30/06/2025
ALLAH ZAI CIKA HASKENSA, KO MUNASO KO BAMASO INSHA ALLAH.
Chan na jiyo Yan Izala (Masu saukin cutar Kungiyanci) da Yan Dariku baki dayansu suna ta jerin gwanon addu’a ga kasar Iran (Yan Shi’a), cikin waki’ar da ta abku cikin kwanakin nan, sai ga shafuka duk ana rige-rigen posta Bidiyoyi da Hotuna irin na nasarar da kasar Iran ke samu akan abokiyar gabatarta, wato dai anyi baje kolin nuna yan uwantaka ta Musulunci, da kishin Musulmi, har aka mance da sabani, sai gashi ALLAH ya nuna Capacity irin na Musulmi cikin wannan yaki, sai na lura, ashe dai waki’a na sawa kawuna su hadu, ko da ace wasu na kallon reni da kuma tirjiya ga wanda yake kira zuwa ga hakan cikin dukkan majalisansa a inda suke.
Lallai duk wanda ya bibiyi wannan gagarumin taro da aka gabatar a birinin Kebbi akan wannan manufa ta hadin kai, to hakika zai tabbatar da cewa wannan jagora Maulana Prof. Ibrahim Maqari na samun nasara cikin kiransa, kuma lallai da sannu ko munaso, ko bamaso, dole zamu hadu da juna inda muka hadu, kuma lokaci na zuwa da zamuke yiwa juna uzuri inda aka samu sabani. Har ya zamo maslahar guda cikinmu zai zamo maslaharmu baki daya, haka matsalama.
ALLAH MUNA ROKONKA KA DAUKAKA WANNAN KURA NA HADIN KAI, KA KARAWA MUSULMI DA MUSULUNCI MARTABA DA KIMA ALFARMAR MANZON ALLAH (S.A.W).
ALHAMDULILLAH.