HAKKOKIN AL-QUR'ANI MAI GIRMA GUDA GOMA(10)
Daga Sheikh Muhammad Bin Uthman
Hakkokin littafin Allah(SWT) a kanmu sun wuce a ce za'a lasafta su. Dalili kuwa shi ne, mu'jizojinsa ba sa karewa, alkhayransa ba su da iyaka, sannan kuma kwarin dalilansa ba ya raunana. Dan haka wannan adadi goma ba ya zo a babin iyakanceawa ko takaitawa ba ne, ya zo ne a babin jan hankali dangane da fitattun hakkokin nasa. Falalar wannan littafi dai ba a boye take ba ga duk mai iymaani
A cikin wani Hadiithi fitacce wanda limamai biyu al-Bukhaary da Muslim(RL) s**a fitar bisa riwayar Abuu Umaamatul Baahily(RA), Manzon Allah(SAW) yana cewa (fassara):
" Ku karanta al-Qur'aani, domin zai zo ranar tahsin al-Qiyaamah yana mai ceto ga ma'abotansa (masu karanta shi)".
Wadannan hakkoki guda goma su ne:
1- Yin iymaani da shi cewa TABBAS saukakke ne daga Allah Madaukaki, hatta sanya wa surorinsa suna, al'amari ne Taw'qiify, wato babu wata mashiga ga ra'ayin wani makhluuqi ciki;
2- Karanta shi tare da cikakkiyar lura kan abinda ya ke karantarwa (tadabburi). A cikin Suuratun Nisaa'i aayah ta 82, Allah Madaukaki Yana cewa (fassara):
"Shin (mutane) ba za su lura da al-Qur'aani ba ne? Ai da daga wajen wanin Allah yake, da sun sami sabani mai yawa cikinsa". Wannan aayah da mak**antanta na nuna mana muhimmancin yin la'akari da kuma matukar yin lura a lokacin da muke Karanta littafin Allah. Wannan shi ne hakki na farko
3- Kasa kunne da kuma yin tsit lokacin da ake karanta shi. Laifi ne baba a kan mutum ya dinga surutu lokacin da a ke Karanta al-Qur'aani. A cikin Suuratul A'raf aayah to 204, Allah Madaukaki Yana cewa:
"Idan ana karanta al-Qur'aani, to Ku kasa kunne a gare shi kuma Ku yi shiru (tsit) da fata cewa Ku za'a rahamshe Ku"
4- Koyo shi. Ma'ana, dole ne Musulmi ya nemi ilmin sanin al-Qur'aani. Wannan shi ma wani hakki ne babba na al-Qur'aani a kan Musulmi.
5- Koyar da shi ga mai neman iliminsa wajibi ne ga wanda ya san shi.
A wani Hadiithi wanda al-Bukhaary da Muslim s**a fitar da shi daga sarkin Musulmi 'Uthmaan Bin 'Affaan(R.A.), Manzon Allah(SAW) Yana cewa (fassara):
"Mafi al-khayrinku shi ne wanda ya koyo (wato ya nemo ilimin) al-Qur'aani sa'annan kuma ya karantar da shi"
6- Kiran mutane zuwa gareshi. Ma'ana, dole ne a sauke hakkin al-Qur'aani da ke kan mu ta hanyar kiran mutane zuwa ga karantarwar da shi Qur'aanin. A aayar karshe - wato aayah 45 ta cikin Suuratu Qaaf-, Allah Madaukaki Yana cewa(fassara):
"Dan haka Ka wa'azantar da wanda ke jin tsoron narkona da al-Qur'aani".
7- Bashi kariya daga masu s**an sa cikin kafirai da munafukai. Haka kuma kare shi daga masu murde ma'anarsa domin goyon bayan wani son zuciya nasu. Misali aayah ta 99 cikin Suuratul Hijri inda Allah Ta'aala Yake cewa (fassara):
" Kuma Ka bauta ma ubangijnka har YAQIINI (mutuwa) tazo maka"
Wani karkataccen dan bid'ah a Sudan sai ya fassara YAQIINI a nan da cewa wai ana nufin TABBAS ne da SAKANKANCEWA. Ma'ana wai idan Ka bauta wa Allah har ka kai ga samun TABBAS a zuciyarka da kuma SAKANKANCEWA kan iymaani, to kana iya barin Ibadah!!
Irin wadannan 'yan bid'an ana iya rusa wannan harigidon nasu ta hanyar fayyace wa al'ummah cewa ai YAQIINI a nan mutuwa a ke nufi. Albaghawy(RL) ya koro hadiithin Ummul 'Alaa al-Ansaariyyah(RA) inda take yabawa Uthmaan Bin Maz'uun(RA).. Sai Manzon Allah(SAW) yace mata ai shi Uthmaan YAQIINI ya zo masa daga ubangijnsa, wato ya rasu. Dadin dadawa, duk da tsananin YAQIININ Manzon Allah(SAW) amma hatta ranar da zai bar Duniyar sallah yake!!
8- Mayar da shi alkali duk lokacin da aka sami gardama da ja in ja
9- Mayar da shi wato al-Qur'aani abin koyi cikin dukkanin al-Amura
10- Girmama shi ta hanyar:
-Rashin sanya tilawarsa a matsayin amo na Kira wato "ring tone". Yin haka haramun ne ta fuskoki guda biyar(5)
- Hanuwa ga barin lakuto yawu domin bude shafukansa.
- Hanuwa ga barin dora wani littafi a kansa
da sauran abubuwa masu k**a da haka.
ALLAH KA DATAR DA MU.
Dandalin Sunnah (Qur'an & Hadith)
Islam Da'awah
08/10/2016
Shafin Farko DUNIYA 'Yan Shi'a na ci gab...
'Yan Shi'a na ci gaba da komawa addinin Kiristanci
Wani bincike da kafar yada labarai ta AP ta yi ya nuna cewa, daruruwan yan Shi'an kasar Iran wadanda s**a nemi mafaka a kasar jamus, na ci gaba da rungumar Kiristanci a matsayin sabon addininsu.
08.10.2016 ~ 08.10.2016
'Yan Shi'a na ci gaba da komawa addinin Kiristanci
Wani bincike da kafar yada labarai ta AP ta yi ya nuna cewa, daruruwan yan Shi'an kasar Iran wadanda s**a nemi mafaka a kasar jamus, na ci gaba da rungumar Kiristanci a matsayin sabon addininsu.
A cewar faston cocin birnin Balin wato malam Gottfried Martens , ya zuwa yanzu Iraniyawan da aka yi wa baptisma sun haura 600,kuma yawan sai dada karuwa yake a kulli yaumin.Haka zalika akwai daidaikun 'yan kasar Afganistan wadanda s**a mara musu baya.
Martens ya kara da cewa kashi 90 a cikin dari na wadanda s**a koma Kiristanci na ci gaba da halartar tarukan ibada da ake shiryawa a cocuna.
Wani sabon tuba a addinin na Kiristanci mai suna Mohammed Ali Zonoobi ya ce :“A gaskiya a yanzu muna iya cewa mun samu 'yancin kai.Abinda ya fi kwantar mana da hankali shi ne tabbacin da muke da shi game da kyaukywar makomar da 'ya 'yanmu zasu samu a Germany,da kuma irin o ingantaccen ilimin zasu samu”.
'Yan Shi'a na ci gaba da komawa addinin Kiristanci Wani bicike da kafar yada labarai ta AP ta yi ya nuna cewa, daruruwan yan Shi'an kasar Iran wadanda s**a nemi mafaka a kasar jamus, na ci gaba da rungumar Kiristanci a matsayin sabon addininsu.
-GHADIR: KALUBALE GA ‘YAN SHI’A
Na Dr. Mansur Sokoto
INGANTACCEN LABARIN GHADIR:
Kalmar Ghadir a larabce, tana nufin wurin da ya tara ruwa da ciyawa.
“Ghadir Khum” sunan wani tafki ne da yake a yankin Juhfa, kilomita 15 daga Rabigh. Nisan sa daga Makka kilomita 160 ne.
Labarin Ghadir:
Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallam ya aiki Khalid dan Walid a matsayin kwamandan rundunar da za ta yi yaki a kasar Yaman daf da fara aikin Hajjin shekara ta 10H, hajjin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da kansa ya jagoranta.
Bayan da rundunar musulmi ta ci nasara sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya aika Sayyidi Ali don ya kula da sha’anin Ganimar da aka samu.
Ali Radhiyallahu Anhu ya raba Ganima, kuma ya cire hakkin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam na Khumusi k**ar yadda Alkur’ani ya zayyana. Daga ciki kuma ya cire ma kansa wata kuyanga da ta ba shi shawa.
Sayyidi Ali bai bata lokaci ba ya zarce zuwa Makka don ya riski maigidansa Sallallahu Alaihi wa Sallam a wurin aikin Hajji. Ya kuma wakilta wani daga cikin sojoji akan sauran aikin da ya rage.
Domin ya dadada ran sojojin, wakilin Sayyidi Ali ya raba ma su tufafi kyawawa daga cikin abin da aka ganimanto. Ya kuma yi ma su izini kowa ya hau rakumin da yake so daga cikin kayan Ganima. Kafin haka, sojoji sun gabatar da bukatar haka ga Sayyidi Ali amma bai amince ba. Sai ya ce ma su, rabonku sai an je Madina.
Sojojin wannan runduna sun hadu da Sayyidi Ali tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam a kan hanyar su ta dawowa bayan gama aikin Hajji. Sayyidi Ali ya nuna rashin jin dadinsa a kan wannan rabo da aka yi kafin lokacin yinsa. Nan take ya yi umurni duk su sauka daga rakuman, s**a kuma mayar da tufafin da aka raba masu. Rayukansu sun baci matuka a kan haka kuma sun kai karar sa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam suna zargin sa da cewa ya kuntata masu.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya iso Ghadir Khum, kuma ya lura da fushi a fuskar wadannan sojoji. Ya yi huduba yana tambayar su
(!ألستُ أولى بالمؤمنين من أنفسهم؟)
“Ashe ban fi muminai cancanta da kawunansu ba?” S**a ce masa, haka ne. Sai ya ce,
(فمن كنت مولاه، فعلي مولاه)
“To, duk wanda nake majibincinsa Ali ma majibincinsa ne”. Ma’ana, bai dace ku bata ranku a kan hukuncin da ya yi ba.
Da wannan babban jagora ya kwantar da wannan rikici da rashin fahimta, ya kuma nuna wajabcin a yi ma jagora da’a, sa’annan ya bayyana matsayin dan uwansa Sayyidi Ali a wurin muminai. Sojojin s**a ba shi hakuri, s**a gane matsayinsa, s**a wuce Madina tare da sauran ayarin mahajjata da suke tare da shi. Wannan shi ne abin da ya faru. Illa iyaka.
TATSUNIYAR GHADIR
**
‘Yan Shi’a sun ribaci wannan abin da ya faru kuma ya zo ya wuce k**ar sauran ire-irensa. S**a fank**a shi, s**a fadada shi, s**a mayar da shi wani gagarumin bukin nadin sarauta. S**a kuma jefi duk Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da kin Allah da kauce ma gaskiya, da jayayya da wannan nadi da s**a ce an yi.
Wannan akidar ta Ghadir a matsayin ranar buki ba a san ta a cikin tarihi ba sai bayan sama da shekaru 340 gwamnatin Shi’a ta Buwaihawa ta kago wannan bidi’a a kasar Iraqi. S**a mayar da ranar 18 ga watan Dhul Hajji a matsayin ranar wannan buki ta kowace shekara. S**an taru a wurin kaburburan manyansu suna ta kururuwa suna la’antar masoyan Allah wadanda s**a ce sun kauce ma umurni Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da ya bayar na mika mulki ga maigida Sayyidi Ali.
Sun kago ruwayoyi barkatai a kan falalar wannan rana, cikin su har da cewa wai, Imam Ar-Ridha ya ce, da mutane sun san matsayi da falalar wannan rana da Mala’iku sun rinka musafaha da su har sau goma a kowace rana.
Haka kuma sun kitsa tatsuniyoyi masu nuna wai, manyan Sahabbai sun yi ma Ali mubaya’a amma a munafurce, sannan s**a shirya makarkashiyar kashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam. A cikin su kuma wai har da duk sauran tara daga cikin mutane goma da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya yi ma su bushara da aljanna.
KALUBALE GA ‘YAN SHI’A
Muna kalubalantar ‘yan Shi’a a kan wannan batu da wadannan tambayoyi:
1. Idan wannan magana ta Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam cewa “Duk wanda nake majibincinsa Ali ma majibincinsa ne” tana nuna wajabcin shugabantar da shi, to me za ku ce game da fadar Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam “Ko wace al’umma tana da amintacce, mu kuma amintaccenmu a cikin wannan al’umma shi ne Abu Ubaida”? Wa ya fi cancanta a cikin su kenan?
2. Idan har gaskiya ne an yi wannan nadin k**ar yadda kuke cewa, me ya sa ba a umurci Sayyidi Ali da ya ci gaba da ba da Sallah ba musamman bayan da ciwon ajali ya k**a Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam?
3. Me ya sa ba ayi wannan bukin a zamanin da Sayyidi Ali yake Khalifa ba ko Sayyidi Al-Hasan ko a zamanin duk Imamanku goma sha daya da s**a rayu kafin Malam Na-boye (Mahadinku) ya zo duniya? Me ya sa sai lokacin da Buwaihi Bafarise mai kamun kifi ya kafa gwamnati sannan aka fara wannan buki a shekarar 352H?
4. Idan hudubar Ghadir tana nufin nadin sarauta ne, me ya sa ba ayi ta a Makka ba in da duk alhazan duniya s**a taru su sama da mahajjata dubu dari?
5. Ashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam bai yi hudubobi a can Makka da Minna da Arafat ba? Me ya sa bai ware huduba ta musamman a kan wannan babbar maganar ta halifancin Sayyidi Ali ba?
6. Ashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam bai yi huduba a kan jinainai da dukiyoyi a ranar babbar sallah ba? Ashe bai yi ma al’umma wasici da muhimman abubuwan da suke bukatar sani ba? Ita wannan maganar ba ta kai muhimmancinsu ba ne ya manta da ita? Me ya sa sai da aka watse, kowa ya bi hanyar garinsu saura mutanen Madina kawai s**a rage sannan ya yi wannan magana a cikin sunkurmin daji a tafkin Ghadir?
7. Ya ya aka yi Sahabbai s**a riwaito wannan hudubar ta Ghadir alhalin kun ce sun boye kaso biyu cikin uku na Alkur’ani masu bayyana falalar Ahlulbaiti?
8. Kun ce duk rikicin da musulmi s**a shiga a tsawon tarihi dalilin kauce ma wannan umurni na ranar Ghadir ne da sahabbai s**a yi. Me ya sa Alkur’ani ya yi biris da labarin Ghadir?
9. Allah Tabaraka wa Ta’ala ya saukar da sura ta musamman a cikin Alkur’ani kan maganar Hudaibiya da mubaya’ar da sahabbai s**a yi ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da har wuri da bishiyar da s**a yi mubaya’a a karkashinta, kuma ya ce ya yarda da su a kan haka bisa ga abin da ke cikin zukatansu na imani da ikhlasi. Kuma ya ce, a lokacin da suke yi ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam mubaya’a hannun Allah yana saman nasu. Me ya sa idan har an yi wannan mubaya’a Allah bai kawo ta ba a cikin Alkur’ani?
10. Mubaya’ar da mata s**a yi ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ita ma Allah ya kawo labarinta cikin Suratul Mumtahana. Shin ita wannan mubaya’ar ta Ghadir ba ta da muhimmanci ne irin wannan mubaya’ar mata ko kuwa?
‘Yan Shi’a ku ji tsoron Allah! Malamanku suna zargin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da boye wannan bayani wai a cikin Makka har suna cewa a kan wannan boyewar da ya yi sai da Allah ya saukar da ayar ”Ya kai wannan manzo ka isar da sakon da aka saukar ma ka daga wurin Ubangijinka. Idan kuwa har ba ka yi ba to, ba ka isar da sakonsa ba. Kuma Allah zai kare ka daga mutane”. To, sannan wai, ya tsaya a Ghadir Khum ya isar da wannan sako. Ku ji tsoron Allah! Ku darajanta manzonsa, ku koma ga gaskiya.
Wallahi, Sayyidi Abubakar da Sayyidi Umar da Sayyidi Usmanu da ma duk sauran sahabbai almajiran Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ba su jiye ma Sayyidi Ali da kome. Kuma ba su da wani kwadayi ga duniya b***e su nemi shugabanci. Allah Ta’ala da kansa cewa ya yi a kan su:
(للفقراء المهاجرين الذين أُخرجوا من ديارهم وأموالهم يبتغون فضلا من الله ورضوانا وينصرون الله ورسوله أولئك هم الصادقون)
“-A bayar da Fai’i- ga talakawa Muhajirai wadanda aka fitar da su daga gidajensu da dukiyoyinsu suna neman falala daga Allah da yarda, kuma suna taimakon Allah da manzonsa. Wadancan su ne masu gaskiya”
To, ka ji. An kore su daga garuruwansu, aka kwace dukiyarsu kuma a cikin zukatansu ba zaman gida ko mallakar dukiya ne a gabansu ba. Babban gurinsu shi ne taimakon Allah da manzonsa. Ka kuma ji Allah ya ce ma su masu gaskiya. Don Allah ta ina wadannan za su yi kwacen mulki kuma har su shirya ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam makarkashiyar kisan sa?!
Ya Allah! Ka shiryar da bayinka, ka ceto su daga muguwar akidar da Farisawa ‘yan bautar wuta s**a kago s**a lullube ta da rigar musulunci don su halaka su.
Allahumma Ameen
20/08/2016
Bidiyo: Kur'ani da Annabi Ne Hanyoyin Tsira-Inji Dalai Lama (Shugaban Addinin Budha)
A albarkacin wata ziyara da ya kai a masallacin Jama na kasar Pakistan, shugaban addinin Buddah na kasar Tibet Dalai Lama ya ce idan ana son a kubutar da duniya daga kanin ta'addanci,to dole ne kowa ya rungumi Kur'ani da halin Annabi Muhammadu (SAW).
A albarkacin wata ziyara da ya kai a masallacin Jama na kasar Pakistan, shugaban addinin Buddah na kasar Tibet Dalai Lama ya ce idan ana son a kubutar da duniya daga kanin ta'addanci,to dole ne kowa ya rungumi Kur'ani da halin Annabi Muhammadu (SAW).
http://www.trt.net.tr/hausa/duniya/2016/08/20/bidiyo-kur-ani-da-annabi-ne-hanyoyin-tsira-555682
Bidiyo: Annabi da Kur'ani ne Hanyoyin Tsira A albarkacin wata ziyara da ya kai a masallacin Jama na kasar Pakistan, shugaban addinin Buddah na kasar Tibet Dalai Lama ya ce idan ana son a kubutar da duniya daga kanin ta'addanci,to dole ne kowa ya rungumi Kur'ani da halin Annabi Muhammadu (SAW).
15/08/2016
¬Shine wanda yayi kuka sabida kai/ke
¬Shine wanda yayi yaki aka cire masa hakori sabida kai/ke
¬Shine wanda ya daure Dutsi a cikinsa mai albarka don tsananin yunwa sabida kai/kai
¬Shine wanda ya hana kansa barci sabida da kai/ke
¬Shine wanda yayi hijira sabida kai/ke
¬Shine wanda bai yarda an zare Ransa mai albarka ba saida aka masa kyakkyawar albishir halinda al'ummarsa zasu kasance sabida kai/ke.
%%Shin kai me kayi masa?%%
~Allahumma salli ala sayyidina Muhammadin wassallim~
Like |Share |Comment |Jazakhallah
13/08/2016
Bidiyo: Yanayin Musulunci a Barazil
'Yan Barazil na ci gaba da Musulunta,addinin Islama kuma na ci gaba da samun gindin zama a kasar.
13.08.2016 ~ 13.08.2016
Bidiyo: Yanayin Musulunci a Barazil
'Yan Barazil na ci gaba da Musulunta,addinin Islama kuma na ci gaba da samun gindin zama a kasar.
'Yan Barazil na ci gaba da Musulunta,addinin Islama kuma na ci gaba da samun gindin zama a kasar.
http://www.trt.net.tr/hausa/duniya/2016/08/13/bidiyo-yanayin-musulunci-a-barazil-550983
Bidiyo: Yanayin Musulunci a Barazil 'Yan Barazil na ci gaba da Musulunta,addinin Islama kuma na ci gaba da samun gindin zama a kasar.
06/08/2016
Majalisar dokokin Girka ta amince da a gina Masallaci na farko a birnin Athens
Majalisar dokokin Girga ta yi muhawara tare da amincewa da gina Masallacin Juma'a na farko a Athens babban birnin kasar.
05.08.2016 ~ 06.08.2016
Majalisar dokokin Girga ta yi muhawara tare da amincewa da gina Masallacin Juma'a na farko a Athens babban birnin kasar.
'Yan majalisu 210 ne s**a jefa kuri'ar amincewa da a gina Masallacin wanda za a samar da shi da kudaden mak**ashi.
Jam'iyyar ANEL da Golden Dawn masu tsattsauran ra'ayi ne s**a nuna rashin amincewa kan a gina Masallacin.
Gwamnatin Girka ta ware wani fili mai girkan eka 17 don samar da Masallacin na Juma'a a birnin.
Ana amfani da Masallacin Jistaraki na Daular Usmaniyya a matsayin gidan ajje kayan tarihi a birnin.
Birnin Athens ne kadai babban birnin wata kaa a nahiyar Turai da babu Masallacin Juma'a.
http://www.trt.net.tr/hausa/duniya/2016/08/05/majalisar-dokokin-girka-ta-amince-da-a-gina-masallaci-na-farko-a-birnin-athens-545249
-------------------------------------------------------------------
-->>"Like" Our Page for more News
-------------------------------------------------------------------
Majalisar dokokin Girka ta amince da a gina Masallaci na farko a birnin Athens Majalisar dokokin Girga ta yi muhawara tare da amincewa da gina Masallacin Juma'a na farko a Athens babban birnin kasar.
31/07/2016
Ana gudanar da zanga zangar wariyar launin fata da kyamar Musulmai a Jamus
An gudanar da zanga zangar kyamar musulunci, wariyar launin fata da kuma rashin amincewa da masu neman mafaka a Jamus
31.07.2016 ~ 31.07.2016
A Berlin babban birnin Jamus ne wasu kungiyoyi s**a gudanar da zanga zangar kyamar musulunci, wariyar launin fata da kuma rashin amincewa da masu neman mafaka a kasar Jamus.
Kungiyoyin sun hau tituna da rike da alluna dake da taken ''ku bar mana kasarmu, bamu son musulumai a kasarmu''. Haka zalika wata kungiyar ra'ayin mazanjiya kuma ta gudanar da zanga -zangar adawar manufofin Shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel imda s**a bukaci Merkel ta yi murabus.
'Yan sanda sun cafke wani mutum da ya yi kirarin Hi**er a yayin zanga-zangar.
Akalla 'yan sanda 700 ne s**a yi tsaron guraren zanga zangar.
http://www.trt.net.tr/hausa/duniya/2016/07/31/ana-gudanar-da-zanga-zangar-wariyar-launin-fata-a-jamus-541374
Zanga-zangar kyamar musulunci a Jamus An gudanar da zanga zangar kyamar musulunci, wariyar launin fata da kuma rashin amincewa da masu neman mafaka a Jamus
27/07/2016
24/07/2016
Allahu-Akbar! Wannan shine Kur'anin Sayyidina Usman (عليه السلام).
--->"Like" Our Page For More Historic Pictures.
22/07/2016
Manzon Allah (صلالله عليه وسلم)
~Yadda ake tsayawa a masa
"Assalamu alaika yaa Rasuulullah!"
____________________________
"Like Our Page For More Historic Pictures".
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Contact the school
Telephone
Website
Address
JIBWIS
Lafia Beriberi
Opening Hours
| Monday | 09:00 - 17:00 |
| 18:00 - 19:00 | |
| Tuesday | 09:00 - 17:00 |
| Friday | 20:14 - 17:00 |