BA KOWACCE RANTSUWA AKE YIWA KAFFARA BA!!
TAMBAYA:
Assalamu alaikum warahamatullah, dan Allah inaso a amsa min wannan tambayar:-shin kowata irin rantsuwa ce ake yin mata kaffara kokuwa ba kowace bace ake yiwa kaffara ba ? na gode.
AMSA:
Wa alaikum assalam, ba kowacce rantsuwa ake yiwa kaffara ba, rantsuwoyi a fiqhun musulunci iri uku ne:
1. Rantsuwar da aka yi akan karya, wannan tana iya turbutsa mutum zuwa wuta, ba ta da kaffara sai istigfari, saboda girman zunubinta.
2. Rantsuwar da ta zo baki yayin magana ba tare da nufi ba, wannan Allah ya yi afuwa akanta, kamar yadda ya bayyana a aya ta: 225 a Suratul Bakara.
3.Rantsuwa akan wani abu da zai zo nan gaba, kamar ya ce : wallahi gobe zan je wuri kaza, in bai je ba, zai yi mata kaffara, kamar yadda aya ta: 89 a suratul Ma'ida ta tabbatar da hakan.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
28/05/2016).
Council For Islamic And Arabic School's Affairs Idi-Araba - Caissa
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Council For Islamic And Arabic School's Affairs Idi-Araba - Caissa, High School, 3, fagbenro Street, idiaraba, mushin, Lagos.
you are welcomed to an institution built to create and enhance the Arabic and Islamic teachings in you based on the understanding and solid foundation of the pious predecessors.
28/05/2020
HUKUNCIN AZUMIN SITTU SHAWWAL 1⃣
Malamai sunyi sabani akan hukuncin azumtar kwanaki shida na cikin watan Shawwal (sittu Shawwal), har zuwa maganganu guda biyu;
1. Magana ta farko: Sunnah ne azumtar wadannan kwanaki shidan, wannan shine maganan mafiya rinjaye daga cikin malamai, tundaga sahabbai da tabi'ai, daga cikin malaman mazhabobi guda biyun nan kuma shine maganan imam shafi'i da imam Ahmad.
📝 DALILANSU:-
wadannan malamai sunyi hujja da dalilai masu yawa amma ga kadan daga ciki;
1. Hadisin Abu Ayyub da manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yake cewa "duk wanda ya azumci ramadhan Sannan ya biyo bayansa da azumtar kwanaki shida na shawwal kamar ya azumci shekarane".
مسلم ١١٦٤، أبو داود ٢٤٣٣، ابن ماجه ١٧١٦
2. Hadisin thauban, Manzon Allah yake cewa "duk wanda ya azumci ramadhan Sannan ya azumci kwanaki shida bayan buda baki (eid fitr) hakan zai zama masa cikon shekara, domin duk wanda yazo da mai kyau guda daya yanada kwatankwacin sa sau goma".
ابن خزيمة ٢١١٥، ابن ماجه ١٧١٥، الدارقطني ١٧٥٥.
2. Magana ta biyu:- s**ace makaruhine yin azumin sittu shawwal, wannan maganan an ruwaito ta daga Abu Hanifa da kuma imam malik Allah yayi musu rahama,
📝 DALILINSU;
1. Sukace gameda hadisan da jumhur sakayi istidlali dasu cewa babu wani dalili acikinsu dake nuni akan falalan azumin sittu shawwal saboda manzon Allah ya kamantashi da azumin shekara wanda shikuma azumin shekara babu shakka makaruhine manzon Allah ya hana.
📖 Jumhur sunbada amsa ga wannan ta'alili nasu da cewa; An karhanta yin azumin shekarane saboda mafsadar da yin zai haifar na rauni da da kuma gazawa wurin yin ayyuka masu falala wanda ma sunfi azumin, amma da badan hakaba ai da azumin shekara shiyafi komai falala saboda cinye lokacine gabadaya cikin da'ar Allah da bautansa. Sannan abunda ake nufi da kamanceceniyan shine wurin samun lada da daraja wacce kuma babu irin waccar mashaqqar da kuma mafsadar acikinsa.
المغني مع الشرح الكبير ٤/٤٣٩
2. Dalilin su na biyu s**ace to aima hadisin da kukayi istidlali dashi bai inganta ba. domin hadisin yazone daga Sa'ad bin Sa'eed wanda shikuma anyi sabani akansa.
📖 Jumhur sun bada amsa da cewa sa'ad bin sa'eed bai kebanta da hadisin ba, ansamu wanda s**a masa mutaba'a,
Daga cikin wadanda s**a masa mutaba'a akwai;
🔸 Hadisin Safwan bin Saleem.
السنن الكبرى ٢٨٧٦، الدارمي ١٧٥٤.
🔸Hadisin Yahya bin Sa'eed.
السنن الكبرى ٢٨٧٩
🔸 Hadisin Abdu Rabbihi bin Sa'eed.
السنن الكبرى ٢٨٧٨.
▪Dan haka Sahabi Abi Ayyubal Ansari bai kadaita da wannan hadisin ba, bal sahabbai goma sha hudu sun rowaito shi.
▪Sannan Umar bin thabit shima bai kadaita da hadisin ba akwai wanda s**a rowaitoshi kamar su Ibnul Munkadir.
▪Hakanan shima sa'ad bin Sa'eed bai kadaita dashi ba, kamar yadda muka anbata asama wadanda s**a masa mutaba'a.
Wannan yake nuna maka cewa hadisin ingantacce ne kuma babu wani rawi acikinsa da ya kadaita dashi.
Sannan babu shakka anyi sabani akansa wasu sun wathathaqa shi kamar yadda aka samu wasu sun da'ifantar dashi. Ibnul Qayyim Allah ya masa rahama yake cewa bayan ya ambato duka illolin da ake tuhumar hadisin dasu ya kuma bada amsa akansu sai yake cewa "Duka wadannan illolin dukda zasu iya hanawa hadisin ya kai kololuwa wurin inganci to amma bazasu taba kaskantar dashi ba (da'ifantar dashi)".
تهذيب السنن ٣/٣٠٩.
Arubutu na gaba zamu tashi akan cigaban dalilan wadanda suke ganin makaruhine yin wannan azumi na sittu shawwal. Allah ya mana muwafaqa.
Julaibeeb
4/10/1441
27/5/2020
FISABILILLAH🌿 "Duk Wanda ya yi nuni akan aikin alkhairi, to, yana da lada kwatankwacin Wanda ya yi aikin" https://www.facebook.com/FISABILILLAH-2169310043281726/ https://t.me/Fisabilillaaah
As Salam alaikum
Ibn-taimiyyah's institute for Arabic and shariah studies na farin cikin taya al'umar musulmi murnar barka da karamar sallah 1/10/1441
Wanda yayi daidai da 23/5/2020.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Telephone
Website
Address
3, Fagbenro Street, Idiaraba, Mushin
Lagos