammadin Nabiyan, aljanna
ta tabbata a gareshi, ba wai zata tabbata ba
tariga ta tabbatar masa don haka muyi ta fadar
wannan kalma don Aljanna ta tabbata a garemu.
HADISI NA TALATIN DA DAYA
Mazon tsira ya na cewa wanda ya yiwa dan
Uwansa kyakkyawar Adua batare da dan Uwan
nasa ya sani ba Ya ce Allah ga dan Uwana wane
yana da bukata iri kaza ka biya masa, ko yana
cikin balai ka yaye masa ko yana cikin wata
fitina ko damuwa ka dauke masa, ba tare da shi
wancan dan uwan yasan kayi masa adua ba
koma baka gaya masa ba. Malaika ya na nan
kusa da kai sai ya ce amin walaka, kai ma Allah
ya baka irin kwatan kwacin abin da ka roka wa
dan uwanka. Kunga jamaa mu rinka rokawa yan
uwan mu adua mai kyau saboda muma malaiku
suyi mana adua mai kyau.
HADISI NA TALATIN DA BIYU
Manzon Allah ya ce wanda ya kare mutun cin
dan uwansa baya nan (maana ana kokarin
tuzarta dan uwanka baya nan sai kayi kakagida
ka kare masa mutuncin sa) to ya zama hakke ne
ga Allah ya yanta ka daga wuta.
HADISI NA TALATIN DA UKU
Annabi Muhammad Sallahu Alaihi Wasallam ya
ce wanda ya dauke abunda zai cutar da mutane
a kan hanya to hakika Allah zai rubuta masa
cikacciyar lada, wanda kuma Allah ya rubutawa
cikakkiyar lada Allah zai shigar dashi a Aljanna.
ALLAH YA TAIMAKE MU
Masoyin ku
Mai neman Rahamar Ubangiji

11/08/2015

ABUBUWA ARBA'IN DA MAZA S**A FI MATA.
1. Maza sun fi Mata hankali.
2. Maza sun fi Mata kaifin basira.
3. Maza sun fi Mata qarfi.
4. Maza sun fi Mata adalci.
5. Maza sun fi Mata hangen nesa. 6. Maza sun fi
Mata rashin gori.
7. Maza sun fi Mata qarfin hali.
8. Maza sun fi Mata kyauta/ sadaka.
9. Maza sun fi Mata iya tarairaya.
10. Maza sun fi Mata kuzari.
11. Maza sun fi Mata tsafta. 12. Maza sun fi
Mata iya magana.
13. Maza sun fi Mata wayo.
14. Maza sun fi Mata lura.
15. Maza sun fi Mata tattali.
16. Maza sun fi Mata iya zama da jama'a.
17. Maza sun fi Mata cika alqawari. 18. Maza
sun
fi Mata dauriya.
19. Maza sun fi Mata kyawun halitta.
20. Maza sun fi Mata natsuwa.
21. Maza sun fi Mata ladabi.
22. Maza sun fi Mata neman arziki.
23. Maza sun fi Mata rashin tsoro. 24. Maza sun
fi Mata tawakkali.
25. Maza sun fi Mata yawan ibada.
26. Maza sun fi Mata wayewa.
27. Maza sun fi Mata ilimi.
28. Maza sun fi Mata iya hukunci.
29. Maza sun fi Mata qwazo. 30. Maza sun fi
Mata kunya.
31. Maza sun fi Mata arziki.
32. Maza sun fi Mata rashin hadama.
33. Maza sun fi Mata riqon addini.
34. Maza sun fi Mata daraja.
35. Maza sun fi Mata son juna. 36. Maza sun fi
Mata kamala.
37. Maza sun fi Mata iya shugabanci.
38. Maza sun fi Mata rashin son kai.
39. Maza sun fi Mata son al'umma.
40. Maza sun fi Mata iya zaman duniya.ยด
Mexa Kuce Game Da Wannan ?

Want your school to be the top-listed School/college in Maiduguri?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Website

Address


Pompomari Sabon Fege Damaturu
Maiduguri