Nigeria Kasa Ta

Nigeria Kasa Ta Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Nigeria Kasa Ta, Tutor/Teacher, Kura.

18/01/2019

Salam

09/10/2018

Nigeria

30/06/2018

Allah Ka Kawo Arziki Mai Yalwa A Kasa Ta Ta Gado Nigeria

23/11/2017

Rundunar sojin Najeriya ta bai wa dukkanin
jami’anta umarnin fara koyan manyan harsunan
kasar wato, Hausa da Yarbanci da yaran Igbo.
Wata sanarwa da mai magana da yawun
rundunar ya fitar a safiyar yau Laraba Birgediya
Janar Sani Usman Kuka Sheka ta ce, ana saran
dukkanin jami’an su kware a manyan harsunan
nan da watan Disamban shekarar 2018.
Kuka Sheka y ce, umarnin na cikin sabon tsarin
koyan harsuna da rundunar sojin ta bullo da shi.
Sanarwar ta ce, sabon tsarin zai taimaka wa
sojojin ta fannin huldar sadarwa da sauran
al’ummar, sannan kuma zai taka rawa wajen
tattara bayanai.
A cewar sanarwar, kwarewa a harsunan uku za
ta bai wa masu neman shiga aikin soji a kasar
wani fifiko na musamman wajen daukan aiki.

24/05/2017

Buhari Ya Warke Daga Mummunar Gubar Da Aka
Sa Masa - Inji Likitansa
Daga Zulyadaini Sidi Mustapha.
Daya daga cikin Likitocin shugaban kasa
Muhammadu Buhari ya shaidawa gidan Talabijin
na Aljazeera cewa ya samu sauki daga
mummunar gubar da aka sa masa. A cewar sa
Shine mutum na farko a Afirka da aka taba sa
wa wannan GUBA ya warke. Kuma na 11 a fadin
duniya.

12/05/2017

MUTANEN NIGERIA MUNA CIKIN JARRABAWA.
Kokasan Mai nene Maganin Musiba?
1- Manzon Allah (saw) yace, Wadanda s**a fi
kowa gamuwa da jarrabawa mai Tsanani sune
Annabawa.
2- Manzon Allah saw yace, Idan Allah yanason
mutane sai ya Jarraba su, wanda ya yarda sai ya
sami yarda, wanda yayi fushi sai ya gamu da
fushi.
3- Manzon Allah saw yace, Manya manyan
sak**ako yana tare da manya manyan bala'o'i.
4- Manzon Allah saw yace, Idan Allah yana nufin
bawansa da Alkhairi sai ya gaggauto masa da
Tsanani a duniya.
5- Manzon Allah saw yace, Babu wata musifa da
zata shafi mumini ko mumina, tun daga taka
kaya, ko fiye da haka face sai Allah, ya Daukaka
musu daraja, ko ya kankare musu zunubi.
Saboda haka Al ummar nigeria Kar muyi fishi
saboada,tsanannin Jarrabawa da bala o 'i da
muka sami kanmu acikin wannan Rayuwa.
Tawani bangaren lefinmune mu Al umma tawani
fuskar kuma Allah ne ya jarrabemu,sabod
a
munjuyamishi baya shima sai yabarmu
dawayonmu, ko dabararmu zata fiddamu?
Allah yana jarabtar wasu Bayinshi
Domin Ya yafe musu zunubi
Domin ya Daukaka musu daraja
Domin ya yi musu Jan kunne kan wani abu da
s**ayi da kuskure
Domin ya Jarraba imaninsu da kaddara.
Yan uwa mutanen nigeria,Ina shawar tanmu
Damuyi gaggawan tuba izuwa ga Allah(swt),mu
nisanci sabawa Allah,mu yawaita neman yafiya
gareshi.
Amma mutane dayawa suna jin Wa'azi Suna
karatu Amma Kadan ne suke Sawa A Aiki
dafatan Allah Kamana Taimako ka kawomana
karshen wannan jarrabawa da muke ciki.

02/05/2017

Falalu Bello Gwada-bawa
JERIN KARANCIN ALBASHIN MA'AIKATA NA
WASSU KASASHEN DUNIYA:
1. Nigeria - $38 (N18,000).
2. Algeria - $175 (N83,000).
3. Belgium - $1,738 (N810,000).
4. Cameroun - 36, 270CFA ($75) N38,000.
5. Chad - $120 (N60,000).
6. Denmark - $1,820 (N900,000).
7. Libya - $430 (N190,000).
8. Japan - $1000 (N450,000).
9. Cote D'ivoire - $72 (36,607)
10. New Zealand -$3,187 (N1.4m).
11. Luxemburg - $2,500 (N1.1m).
12. Spain - $760. (N300,000).
13. Switzerland - $5,620 - N2.5m.
14. USA - $11 per hour.
Ammana kuma abun mamaki, Yan siyasar
Nijeriya
sunfi na kowacce kasa diban albashi.
Kamar misali a kasar Luxemburg inda karancin
albashi shine: $2,500, yan majalisun su ana
biyansu $7,400.
A Libya kuma inda karancin albashin su shine:
$430, yan majalisun su kuma suna diban $3000.
A Nijeriya kuma, inda karancin albashi shine $38
(N18,000), yan majalisunmu kuma suna diban
$65,000 (N29m) kuma ba tareda an samu
outstanding albashi ba.
Allah Ta'ala muke roqo Ya ke6o bayi daga
hannun kuraye.

20/04/2017

Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Yemi
Osinbajo ya kare zarge-zargen da ake yi wa
gwamnatin Muhammadu Buhari na take hakkin
bil'adama da rashin martaba fannin shari'a.
A wani jawabi na bidiyo da aka wallafa a shafin
gwamnati na Twitter , Mista Osinbajo ya ce shi
mutum ne da ke tsayawa tsayin daka wajen
ganin an mutunta umarnin kotu.
Ya nuna cewa dalilin da ya sa gwamnati ba za ta
saki shugaban kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta
'yan Shi'a Ibrahim El-Zakzaky ba, shi ne saboda
ta daukaka kara kan hukuncin kotun da ya ce a
sake shi.
Gwamnatin Buhari na shan s**a kan yadda ta ke
cigaba da tsare El-Zakzaky, da jagoran 'yan
awaren Biafra Nnamdi Kanu da tsahon mai ba da
shawara kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki.
Mutanen uku sun shafe wata da watanni a
hannun hukumomi duk da cewa kotu ta ba da
umarnin a sake su a lokuta daban-daban.
Mista Osinbajo ya ce "duk lokacin da kotu ta ba
da wani umarni, to ya zama dole a yi aiki da shi.
Sai dai kuma muna da damar da za mu daukaka
kara," in ji shi.
A watan Disamban bara ne wata kotu ta yanke
hukuncin cewa tsarewar da ake yi wa Sheikh El-
Zakzaky ta saba wa doka kuma ta umarci a sake
shi cikin kwana 45, sai dai gwamnati ta yi burus
da umarnin.
An k**a shi ne a watan Disambar shekarar 2015,
bayan wani rikici da sojoji s**a yi da mambobin
kungiyarsa a Zariya, inda aka kashe daruruwan
mabiyansa.
Sai dai har yanzu ba a tuhume shi da aka laifin
komai ba.
Shi kuwa Nnamdi Kanu yana tsare ne saboda
zargin cin amanar kasa da ke da alaka da
fafutikar neman kafa kasar Biafra.
Yayin da shi kuma Dasuki ke fuskantar shari'a
kan zargin almundahana da cin hanci, zargin da
ya musanta yana mai cewa siyasa ce kawai.

Address

Kura

Telephone

+2348024717141

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nigeria Kasa Ta posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category