22/12/2015
SHARHI AKAN WAKAR “NI DAI
BARHAMA NAKE BAUTAWA, DAN SHI
YA HALICCENI”
Daga Muhammad Rabiu Umar
Dalilin Yin Wakar “Ni Dai Barhama
Nake Bautawa, Don Shi Ya Halicce Ni”
A yan kwanakin nan wata waka da
wani mawaki ya yi mai take “Ni dai
Barhama nake bautawa, don shi ya
halicce ni” ta jawo cece-kuce a tsakanin
mutane, kuma da yawa daga cikin
mutane sun yi mamakin a ce wai
musulmi ne ya yi wannan wakar,
wanda daga baya-bayan nan
gwamnatin Kano ta hanyar hukumar
tace finafinan ta bada sammacin a kamo
wannan mawaki.
Amma alal-hakika duk wanda ya san
irin akidar da take cikin manya-manyan
littattafan darikun sufaye – musamman
yan tijjaniyya – to ba zai yi mamakin jin
irin wannan waka ta fito daga irin masu
wannan darika.
Idan muka dauki babban littafin darikar
tijjaniyya mai suna “Jawahirul Ma’ani”
zamu ga cike yake da akidar “Komai
Allah ne” ma’ana duk wani abu da yake
duniyar nan Allah ne, kuma in an bauta
masa babu laifi, Allah aka bautawa, ga
kadan daga cikin abin da ya zo akan
haka : Shehu Tijjani ya ce :
“ ﻓﻤﺎ ﻓﻲ ﺫﻭﺍﺕ ﺍﻟﻮﺟﻮﺩ ﻛﻠﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﺳﺒﺤﺎﻧﻪ
ﻭﺗﻌﺎﻟﻰ ﺗﺠﻠﻰ ﺑﺼﻮﺭﻫﺎ ﻭﺃﺳﻤﺎﺋﻬﺎ، ﻭﻣﺎ ﺛﻢّ ﺇﻻ
ﺃﺳﻤﺎﺅﻩ ﻭﺻﻔﺎﺗﻪ” ( ﺟﻮﺍﻫﺮ ﺍﻟﻤﻌﺎﻧﻲ : 1/259 ).
Ma’ana “Babu abin da yake cikin zatin
dukkan samammu gaba dayansu sai
Allah Subhanahu Wa Ta’ala, shi ne ya
bayyana a surarsu da sunayensu. Babu
wani abu sai sunayensa da
siffofinsa” (Jawahirul Ma’ani 1/259).
Wannan magana tana nuna cewa duk
wani abin da yake samamme a wannan
duniya to ba komai ba ne face Allah ne,
saboda Allah ne ya bayyana a cikin
dukkan komai da sunayensa da
siffofinsa.
A wani wurin ya ce :
“ ﺇﻥ ﺟﻤﻴﻊ ﺍﻟﻤﺨﻠﻮﻗﺎﺕ ﻣﺮﺍﺗﺐ ﻟﻠﺤﻖ…ﻓﺈﻥ ﺍﻟﻮﺟﻮﺩ
ﻋﻴﻦ ﻭﺍﺣﺪﺓ ﻻ ﺗﺠﺰﺅ ﻓﻴﻬﺎ ﻋﻠﻰ ﻛﺜﺮﺓ ﺃﺟﻨﺎﺳﻬﺎ
ﻭﺃﻧﻮﺍﻋﻬﺎ ﻭﻭﺣﺪﺗﻬﺎ” ( ﺟﻮﺍﻫﺮ ﺍﻟﻤﻌﺎﻧﻲ : 2/92 ).
Ma’ana : “Dukkan ababen halitta wasu
yanki ne na Allah….saboda da dukkan
samamme abu daya ne, babu wani
yanki-yanki a cikinsa, duk da jinsinsa
mai yawa da nau’o’insa da
hadewarsa” (Aljawahir 2/92).
Wannan bayani yana nuna cewa duk
wata halitta Allah ce ita, kuma komai da
muke gani abu daya ne, wanda shi ne
Allah!.
Ya sake cewa :
“ ﻓﻜﻞ ﻋﺎﺑﺪ ﺃﻭ ﺳﺎﺟﺪ ﻟﻐﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﻈﺎﻫﺮ ﻓﻤﺎ
ﻋﺒﺪ ﻭﻻ ﺳﺠﺪ ﺇﻻ ﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ، ﻷﻧﻪ ﻫﻮ ﺍﻟﻤﺘﺠﻠﻲ ﻓﻲ
ﺗﻠﻚ ﺍﻷﻟﺒﺎﺱ، ﻭﺗﻠﻚ ﺍﻟﻤﻌﺒﻮﺩﺍﺕ ﻛﻠﻬﺎ ﺗﺴﺠﺪ ﻟﻠﻪ
ﺗﻌﺎﻟﻰ … ﻭﻗﻮﻟﻪ “ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺎ” ﻳﻌﻨﻲ ﻻ ﻣﻌﺒﻮﺩ
ﻏﻴﺮﻱ ﻭﺇﻥ ﻋﺒﺪ ﺍﻷﻭﺛﺎﻥ ﻣﻦ ﻋﺒﺪﻫﺎ ﻓﻤﺎ ﻋﺒﺪ
ﻏﻴﺮﻱ” ( ﺟﻮﺍﻫﺮ ﺍﻟﻤﻌﺎﻧﻲ : 1/184 )
“Duk wani mai bauta ko mai sujjada ga
wanin Allah a zahiri, ba wanda ya
bautawa ko ya yi wa sujjada sai Allah
Ta’ala, saboda shi ne yake bayyana a
cikin wadannan abubuwa, kuma duk
wadannan abubuwa da ake bautawa
suna sujjada ne ga Allah (S.W.T)
….sannan fadin Allah “Babu abin
bautawa sai ni” yana nufin babu wani
abin bautawa, wanda ba ni ba, ko da
kuwa masu bautar gumaka sun bauta
masu, ba su bautawa wani
ba” (Jawahirul Ma’ani 1/184).
Wannan kadan kenan daga cikin
mummunar akidar dake cikin wannan
babban littafin na darikar tijjaniyya. To
yanzu dan uwa mai karatu wanda ya
karanta wadannan maganganu, kuma
ya yi imani da su, ya yarda da cewa
wanda ya yi su, waliyyi ne daga cikin
waliyyan Allah, kuma duk abin da yake
fada Annabi ne (S.A.W) yake fada masa,
a farke a cikin barci, to yaya ba zai ce
“Barhama Yake Bautawa ba”!.
Wata kila mai karatu ya ce, to ba
Barhama ba ne ya koyar da haka, don
haka me ya sa shi mai wakar bai ce “Shi
Tijjani yake bautawa ba” sai ya ce
Barhama.
Dalili, shi kansa Barhama din wato
shehu Ibrahim Inyass haka shi ma ya
koyar ya kuma kira muridansa da
mabiyansa a kan haka, a cikin
littattafansa, ga kadan daga cikin abin
da ya fada a kan haka :
Yana cewa :
ﻓﺈﻥّ ﺍﻟﺸّﻴﺦَ ﻣﻈـﻬﺮُ ﺫﺍﺕ ﺭﺑِّﻲ ﻭﻋﻴﻦُ ﺍﻟﻌَﻴﻦ ﻋﻴﻦُ
ﺃﺑﻲ ﺍﻟﻌﺒﺎﺱ . )) ﺩﻳﻮﺍﻥ ﺗﺤﻔﺔ ﺃﻃﺎﻳﺐ ﺍﻷﻧﻔﺎﺱ ((
(ﺹ 86 ).
Ma’ana : Lallai hakika shehu shi ne
Mazharin zatin Ubangijina. Kuma
Hakikanin zati, shi ne zatin Abul Abbasi
(wato shehu Tijjani).
Anan zamu ga Inyass yana cewa shehu
Tijjani shi ne Allah, kuma duk wani zati
na wani abu, ba komai ba ne face zatin
shehu Tijjani, don haka komai shehu
Tijjani ne, shi kuma Allah ne!!.
A wani wuri cewa ya yi :
ﺧﻠﻴﻔﺔُ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺃﺭﺽٍ ﻟﺬﻟﻚ ﻣَﻦ ﺭﺁﻛﻢُ ﻗﺪ ﺭَﺃﻯ ﺭﺏَّ
ﺍﻟﺒﺮﻳَّﺎﺕ
Ma’ana : “Khalifan Allah a bayan kasa,
don haka duk wanda ya ganku, to lallai
ya ga ubangijin halitta”. (Duba littafinsa
Diwanu Tuhafatil Adayibil Anfas).
Subhanallahi, don ka ji mai karatu duk
wanda ya ga shehu Tijjani to ya ga
Allah, Ma’ana da Allah da Shehu Tijjani
duk abu daya ne!!!.
Wannan kadan kenan daga cikin akidun
da suke cikin littattafan wadannan
sufaye, kuma a kansu ne suke kokarin
renon mabiyansu, wanda har akwai
wata tarbiyya da ake wa muridi, wadda
bayan ya yi ta, sai zama Allah, kuma
komai ya zama Allah a wurinsa, Sheikh
Dahiru Mai gari (Allah Ya Yi masa
Rahama) ya yi rubuta akan wannan
tarbiyya da darika, ya tabbatar da
wadannan abubuwa.
Don yan uwa in ana so a magance ci
gaba da faruwar irin wadannan wakoki
to dole ne sai an wancakalar da
wadancan littattafai, kuma an dawo kan
koyarwar Alkur’ani da Hadisi a bisa
fahimtar magabata na Kwarai. Allah ya
tsare mana Imaninmu Ameen.